
Daga WILLIE ATTAH, Gombe
Reshen Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) na Jami’ar Jihar Gombe (GSU) ya bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 14 da ta biya musu bukatunsu, ko kuma su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.
Kungiyar ta sanar da hakan ne bayan taron majalisarta da aka gudanar ranar Talata.
Wata wasika da aka aike wa mambobin kungiyar da al’ummar jami’ar, wadda manema labarai suka samu a daren Talata, ta tabbatar da cewa reshen ya samu amincewar Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na ASUU na shiga yajin aikin bayan karewar wa’adin.
Wasikar mai dauke da kwanan watan 11 ga Agusta, 2026, na da take: “Permission by the ASUU National Executive Council to Commence a Total, Comprehensive and Indefinite Strike Action.”
A cewar wasikar, reshen ya karbi rahoton ziyarar da NEC ta kai jami’ar dangane da korafe-korafen kungiyar kan gwamnatin jihar da sauran batutuwan da ke jiran warwarewa.
Kungiyar ta ce ta yanke shawarar fara cikakken yajin aiki na dindindin domin tilasta a biya bukatunta idan har ba a magance matsalolin ba bayan karewar wa’adin.
Shugabar reshen kungiyar, Mustapha S. Muhammad, da Sakataren reshen, Aliyu Shelleng, ne suka sanya hannu a wasikar.
