
Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sake jaddada goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, yana mai bayyana shi a matsayin ɗan jihar.
Adeleke ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Lahadi, jim kaɗan bayan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun na ranar 15 ga Agusta.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa gwamnan ya kuma yaba wa Tinubu kan abin da ya bayyana a matsayin goyon bayan da ya bayar domin ganin an gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci a jihar.
Adeleke ya ce, “A wannan lokaci, dole ne in nuna matuƙar godiya ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu, bisa gagarumin goyon bayan da ya bayar domin ganin an gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci.
“Shugaban Ƙasa ɗan Jihar Osun ne, don haka ina sake jaddada goyon bayan da na riga na ba shi domin ya sake neman wa’adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.”
Gwamnan ya riga ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, duk da cewa a lokacin yana cikin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), kafin daga bisani ya koma jam’iyyar Accord Party gabanin zaɓen gwamnan Osun na 2026.
Jami’in da ya jagoranci tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Joshua Ogunwole, Mataimakin Shugaban Jami’ar Federal University, Oye-Ekiti, ya ayyana Adeleke a matsayin wanda ya yi nasara da misalin ƙarfe 7:24 na safe ranar Lahadi.
Dan takarar Accord Party ya samu ƙuri’u 511,067, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya samu ƙuri’u 444,815.
Adeleke ya lashe ƙananan hukumomi 19 daga cikin 30 na jihar, yayin da Oyebamiji ya lashe 11.
Dan takarar African Democratic Congress (ADC), Najeem Salaam, ya zo na uku da ƙuri’u 17,180.
Nasarar ta tabbatar wa Adeleke da wa’adi na biyu a matsayin gwamnan Osun, bayan da aka zaɓe shi a 2022 a ƙarƙashin tutar PDP, kafin ya koma Accord Party domin shiga zaɓen 2026.
Tun da farko a ranar Lahadi, Adeleke ya gode wa Tinubu bisa kiransa ta waya domin taya shi murnar nasarar da ya samu, inda ya ce yana sa ran Oyebamiji ma zai kira shi domin taya shi murna.
Ya ce, “Eh, a nan babu mai nasara kuma babu wanda aka kayar. Ina son su zo. Ina kuma sa ran Oyebamiji, a matsayinsa na mutum mai wayewa, zai kira ni ya taya ni murna.”
Ya ƙara da cewa, “Tabbas ina so in yi amfani da wannan dama domin gode wa Mai Girma Shugaban Ƙasa. Shugaban Ƙasa ya kira ni kuma ya taya ni murna. Ina gode maka, Mai Girma Shugaban Ƙasa, saboda tabbatar da cewa dimokuraɗiyya ta ci gaba da wanzuwa, domin ka yi fafutuka a kanta.”