
Daga ALFRED NANMAN
Gwamnatin Jihar Filato ta bukaci al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da nuna hakuri bayan martanin jama’a da ya biyo bayan wani hukuncin Babbar Kotun Jihar kan bayar da takardun shaidar asali da na zama a Karamar Hukumar Jos Ta Arewa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, Kwamishinar Yada Labarai da Sadarwa ta jihar, Joyce Lohya Ramnap, ta ce gwamnati ta lura da muhawara mai zafi da kuma damuwar da hukuncin ya haifar tsakanin jama’a da masu ruwa da tsaki.
Ta ce gwamnati na nuna damuwa cewa wasu daga cikin kalaman da ake yi kan hukuncin na iya tayar da tarzoma ko rashin jituwa tsakanin al’ummomin da suka dade suna rayuwa cikin zaman lafiya tare.
Yayin da ta amince da hakkin ’yan kasa na kundin tsarin mulki na bayyana ra’ayoyinsu kan batutuwan da suka shafi muradun jama’a, gwamnatin ta bukaci mutane, kungiyoyi da masu ruwa da tsaki su kasance masu nuna kwarewa da sanin ya kamata a yayin bayyana matsayinsu.
Sanarwar ta bayyana cewa Karamar Hukumar Jos Ta Arewa, kamar kowace bangare da ba ta gamsu da hukuncin kotu ba, tana da damar neman gyara ta hanyar daukaka kara.
Saboda haka, gwamnatin ta yi kira ga dukkan bangarorin da su bari doka ta bi hanyarta ba tare da furta kalamai ko daukar matakan da za su iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a ba.
“Gwamnatin Jihar Filato na nan daram kan bin doka, mutunta kundin tsarin mulki da kuma kare ’yancin kai na bangaren shari’a,” in ji Ramnap.
Ta kara da cewa gwamnati ba za ta bari wani mutum ko kungiya su yi amfani da lamarin wajen ruruta kiyayya, haddasa rarrabuwar kawuna ko kawo barazana ga zaman lafiya da hadin kai a jihar ba.
Ramnap ta kuma ce batutuwan da suka shafi asali, zama dan kasa da kuma hakkokin mazauna wuri sun dade suna cikin muhawarar kundin tsarin mulki da ta kasa baki daya, don haka bai dace a takaita irin wadannan batutuwa ga karamar hukuma guda daya ba.
Ta yi kira ga mazauna jihar, shugabannin al’umma, na addinai, na matasa da kungiyoyin fararen hula da su kasance masu bin doka, kwantar da hankali tare da ci gaba da ba da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a fadin jihar.
Gwamnatin ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da adalci, daidaito, hada kai da kuma kare hakkoki da mutuncin daukacin mazauna jihar ba tare da la’akari da kabila, addini ko al’adunsu ba.