
Shahararren mawaki Paul Okoye, wanda aka fi sani da Rudeboy, ya sake tayar da kura kan rikicin da ya dade yana ci gaba a tsakanin iyalan Okoye, inda ya bayyana cewa watakila ba zai taba yafe wa ɗan uwansa tagwaye, Peter Okoye ba.
Da yake magana a wata hira, Rudeboy ya bayyana matukar takaicinsa kan abubuwan da suka faru a tsakaninsu, yana mai cewa raɗaɗin da rikicin iyali ya jawo ya yi tsanani fiye da yadda zai iya mantawa da shi.
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa mawakin ya ce abin da ya fi ba shi ciwo shi ne yadda ɗan uwansa tagwaye ya bari sabanin da ke tsakanin iyalan ya kai matsayin da sulhu ya zama mai wahala.
A cewar Rudeboy, amincewar da ke tsakaninsu ta rushe gaba ɗaya, lamarin da ya sa yafiya ta zama abu mai matukar wahala duk da kiraye-kirayen da masoya da masu yi musu fatan alheri ke yi na su sasanta.
“Ba na tsammanin zan iya yafe wa ɗan uwana tagwaye. Abin da ya faru wani abu ne da ban taba tsammanin zai fito daga jinin cikina ba,” in ji shi.
Ya jaddada cewa matsalar ba ta shafi waka ko kuma alamar P-Square ba ce, illa rikicin iyali da cin amana, yana mai cewa akwai wasu abubuwa da ke barin tabo na har abada.
Rudeboy ya kuma bayyana cewa rikicin ya kai matsayin da dawo da kyakkyawar alaka ba zai samu ta hanyar neman afuwar jama’a ko kokarin sasanci kadai ba.
“Matsalar ba waka ba ce. Ta fi haka zurfi. Ta shafi iyali ne, amana da cin amana,” in ji shi.
Mawakin ya ce sau da dama a baya ya zabi yin shiru ne domin kare mutuncin iyalinsu, amma ya ga ya zama dole ya yi magana saboda yadda rikicin da ke tsakaninsu ke ci gaba da tayar da ce-ce-ku-ce.
Ya kara da cewa duk da cewa mutane da dama na ci gaba da fatan sake haduwar kungiyar P-Square, irin wannan fata ba ta la’akari da irin raɗaɗin da rikicin iyalin ya jawo ba.
A cewar Tribune, Rudeboy ya ce yanzu ya fi mayar da hankali kan rayuwarsa ta kashin kai, ‘ya’yansa da harkar wakarsa maimakon ci gaba da damuwa kan rikice-rikicen da ba a warware ba, yana mai cewa samun kwanciyar hankali shi ne abin da ya fi ba wa muhimmanci.
Sabbin kalaman nasa sun sake jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masoya, musamman wadanda suka yi fatan tagwayen mawakan za su rufe babin sabaninsu baki daya bayan da suka taba sasanta a baya bayan shekaru na rabuwa.
