
Daga AFOSEH HAMZA
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce idan shi da Peter Obi suka samu nasara a zaben 2027, gwamnatinsu za ta bi hanyoyi daban-daban wajen magance matsalar tsaro, ciki har da tattaunawa da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a daren Litinin.
Ya ce magance matsalar tsaron kasar na bukatar dawo da amincewar jama’a ga hukumomin tsaro domin su rika ba da sahihan bayanan sirri ba tare da tsoro ba.
A cewarsa, mazauna yankunan da matsalar tsaro ta yi kamari sun san wadanda ke aikata laifukan da kuma wuraren da suke.
Ya ce, “Idan ka je yankunan da ake fama da rashin tsaro, mutane sun san kusan komai. Sun san inda masu aikata laifukan suke da kuma sunayensu.”
Sai dai ya ce mutane da dama ba sa son ba jami’an tsaro bayanai saboda irin abubuwan da suka fuskanta bayan sun taba yin hakan a baya.
A cewarsa, gwamnatinsu za ta sake gina amincewar jama’a tare da shiga tattaunawa da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka domin a shawo kansu su daina ayyukansu.
Ya ce, “Za mu ba mutane kwarin gwiwa, sannan mu tattauna da ‘yan ta’adda da sauran masu laifi domin ganin yadda za a dakile ayyukansu. Za mu zauna mu tattauna da kowa.”
Kwankwaso ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen amfani da sojoji da sauran hukumomin tsaro a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
