
Tsagin jam’iyyar PDP na Jihar Legas mai goyon bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi kira ga Cif Bode George da ya dawo cikin abin da ya kira “babban tsarin jagorancin jam’iyyar” domin sake farfaɗo da ita gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Sakataren tsare-tsare na tsagin jam’iyyar a jihar, Mista Hakeem Olalemi, ne ya yi wannan kira a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Legas ranar Lahadi.
NAN ta ruwaito cewa George, tsohon Mataimakin Shugaban PDP na Ƙasa, yana tare da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) ƙarƙashin jagorancin Dakta Kabiru Turaki, wanda Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ke mara wa baya.
George ya daɗe yana sukar Wike da kuma matakan da ya ɗauka game da PDP tun bayan ɓarkewar rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar.
Da yake magana kan halin da jam’iyyar ke ciki da kuma shirye-shiryenta na babban zaɓen 2027 a jihar, Olalemi ya ce har yanzu George babban jagora ne mai mutunci kuma muhimmin jigo a cikin iyalan PDP duk da sabanin ra’ayoyin da ke akwai a cikin jam’iyyar.
A cewarsa, gogewa da gudunmawar da George ya bayar ga PDP sun sa ya zama jigo mai matuƙar muhimmanci ga ci gaban jam’iyyar.
Olalemi ya ce yana da muhimmanci tsohon jami’in jam’iyyar na ƙasa ya ci gaba da kasancewa cikin babban tsarin jagorancin PDP domin samun ci gaba.
Ya ce, “Kullum muna maraba da Cif Bode George a PDP. Muna girmama shi sosai kuma akwai gurbi a gare shi a cikin jam’iyyar.
“Cif Bode George na son PDP. Ba zai iya barin PDP ba. Zai dawo cikin babban tsari domin yin aiki don ci gaban jam’iyyar.
“Shi tamkar mahaifinmu ne. Yana daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar, don haka babu wanda zai tambayi inda ya fito. Za mu yi masa kyakkyawar maraba idan ya dawo.”
Olalemi ya ce duk da wasu sabani tsakanin shugabanni da mambobi, PDP har yanzu iyali ɗaya ce.
Ya ƙara da cewa sulhu da haɗin kai na daga cikin al’adun jam’iyyar da suka daɗe suna taimaka mata wajen ci gaba.
Ya ce, “PDP iyali ce. Idan hannu ɗaya ya hukunta yaro, ɗayan hannun ne ke dawo da shi gida.
“Wannan ne ya sa muka ci gaba da kasancewa tare. Akwai gurbi ga duk wanda ke son ci gaban jam’iyyar.
“Dole ne mu manta da abubuwan da suka faru a baya. Muna son kowa da kowa da ke ɗaya ɓangaren ya dawo mu haɗa kai domin sake gina jam’iyyar.”
Jigon na PDP ya kuma buƙaci shugabanni su mara wa abin da ya kira Kwamitin Ayyuka na Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abdurahman Mohammed baya domin tunkarar zaɓen 2027 da ma bayan haka.
Ya ce wajibi ne dukkan mambobi da masu ruwa da tsaki su haɗa kai wajen ƙarfafa jam’iyyar.
Har ila yau, Olalemi ya yi watsi da fargabar da ake nunawa game da bullowar wasu dandamalin adawa a jihar.
Ya bayyana irin waɗannan ƙungiyoyin siyasa a matsayin marasa ƙarfi kuma waɗanda ba za su iya zama barazana ga matsayin PDP ba.
A cewarsa, “Babu wata jam’iyyar adawa a Legas da za a iya kwatantawa da PDP.
“Waɗannan ƙananan jam’iyyun da suke fitowa ba za su iya kaiwa matsayinmu ba ta fuskar gogewa, ƙwarewa da tsarin siyasa.
“Ku dubi tarihin ‘yan takararsu na gwamna. Wa a cikinsu ne za a iya kwatantawa da ɗan takararmu ta fuskar gogewa da ƙwarewa?”
Olalemi ya ce jam’iyyar ta fara ƙarfafa tsarinta a sassa daban-daban na jihar domin shirin zaɓen 2027.
Ya ce mambobin PDP na ci gaba da tattara magoya baya a matakan mazabu, ƙananan hukumomi da yankuna.
Ya ce, “Ina tabbatar muku cewa PDP a Jihar Legas ta shirya tsaf domin fafatawa da APC a babban zaɓen shekarar 2027.
“Mun shirya tsaf domin kalubalantar su a 2027. Muna sake fasalin injin siyasar mu a matakan ƙananan hukumomi, mazabu da yankuna.
“PDP tana ko’ina a Legas. Yawancin ‘yan takarar waɗancan jam’iyyun adawa sun taɓa kasancewa mambobin PDP ne.”
Olalemi ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa ‘yan siyasar da suka fice daga PDP za su dawo cikinta nan gaba.
Ya danganta wannan tabbaci da ƙarfin tsarin jam’iyyar da kuma kasancewarta a faɗin ƙasar nan.
“Waɗanda suka fita za su dawo. Dukkansu za su dawo PDP domin sun san inda ingantaccen tsari yake,” in ji Olalemi.
(NAN)