
Ga dubban manoma a Filato, noman dankalin turawa ba sana’ar lokacin damina kawai ba ce, domin shi ne ginshikin samun kudin shiga ga iyalai, samar da abinci da kuma ci gaban rayuwarsu. Sai dai wata cuta da za ta iya lalata gonar da ake sa ran za ta bayar da amfani mai yawa cikin ‘yan kwanaki ta sake jefa manoma cikin asara. DASPAN DANJUMA ya duba yadda cutar bature ke kara barazana ga noman dankalin turawa, irin asarar da manoma ke fuskanta da kuma kokarin samar da ingantattun iri da hanyoyin noma da za su taimaka wajen kare matsayin Filato a matsayin daya daga cikin jihohin da suka fi shahara wajen noman dankalin turawa
Manoman dankalin turawa a Jihar Filato na sake kirga asarar da suka tafka yayin da cutar bature ke yaduwa a manyan yankunan da ake noman dankalin turawa, tana lalata amfanin gona tare da barazana ga rayuwar manoma.
Cutar bature, wadda wata halitta mai kama da naman gwari mai suna Phytophthora infestans ke haddasawa, tana kai wa ganyaye, kara da tubers na dankalin turawa hari. A lokacin sanyi da yawan danshi, cutar tana yaduwa cikin sauri kuma tana iya rube amfanin gona cikin ‘yan kwanaki.
Fiye da shekaru 10 kenan manoman dankalin turawa na damina a Filato suna fama da wannan cuta. Sau da yawa tana bayyana makonni hudu zuwa shida bayan shuka, ta lalata aikin da manoma suka kwashe watanni suna yi tare da jari da suka zuba a gonakinsu.
Fata ta dushe a farkon wannan daminar
Raguwar bullar cutar a bara ta sa manoma da dama suka shiga wannan daminar da kwarin gwiwa. Wasu ma sun kara yawan filayen da suka noma, suna fatan samun amfanin gona mai yawa.
Amma wannan fata ba ta dade ba. Zuwa watan Yuni, makonni hudu zuwa shida kacal bayan shuka, aka fara samun bullar cutar bature, wadda ta yadu cikin sauri zuwa wasu gonaki. Wasu manoma, saboda rashin sanin abin da ya haddasa cutar, sun danganta lamarin da al’amuran tsafi da suka yi imanin cewa sai an yi musu tsarkakewa.
Daraktan Ayyukan Noma na Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara ta Jihar Filato, Langs Gyang, ya yi watsi da wannan ra’ayi, inda ya danganta bullar cutar da yanayin sanyi da ruwan sama.
“Yanayin sauyin yanayi ne kawai ya haddasa hakan. A bana muna samun ruwan sama mai karfi idan aka kwatanta da bara. Kun san cewa cutar bature tana samun damar yaduwa sosai a lokacin sanyi da yawan ruwan sama, wanda ke kara tsananta kamuwa da cutar da kuma saurin yaduwarta,” ya bayyana.
Illar cutar na bayyana karara a gonaki. Duk da amfani da magungunan kashe cututtuka, manoma da dama sun girbi amfanin da ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da bara.
Danjuma Iliya, wani manomi daga kauyen Konbiring da ke Ampang West, karamar hukumar Mangu, ya ce amfanin da ya samu ya ragu matuka.
“Bara, a wannan gonar dai, na sayar da buhu 45 lokacin da babu bullar cutar bature. Amma bana buhu 17 kacal na sayar, duk da cewa na fara fesa maganin cutar makonni biyar bayan shuka, sau biyu a mako,” ya koka.
Langs ya bayyana cewa ci gaba da noman dankalin turawa a gona daya tsawon shekaru na kara sa gonaki zama cikin hadarin kamuwa da cutar, ko da manoma sun fara amfani da maganin cutar da wuri.
Haka lamarin yake a Bokkos, inda amfanin gonar Ronald Bitrus Mabur ya ragu daga buhu 20 a bara zuwa buhu bakwai kacal a bana.
Asarar kudi ta fi tsanani ga manoman da suka karbi bashi domin gudanar da noman nasu.
Mista Zuhuman Datal na gundumar Kerang, ita ma a karamar hukumar Mangu, ya karbi bashin Naira 300,000 kan ruwa na kashi 10 cikin 100 na tsawon watanni uku domin gudanar da gonarsa mai girman hekta uku.
“Saboda tsadar ma’aikata da kayan aikin gona kamar taki da dusa, sai da na nemi bashin Naira 300,000 a watan Mayu kan ruwa na kashi 10 cikin 100. Tsarina shi ne zuwa watan Agusta in girbe amfanin gona, in biya bashin, sannan in yi kokarin sayen taki don noman masara. Amma yanzu ban samu ko rabin kudin ba. Na shiga rudani, ban san ta inda zan fara ba,” ya ce.
Ingantaccen irin dankali ya ba da fata
Duk da asarar da ake samu, akwai wani irin dankalin turawa da ke ba wasu manoma damar samun kyakkyawan fata. Irin dankalin da ake kira ‘Connect’, wanda manoma suka ce yana da juriya ga cutar bature, yana bayar da amfanin gona mai yawa a wasu gonaki.
Kenneth Da’ar na Ampang West ya shuka buhu takwas na irin ‘Connect’, inda ya girbi buhu 35.
“Ina cikin wadanda suka yi sa’a suka samu irin wannan iri, kuma ina gode wa Allah saboda hakan,” ya bayyana.
Wannan sakamakon na nuna muhimmancin samar da ire-iren dankalin turawa da za su iya jure wannan cuta, musamman a lokacin da sauyin yanayi ke kara samar da yanayin da ya dace da yaduwar cutar.
Hukumomin aikin gona sun kuma jaddada cewa rigakafi shi ne muhimmin makamin yaki da cutar bature.
Langs ya bukaci manoma su fara amfani da maganin kashe cututtuka tun da wuri, duk bayan makonni biyu, sannan su kara amfani da shi zuwa sau biyu a mako idan ruwan sama ya tsananta.
“Yawancin manoma suna jira har sai shuka ta fara nuna alamun kamuwa da cuta kafin su fara amfani da maganin. Amma abin da muke son manoma su sani shi ne, yawancin magungunan sun fi yin aikin rigakafi ne, ba maganin cutar bayan ta kamu ba,” ya ce.
Ya kuma gargadi manoma da kada su dogara da masu sayar da magungunan wajen sanin adadin da ya kamata a yi amfani da shi.
“Matsalar yawancin manoma ita ce suna dogaro da abin da masu sayar da maganin suke gaya musu game da adadin da za su yi amfani da shi, wanda galibi ba daidai ba ne, kuma hakan yana sa magungunan su kasa yin aiki yadda ya kamata,” ya jaddada.
Sakon a nan a bayyane yake: manoma ba za su iya jira har sai cutar bature ta bayyana kafin su dauki mataki ba. Yin amfani da magani a kan lokaci, bin adadin da ya dace da kuma inganta hanyoyin noma na iya taimakawa sosai wajen rage asara.
Shirin gwamnati da makomar noman dankali
Gwamnatin Jihar Filato na kokarin samar da hanyoyin magance matsalar cikin dogon lokaci.
Langs ya bayyana cewa kaddamar da wani sabon ingantaccen irin dankalin turawa da Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang ya yi na daga cikin muhimman matakan samar da ire-iren dankalin da ke da juriya ga cututtuka.
“Sabon irin yanzu yana hannun masu samar da iri domin su yi yawan samar da shi. A cikin shekara guda mai zuwa, wannan iri zai kasance a hannun kowane manomin dankalin turawa a Filato, wanda zai kawo karshen cutar bature,” ya ce.
Jihar ta kuma kafa dakin binciken tissue culture a karamar hukumar Mangu domin tsarkake sassan dankalin turawa da suka kamu da cuta tare da samar da kayan shuka marasa cuta.
“Babban manufar dakin binciken tissue culture na dankalin turawa shi ne tsarkake irin dankalin da ya kamu da cuta tare da samar da kananan tsirrai masu yawa, wadanda daga bisani za a sarrafa su su zama iri marasa cuta domin yawan samar da su,” Langs ya kara da cewa.
Ana sa ran shirin zai rage dogaro da irin dankalin da ake shigowa da shi daga kasashen waje tare da taimakawa wajen karewa da inganta ire-iren dankalin turawa na cikin gida.
A yanzu dai, yaki da cutar bature na bukatar daukar matakin gaggawa. Ingantattun iri, fasahar tissue culture da ingantattun hanyoyin noma suna ba da fata, amma manoma da dama sun riga sun shiga wani yanayi na karancin amfanin gona, karuwar basussuka da raguwar kudaden da suke samu.
Babban kalubalen da ke gaban hukumomi shi ne tabbatar da cewa hanyoyin magance matsalar da ake samarwa ba su tsaya a dakunan bincike, hannun masu samar da iri ko sanarwar gwamnati kadai ba. Manoma suna bukatar samun ingantattun iri, sahihin bayani, kayan aikin gona masu saukin kudi da kuma ma’aikatan fadada ilimin noma da za su rika ba su shawara kafin wata sabuwar damina ta zo.
Noman dankalin turawa a Filato na tallafa wa dubban iyalai tare da bayar da gagarumar gudummawa ga tattalin arzikin noma na jihar. Barin cutar bature ta ci gaba da lalata jarin manoma zai iya yin illa ba ga rayuwar manoma kadai ba, har ma da daukacin sarkar darajar dankalin turawa.
Har sai an samar da ire-iren dankalin da suka fi juriya ga cutar cikin yalwa tare da amfani da ingantattun hanyoyin dakile cututtuka a manyan gonaki, cutar bature za ta ci gaba da kasancewa babbar barazana. Don haka, yaki da cutar dole ne ya wuce mayar da martani bayan ta barke, ya koma kan rigakafinta tun kafin ta lalata wani sabon amfanin gona.
