Monday, November 23, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Abinci

Me ya sa dakuwa ke ci gaba da jan hankalin ‘yan Najeriya a wannan zamani?

by The Nigeria Standard
June 10, 2026
in Abinci
Reading Time: 5 mins read
0 0
Me ya sa dakuwa ke ci gaba da jan hankalin ‘yan Najeriya a wannan zamani?
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Tun kafin zuwan kayan ciye-ciye masu kunshi masu launi da kuma kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje, al’ummomin Najeriya sun dade suna dogaro da abinci na gargajiya wajen samun kuzari da gina jiki. Daya daga cikin irin wadannan kayan marmari shi ne dakuwa, wani nau’in abin ci na gargajiya daga Arewacin Najeriya wanda dandano, sinadarai masu gina jiki da kuma al’adarsa suka sa ya ci gaba da kasancewa abin so duk da sauyin zamani da salon cin abinci. LOIS DADU’UT ta yi nazari kan dalilan da suka sa wannan tsohon abin ci ke ci gaba da samun karbuwa musamman a tsakanin masu kula da lafiyarsu

A kasuwar da kayan ciye-ciye na zamani suka mamaye rumfuna da shaguna, dakuwa na ci gaba da rike matsayinsa a matsayin daya daga cikin shahararrun kayan marmarin gargajiya daga Arewacin Najeriya. Ana yin sa ne da gyada da aka gasa, garin gero ko dawa, sukari da kayan kamshi irin su citta da sauran kayan yaji.

Dakuwa ya kasance abin ci da ya shahara tun shekaru masu yawa, ana samun sa a kasuwanni, ana gabatar da shi a taruka da bukukuwa, sannan mutane kan dauke shi a matsayin abin ci mai samar da kuzari cikin gaggawa.

Baya ga kasancewa abin ciye-ciye, dakuwa na hada dandano mai armashi da sinadarai masu gina jiki, kuma masu sana’ar sarrafa shi sun ce har yanzu bukatarsa na nan daram.

Abin da ya fi jan hankalin masu son dakuwa shi ne saukin yadda ake hada shi. Gyadar da aka gasa tana ba shi dandano mai armashi, yayin da citta, kanumfari da sauran kayan yaji ke kara masa kamshi da dandano na musamman.

Sakamakon haka, ana samun wani abin ci mai laushi da saukin narkewa wanda ke dauke da zaqi na halitta, abin da masu amfani da shi da dama suka fi so fiye da kayan ciye-ciye da aka sarrafa a masana’antu.

“Da zarar ka dandani dakuwa mai kyau, ba za ka manta da shi ba,” in ji Grace Audu, wadda ta dade tana amfani da shi a Jos.

“Gyada da kayan yaji suna ba shi wani dandano na musamman, sannan laushinsa ya bambanta da busassun biskit da ake saye a shaguna. Yana ba ka jin cewa abin ci ne na halitta, ba wanda aka yi a masana’anta ba.”

Hadin dandano da sinadarai masu gina jiki

Masana harkar abinci sun bayyana cewa dakuwa ba dandano kawai yake bayarwa ba, har ma yana dauke da sinadarai masu amfani ga jiki. Gyada na samar da sinadarin furotin na tsirrai da kuma kitsen da ke da amfani ga lafiyar jiki, wadanda ke taimakawa wajen gyaran sassan jiki da kuma samar da koshi.

Haka kuma gero da dawa na dauke da sinadarin fibre, bitamin da ma’adanai da ke taimakawa wajen narkar da abinci da kuma inganta ayyukan jiki gaba daya.

“Dakuwa na samar da kuzari cikin sauri kuma yana taimakawa wajen ci gaba da samun kuzari na wani lokaci saboda haduwar gyada da hatsi a cikinsa,” in ji Haruna Bala, wani masanin abinci.

“Wannan ne ya sa mutane suka dade suna amfani da shi. Haka kuma yana samar da magnesium wanda ke taimakawa tsokoki da jijiyoyi, phosphorus da ke karfafa kasusuwa da hakora, da kuma Vitamin E wanda ke aiki a matsayin sinadarin kariya ga jiki.”

Ya kara da cewa kayan yajin da ake amfani da su wajen hada dakuwa suna da wasu fa’idodi ga lafiya.

“Citta da kanumfari na dauke da wasu sinadarai da ke taimakawa jiki wajen yakar matsalolin da ka iya lalata kwayoyin halitta,” in ji shi.

Sirrin ci gaba da karbuwarsa

A Kasuwar Jos North, Aisha Ibrahim ta shafe sama da shekara 15 tana sayar da dakuwa. A cewarta, sirrin nasarar wannan abin ci yana cikin yadda ake sarrafa shi.

“Har yanzu muna murza shi ta hanyar gargajiya bayan mun gasa sabuwar gyada kowace safiya, sannan mu hada ta da garin gero, dan sukari da citta,” in ji ta.

Aisha ta bayyana cewa duk da cewa wasu masu sana’ar yanzu suna amfani da injuna wajen sarrafa dakuwa, har yanzu kwastomomi da dama sun fi son wanda aka yi da hannu saboda yadda yake da dandano da laushi.

“Mutane da yawa suna cewa wanda aka murza da hannu ya fi dadi kuma ya fi armashi,” in ji ta.

“Uwaye suna saya wa ‘ya’yansu masu zuwa makaranta, yayin da matafiya kuma kan dauke shi lokacin tafiya mai nisa.”

Wata masaniyar abinci mai suna Jummai ta ce ana kara samun masu sha’awar abincin gargajiya a hankali.

“A baya matasa da yawa sun fi son kayan ciye-ciye na kasashen waje. Amma yanzu saboda karin wayar da kai game da cin abinci mai anfani ga lafiya, mutane da yawa suna komawa ga dakuwa da sauran kayan marmarin gargajiya saboda amfaninsu ga lafiya,” in ji ta.

Kare al’adun cin abinci mai lafiya

Duk da muhimmancin sinadaransa ga jiki, masana sun gargadi mutane da su rika cin dakuwa cikin matsakaici.

“Saboda yana dauke da gyada mai yawa kuma galibi ana kara masa sukari, yana iya kasancewa mai yawan kuzari da sinadarin kalori,” in ji masana.

“Mutanen da ke kula da nauyinsu ko kuma matakan sikarin jininsu ya kamata su rika cin sa a gwargwado.”

Ba kamar yawancin kayan ciye-ciye na zamani da ke dauke da sinadarai na kariya da kuma wasu abubuwan da ake kara musu ba, dakuwa na dogaro ne da kayan hadi na halitta masu sauki.

Yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan muhimmancin cin abinci mai lafiya da kuma kare abincin gargajiya, dakuwa na ci gaba da zama hujja cewa abincin gida na iya hada dandano, al’ada da sinadarai masu gina jiki cikin nasara.

Ci gaba da karbuwar sa na nuna hikimar da ke cikin tsarin abincin gargajiya da kuma yadda kayan abinci na gida ke ci gaba da kasancewa masu amfani da armashi.

Ga ‘yan Najeriya da dama, dakuwa ya fi zama abin ciye-ciye kawai. Ya kasance wata alama ta al’ada, zumunci da rayuwa mai kyau, yana hada al’ummomi da tsararraki ta hanyar soyayya da girmama daya daga cikin shahararrun kayan marmarin Arewacin Najeriya.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media