
Ministan Kuɗi kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki na Ƙasa, Mista Taiwo Oyedele, ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar sun hana tattalin arzikin Najeriya durƙushewa, inda ya bayyana cire tallafin man fetur a matsayin mataki mai muhimmanci da ya dawo da daidaito ga tattalin arzikin ƙasar.
Oyedele ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja yayin zaman taron koli na Ƙungiyar Masu Ɗaukar Ma’aikata ta Najeriya (NECA) na shekarar 2026.
Da yake jawabi a kan taken, “Sauye-sauyen Tattalin Arziki: Nasarori, Ƙalubale da Makoma,” ministan ya ce tattalin arzikin Najeriya ya kusa durƙushewa kafin gwamnatin ta fara aiwatar da sauye-sauyen, musamman cire tallafin man fetur.
“Kafin a cire tallafin, Najeriya ba ta da fiye da watanni uku kafin ta shiga mummunar matsalar ƙarancin man fetur.
“Mutane za su riƙa da kuɗi amma ba za su samu fetur su saya ba, saboda tsarin tallafin ya zama abin da ba za a iya ci gaba da ɗauka ba,” in ji shi.
Oyedele ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta riga ta kashe kuɗaɗen shigar da ake samu daga man fetur wajen biyan tallafin, har ta kai ga karɓar bashi bisa hasashen abin da za a samar daga ɗanyen mai nan gaba.
A cewarsa, hakan na nufin an riga an jinginar da wani babban kaso na albarkatun man fetur na ƙasar.
Ya ce sauye-sauyen sun dawo da kwanciyar hankali ga tattalin arzikin ƙasar bayan wani lokaci da aka fuskanci tashin farashin mai, hauhawar farashi, tsadar sufuri da kuma sauye-sauyen canjin kuɗaɗe.
“Mun bar lokacin rashin tabbas muka shiga zaman daidaito. Kuma wannan daidaito yana da matuƙar muhimmanci domin ba za a samu ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa ko samar da ayyukan yi ba idan babu shi,” in ji Oyedele.
Ya ce mataki na gaba na manufofin gwamnati shi ne haɓaka bunƙasar tattalin arziki mai samar da ayyukan yi.
A cewarsa, gwamnati na da burin samun bunƙasar GDP ta ainihi da kashi bakwai cikin ɗari a duk shekara, wanda zai haifar da ƙaruwar kuɗin shiga na kowane ɗan ƙasa da aƙalla kashi biyar cikin ɗari.
“Dole ne sadaukarwar da ‘yan Najeriya suka yi kada ta tafi a banza. Ya kamata mu ci gaba da goyon bayan waɗannan sauye-sauye domin cimma ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa ga kowa,” in ji shi.
Ministan ya ce an tsara sauye-sauyen ne domin kare ƙananan ‘yan kasuwa da masu ƙaramin ƙarfi, tare da kira ga masu hannu da shuni su ƙara ba da gudunmawa wajen tallafa wa manufofin gwamnati.
Ya jaddada cewa gwamnati ba za ta iya ci gaba da samar da jin daɗin jama’a ta hanyar buga kuɗi ba.
“Ba za mu iya gina tsarin jin daɗin jama’a mai ɗorewa ta hanyar buga kuɗi kawai ba. Dole gwamnati ta samar da isassun kuɗaɗen shiga kafin ta raba albarkatu domin kare marasa ƙarfi da ƙarfafa tattalin arziki,” in ji shi.
Ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya su fahimci manufofin gwamnati kafin su riƙa sukar su.
“Ba za ku iya ɗora gwamnati kan hanya ta hanyar fushi kawai ba. Ilimi da fahimta su ne mabuɗin tattaunawa mai amfani da kuma warware matsalolin ƙasa,” in ji Oyedele.
Ya kuma bayyana cewa bashin Najeriya na cikin yanayi mai kyau idan aka kwatanta da girman tattalin arzikinta, yana mai cewa ƙasar na cikin ƙasashen da ke da mafi ƙarancin kaso na bashi idan aka kwatanta da GDP, kuma tana samun rancen kuɗi cikin sauƙin ruwa.
Har ila yau, ya buƙaci ‘yan Najeriya su riƙa yaɗa sahihan bayanai game da tattalin arzikin ƙasar, yana mai gargadin cewa yaɗa mummunan hoto kan tattalin arziki na hana masu zuba jari zuwa ƙasar tare da ƙara tsadar bunƙasar tattalin arziki.
A nasa jawabin, Babban Daraktan Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIA), Dakta Kelechi Ohiri, ya yi kira da a ƙara zuba jari a fannin lafiya.
Ya ce zuba jari a harkar lafiya na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziki, yana mai bayyana albarkatun ɗan Adam a matsayin babbar dukiyar Najeriya.
A cewarsa, faɗaɗa tsarin inshorar lafiya zai rage talaucin da matsalolin lafiya ke haifarwa, ya ƙara yawan aiki tare da kare iyalai daga kashe kuɗaɗe masu yawa wajen neman magani.
Ya bayyana cewa adadin masu shiga tsarin inshorar lafiya ya ƙaru daga miliyan 16 zuwa miliyan 22, wanda ya nuna ƙarin kashi 34 cikin ɗari tun bayan fara aiwatar da dokar NHIA.
“Masu ɗaukar ma’aikata su tabbatar da cewa ma’aikatansu suna da inshorar lafiya domin hakan ba wai kawai alhakin zamantakewa ba ne, har ma yana ƙara yawan aiki.
“Mun kuma faɗaɗa tsarin ga marasa galihu,” in ji Ohiri.
Ya ƙara da cewa sama da mata 50,000 sun amfana da kulawar haihuwa ta gaggawa kyauta a asibitoci fiye da 270 da aka amince da su a faɗin ƙasar.
Ya kuma ce NHIA ta faɗaɗa amfanin inshorar lafiya domin taimakawa wajen yaƙi da cututtukan da ba masu yaɗuwa ba da ke ƙaruwa a Najeriya.
NAN
