Saturday, October 24, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Labari

MBF ta ki amince da shirin kiwo a Tsakiyar Kasa

by The Nigeria Standard
August 18, 2026
in Labari
Reading Time: 3 mins read
0 0
MBF rejects proposed cattle ranching in Middle Belt
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga BENJAMIN AUTA, Kaduna

Kungiyar Middle Belt Forum (MBF) ta ki amincewa da sabon shirin gwamnatin tarayya na samarwa da ware filaye domin kiwon shanu a wasu jihohin yankin Tsakiyar Kasa, tana mai cewa shirin wata hanya ce ta boye ta kafa matsugunan makiyaya a yankin.

Kungiyar ta bayyana matsayinta ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’arta, Luka Biniyat, ya sanya wa hannu, wadda aka mika wa ‘YANCIN DAN ADAM a Kaduna.

MBF ta ce jihohin Adamawa, Kaduna, Plateau, Benue da Taraba, tare da Babban Birnin Tarayya Abuja, sun fuskanci munanan hare-hare da kaura da aka danganta da tashe-tashen hankula da wasu mayakan Fulani suka aikata.

Ta bayyana shirin a matsayin wata “hanyar kwace filaye da karfi” da ake kokarin gabatarwa a matsayin bunkasa kiwo, tana mai cewa hakan na iya kai wa ga kwace filayen kakanni na al’ummomin asalin yankin Tsakiyar Kasa.

Kungiyar ta kuma soki Ministan Raya Kiwo, Idi Maiha, tana mai cewa kasancewarsa Bafullatani kuma mai kiwon shanu na iya yin tasiri wajen yadda ake aiwatar da shirin.

Ta ce idan manufar shirin ita ce bunkasa kiwo da gaske, ya kamata a yi la’akari da dimbin filayen da ba a mamaye ba da ke wasu sassan arewacin Najeriya, ciki har da Jigawa, Kano, Sakkwato, Bauchi, Zamfara da arewacin Kebbi.

MBF ta kuma nuna shakku kan sauya wasu daga cikin jihohin da aka zaba domin fara shirin kiwon, tana mai cewa Kano na cikin jihohi shida da Ministan ya ambata a watan Janairun 2026, amma daga baya aka maye gurbinta da Nasarawa.

A cewar kungiyar, sauyin ya kara tayar da hankalin al’ummomin Tsakiyar Kasa kan manufar shirin da kuma illolin da zai iya haifarwa.

MBF ta ce an yi watsi da ko kuma an mamaye dubban kadada na filaye a yankin Tsakiyar Kasa sakamakon hare-hare, kashe-kashe da kaurar da ake dangantawa da kungiyoyin masu dauke da makamai.

Ta ce ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali wajen kare wadannan filaye da dawo da su ga mutanen da aka raba da su, maimakon ware wasu filaye domin matsugunan kiwon shanu.

Kungiyar ta kuma ce tsarin kiwon shanu na Wase a Jihar Plateau, wanda ta ce Ministan ya rika ambata a matsayin misali, ya fuskanci adawa daga wasu manoma da ’yan asalin jihar.

Saboda haka, MBF ta bukaci a dakatar da kuma soke abin da ta kira “shirin tsokana” nan take, tare da kira ga al’ummomin da abin ya shafa da su yi amfani da hanyoyin doka da kundin tsarin mulki wajen kalubalantar aiwatar da shi.

Ta kuma yi kira ga masana shari’a a fadin yankin Tsakiyar Kasa da su hada karfi wajen kalubalantar duk wani kwace ko rabon fili da ba ya bisa ka’ida a karkashin shirin.

Kungiyar ta kara kira ga ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa daga jihohin da abin ya shafa da su kare muradun al’ummominsu tare da gayyatar Ministan domin ya yi bayani kan shirin da kuma amsa damuwar da al’ummomin suka bayyana.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media