Thursday, November 19, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Ra'ayi

Talauci ne ke rura kasuwancin sayar da kwayayen haihuwar mata a Najeriya

by The Nigeria Standard
July 20, 2026
in Ra'ayi
Reading Time: 4 mins read
0 0
IWD: MRA urges governments to remove barriers, limiting women’s access to information
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga CHRISTIANA DANGYANG

A yau a Najeriya, wasu ‘yan mata na biyan kuɗin makaranta ta hanyar sayar da ƙwayayen haihuwarsu. Wasu kuma suna samun kuɗin sayen abinci, biyan haya, sayen wayoyin hannu da sauran buƙatun rayuwa daga abin da ake biyansu bayan an cire musu ƙwayayen haihuwa. Wannan lamari abin takaici ne matuƙa.

Wannan ba jita-jita ba ce, kuma ba wani abu ne da ke faruwa sau ɗaya-ɗaya ba. A maimakon haka, wata sabuwar al’ada ce da ke ƙara yaɗuwa a cibiyoyin kula da masu fama da matsalar rashin haihuwa da ke Abuja, Legas, Jos da sauran sassan ƙasar nan.

Fiye da komai, wannan al’amari ya fi bayyana irin tsananin talaucin da ya addabi Najeriya fiye da abin da yake faɗa game da matan da ke bayar da ƙwayayen haihuwar.

Mafi yawan masu bayar da ƙwayayen haihuwar ɗalibai ne, uwaye marasa galihu da kuma ‘yan mata masu shekaru tsakanin 20 zuwa 28, duk da cewa akwai wasu manyan mata da su ma ke shiga wannan harka.

Kafin a cire musu ƙwayayen haihuwar, ana yi musu allurar ƙara kuzarin ƙwai har na tsawon kwanaki 10 zuwa 14, ana ci gaba da duba lafiyarsu ta na’urar bincike, sannan a yi musu aikin cire ƙwayayen haihuwar wanda kan ɗauki kusan minti 45. A sakamakon haka, ana biyansu tsakanin naira dubu 120 zuwa dubu 200 a kowane zagaye.

Ga wasu, wannan kuɗi ne ke biyan kuɗin makaranta; ga wasu kuma yana biyan haya, sayen abinci ko taimaka wa iyayensu wajen ciyar da iyali. Wasu ma sun amince cewa suna yin hakan ne domin su yi rayuwa irin ta takwarorinsu.

Sai dai babbar tambayar ita ce, za a iya cewa wannan zaɓi ne da suke yi da yardar kansu? Idan madadin hakan shi ne yunwa, ficewa daga makaranta ko rasa matsuguni, shin za a iya cewa sun yanke wannan shawara cikin ‘yanci?

Babban abin da ke ƙara rura wannan al’amari shi ne talauci. Yayin da kuɗin makaranta ke ci gaba da ƙaruwa, hauhawar farashin kayan masarufi ke ƙara tsananta, kuma tallafin gwamnati ga marasa ƙarfi bai wadatar ba, matasa mata da dama sun rasa hanyoyin samun abin dogaro.

A irin wannan yanayi ne jikin mutum ya zama tamkar kadarar ƙarshe da za a iya musanyawa da kuɗi. Cibiyoyin kula da masu fama da rashin haihuwa sun fara zama wuraren da ake mayar da matsin rayuwa kuɗi. Najeriya ta gaza samar wa matasa isassun guraben aikin yi.

Haka kuma, karatun gaba da sakandare ya ƙara tsada, yayin da iyalai da dama ke fama da wahalar biyan ko da buƙatun yau da kullum. Saboda haka, bai kamata ya ba kowa mamaki ba idan wasu ‘yan mata sun fara kallon bayar da ƙwayayen haihuwa a matsayin hanyar tsira maimakon taimakon wasu.

A zahiri, matsin rayuwa ya zama mafi girman abin da ke tallata wannan sana’a. Talauci ne ke jawo masu bayar da ƙwayayen haihuwa, ba tallace-tallacen cibiyoyin lafiya ba.

Ci gaban wannan al’amari ya kuma haifar da wata babbar damuwa, wato yadda ake mayar da abin da ya kamata ya kasance aikin likitanci mai tsauraran ƙa’idoji zuwa wata sana’ar neman kuɗi. Duk da cewa ƙwararrun likitocin haihuwa suna cewa cire ƙwayayen haihuwa ba ya da haɗari idan an gudanar da shi yadda ya kamata, rahotannin da ke fitowa daga wasu mata da suka bayar da ƙwayayen haihuwar sun nuna akasin hakan.

Wasu sun koka kan rashin cikakken bayani kafin a yi musu aikin, gaggawar sallamarsu bayan an gama aikin da kuma rashin kula da su bayan sun koma gida.

Wani lamari mai tayar da hankali da ya faru a Jos ya ƙara fito da waɗannan damuwar fili. A cewar wata ƙawar mamaciyar da ta shaida wa ‘YANCIN DAN ADAM, wata budurwa ta fara fama da matsanancin ciwo da kumburi bayan an cire mata ƙwayayen haihuwa. Daga baya ta rasu, inda ake zargin rikicewar lafiyarta ta samo asali ne daga cutar Ovarian Hyperstimulation Syndrome (OHSS), wadda aka sani na iya faruwa sakamakon amfani da magungunan motsa ƙwayayen haihuwa.

Ƙawar tata ta yi zargin cewa ba a yi mata cikakken bayani kan haɗarin da aikin zai iya haifarwa ba kafin ta amince da shi.

Ko da yake ana sanya hannu a takardun amincewa kafin gudanar da irin wannan aiki, akwai alamu da ke nuna cewa a lokuta da dama ba a ba masu bayar da ƙwayayen haihuwar cikakken bayani kafin su yanke shawara. Haka kuma, rahotannin da ke cewa ana biyan kuɗi a sassa-sassa, ana ba da lada ga masu kawo sababbin masu bayar da ƙwayayen haihuwa, sannan ana ƙarfafa wasu daga cikinsu su ci gaba zuwa aikin ɗaukar ciki domin wasu (surrogacy), sun ƙara tayar da tambayoyi masu muhimmanci kan ɗabi’a. Bai kamata harkar lafiya ta zama wata hanyar kasuwanci da ke cin moriyar talaucin mutane ba.

Idan har za a ci gaba da gudanar da wannan sana’a, wajibi ne gwamnati ta sanya mata tsauraran ƙa’idoji. Ya kamata a tabbatar da cewa ana ba masu bayar da ƙwayayen haihuwa shawarwari masu zaman kansu kafin su yanke hukunci.

Haka kuma, dole cibiyoyin lafiya su bayyana dukkan haɗurran da aikin zai iya haifarwa, ciki har da OHSS, zubar jini, kamuwa da cututtuka da kuma yiwuwar matsalolin da ka iya tasowa nan gaba. Bugu da ƙari, ya kamata a kayyade adadin lokutan da mutum zai iya bayar da ƙwayayen haihuwa tare da tabbatar da cikakken kulawa bayan an gudanar da aikin.

Duk wani abu ƙasa da haka yana nuna gazawa wajen kare rayuwar mata masu rauni.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media