
Daga DUNG CHUNG
Kungiyar kwallon kafa ta Wisdom Football Academy da ke Trade Centre a Kuru ta nuna bajinta inda ta doke mai masaukin baki, Think Right Football Academy ta Bukuru da ci 2-1 a wasan kusa da na karshe, lamarin da ya ba ta tikitin zuwa wasan karshe na gasar kwallon kafa ta matasa da ake gudanarwa.
Wasan da aka dade ana jira ya cika alkawarin da aka yi masa, inda aka sha fafatawa mai zafi, daukar hankali da kuma nuna kwarewa daga bangarorin biyu kafin Wisdom Academy ta yi nasara a gaban dimbin magoya baya a Bukuru.
Gasar ta fara ne da halartar cibiyoyin horas da matasa 16 daga Karamar Hukumar Jos ta Kudu da wasu kananan hukumomi daban-daban na Jihar Filato, inda ta samar da wata dama ta gano da kuma nuna hazikan ‘yan kwallon kafa masu tasowa.
Wasan kusa da na karshe ya kasance daya daga cikin wasannin da suka fi daukar hankali a gasar baki daya.
Tare da goyon bayan magoya bayansu, Think Right Academy ta shiga wasan da kwarin gwiwa da burin amfani da filin gidansu domin samun gurbin zuwa wasan karshe.
Kungiyar ta Bukuru ta fara wasan cikin kuzari, tana rike kwallo da kuma kai hare-hare masu hatsari.
Sai dai Wisdom Academy ta zo da wata dabara ta daban.
Tun daga farkon wasan, kungiyar ta Kuru ta nuna tsari mai kyau a baya, da’a a tsakiya da kuma kaifin kai hare-haren gaggawa, abin da ya nuna cewa ta shirya tsaf domin kalubalantar mai masaukin baki.
Bayan fafatawar da aka yi ba tare da wata kungiya ta fi karfin daya ba, an samu kwallon farko a minti na 41 lokacin da Pwajok David ya yi anfani da kuskuren da masu tsaron baya suka yi wajen zura kwallo cikin natsuwa tare da bai wa Wisdom Academy jagora.
Kwallon ta girgiza magoya bayan gida tare da karkatar da ragamar wasan zuwa bangaren baki.
Sai dai Think Right Academy ta mayar da martani cikin gaggawa. Mintuna biyu kacal bayan haka Trevor Mark ya farke kwallon da bugun da ya cika ka’ida, lamarin da ya tayar da murna a tsakanin magoya bayan Bukuru.
Da wannan ne aka tafi hutun rabin lokaci ana kunnen doki 1-1.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, wasan ya kara zafafa yayin da kowacce kungiya ke neman kwallon nasara.
An yi gwabza fada mai zafi a tsakiya, masu tsaron baya suna dakile hare-hare masu hatsari, yayin da masu tsaron raga suka yi muhimman cetuka domin kare kungiyoyinsu.
Yayin da alamu ke nuna cewa za a tafi karin lokaci, Wisdom Academy ta samu kwallon da ta yanke hukuncin wasan.
Sunday Yohanna ya nuna kwarewa da natsuwa a cikin akwatin bugun fenareti kafin ya zura kwallo cikin salo mai kayatarwa domin dawo da kungiyar tasa kan gaba da kuma girgiza magoya bayan gida.
Kwallon ta sa Think Right Academy ta kara kaimi wajen neman farke kwallo, inda ta tura ‘yan wasanta gaba baki daya.
Sai dai duk da matsin lambar da ta yi a karshen wasan, masu tsaron bayan Wisdom Academy sun tsaya tsayin daka wajen dakile duk wani hari.
Da aka busa karshen wasa, an ga murna ta barke a tsakanin ‘yan wasa, masu horarwa da magoya bayan Wisdom Academy yayin da suke murnar nasarar da suka samu da ci 2-1 tare da kai wa wasan karshe.
Ga Think Right Academy kuwa, rashin nasarar ya kawo karshen tafiyar da ta yi mai kayatarwa a gasar.
Duk da haka, bajintar da ta nuna a duk tsawon gasar ta jawo mata yabo tare da nuna irin ci gaban da ake samu wajen bunkasa kwallon kafa a makarantar horas da matasan.
Bayan sakamakon wasan, wannan fafatawa ta sake tabbatar da irin dimbin hazikan ‘yan wasa da ke tasowa daga kwallon kafa ta matasa a Jihar Filato.
Daga cikin cibiyoyi 16 da suka fara gasar, Wisdom Academy Trade Centre, Kuru, ta samu damar fafatawa domin lashe kofin zakarun gasar, yayin da gasar ke ci gaba da nuna kyakkyawar makomar kwallon kafa a Jos ta Kudu da sauran wurare
