
Daga DUMAH RANDONG
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya yi kira da a ɗauki matakin gaggawa da dorewa a matakin ƙasa domin magance matsalar yara da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake buɗe taron kwanaki uku na Basic Education in Nigeria BootCamp (BEN-B) a Jos, wanda aka yi wa taken, ‘Enhancing Access to Inclusive Quality Education and Bridging the Gap for Out-of-School Children in Nigeria’.
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ce ke jagorantar taron, wanda ke mayar da hankali kan sauya manufofi zuwa ayyuka na zahiri domin farfaɗo da ilimin firamare ta hanyar bincike da shaidar aiki.
An wakilci Gwamna Mutfwang da mataimakiyarsa, Ngo Josephine Piyo, inda ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da ake yi, har yanzu miliyoyin yara a Najeriya ba sa zuwa makaranta.
Ya ce wannan matsala na da tasiri mai tsanani ga ci gaban ƙasa, tsaro da zaman lafiya, yana mai cewa ba wai ƙididdiga kawai ba ce matsalar.
A cewarsa, yaran da ba sa zuwa makaranta suna wakiltar “mafarkai miliyoyi da aka jinkirta, basira da ba a amfani da ita ba da kuma makoma marar tabbas,” yana mai cewa idan ba a shigar da su cikin tsarin ilimi ba, za su fuskanci talauci, aikin yara, rashin tsaro, nisan makarantu da ƙarancin kayan koyo.
Gwamnan ya ce taken taron ya yi daidai da manufar Renewed Hope na Shugaba Tinubu, wadda ke da nufin samar da ci gaba mai haɗa kowa da kowa.
Ya bayyana cewa jihar Filato ta ɗauki matakai na musamman wajen faɗaɗa gine-ginen makarantu, ƙarfafa malamai da kuma haɗa al’umma domin tabbatar da cewa yara ba kawai suna shiga makaranta ba ne, har ma suna ci gaba da halarta.
Ya ce an gina tare da gyara ajujuwa 397 da wasu 557, wanda ya inganta yanayin koyo a faɗin jihar.Haka kuma ya ambaci sabuwar manufar ilimi ta “Alternative Learning Pathways” da kuma ƙa’idar mayar da ‘yan mata da suka yi aure ko masu juna biyu makaranta, a matsayin muhimman matakai na tabbatar da ilimi ga kowa.
Ya yi kira ga shugabanni a kowane mataki da su ƙara mayar da hankali kan ilimi, tare da jinjinawa Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da abokan hulɗa bisa shirya taron.
Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ya bayyana cewa kafin gwamnatin Shugaba Tinubu, Najeriya na da kimanin yara miliyan 15 da ba sa zuwa makaranta, amma ana samun ci gaba wajen sauya wannan yanayi.Ya ce gwamnati na ci gaba da ƙarfafa ilimin firamare da inganta yanayin koyo, tare da bunƙasa ilimin fasaha da sana’o’i.A cewarsa, ana gudanar da gangamin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta tare da gyare-gyare a tsarin karatu da horar da malamai.
Ministar Ƙasa a Ma’aikatar Ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad, ta bayyana taron a matsayin neman mafita mai ɗorewa ga matsalar ilimi, tare da sanar da cewa sabon tsarin rabon littattafai da ƙa’idojin ranking zai fara aiki a watan Satumba 2026.
Ta jaddada aniyar gwamnati na inganta ilimi bisa manufar Renewed Hope tare da kira ga malamai da su rungumi tsarin horar da malamai na zamani (Digital Teacher Training Policy).
Manyan jami’ai daga ma’aikatar ilimi da hukumomi daban-daban sun yaba da shirin a matsayin mataki mai muhimmanci wajen magance matsalar ilimi a matakin tushe.