
Daga ABBAS GUNGURA, Bauchi
Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya bukaci a karfafa cibiyoyin dimokuradiyya, jam’iyyun siyasa da kuma tabbatar da cikakken ’yancin bangaren shari’a domin kare dimokuradiyya a fadin Afirka.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a Taron Tattaunawar Dimokuradiyya na 2026 da Gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa ta Sir Ahmadu Bello da ke Bauchi.
An gudanar da taron ne a karkashin taken: “Beyond Elections: Can Political Parties and the Judiciary Save African Democracy?”
Tsohon shugaban, wanda shi ne shugaban zaman taron, ya nuna damuwa kan halin da dimokuradiyya ke ciki a Afirka, yana mai cewa tsarin da ake amfani da shi a nahiyar ya samo asali ne daga tsarin dimokuradiyyar kasashen Yamma da aka gada tun lokacin mulkin mallaka.
Ya kalubalanci shugabannin Afirka da masana ilimi da su sake nazarin tsarin tare da samar da tsarin dimokuradiyya da ya dace da tarihin nahiyar da yanayinta na siyasa da tattalin arziki.
Wanda ya kafa Gidauniyar Goodluck Jonathan kuma tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ya ce zabe kadai ba zai iya dore da dimokuradiyya ba.
Jonathan ya ce tabarbarewar dimokuradiyya tana farawa ne da raunana cibiyoyi, rashin mutunta kundin tsarin mulki, amfani da iko ba bisa ka’ida ba da kuma raguwar amincewar jama’a.
Ya kuma ce bai kamata a ci gaba da kiran tsarin da ake bi yanzu da “dimokuradiyyar Afirka” ba, yana mai kira da a samar da tsarin da ya dace da hakikanin yanayin nahiyar.
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce dimokuradiyya dole ta wuce gudanar da zabe kawai, yana mai jaddada bukatar jam’iyyun siyasa masu rikon amana da kuma bangaren shari’a mai cikakken ’yanci da jarumtaka wajen kare doka da amincewar jama’a.
Ya yaba wa Gidauniyar Goodluck Jonathan bisa ci gaba da shirya wannan taro na shekara-shekara da kuma kokarinta wajen inganta mika mulki cikin lumana da karfafa cibiyoyi a nahiyar Afirka.
Babbar Daraktar Gidauniyar, Misis Ann Iyonu, ta ce manufar taron ita ce karkatar da hankali daga batun zabe kadai zuwa cibiyoyi da hanyoyin da ke tabbatar da dorewar dimokuradiyya bayan an kammala kirga kuri’u.
Taron ya kunshi babban zaman tattaunawa da ya samu halartar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Namadi Sambo, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Labour, Peter Obi, tsohon Gwamnan Jihar Filato, Jonah Jang, Shugaban Jam’iyyar National Democratic Congress ta Ghana, wakilan Babban Ofishin Jakadancin Gambiya da sauran ’yan siyasa, jami’an diflomasiyya da masana ilimi.
