
Daga ABDULRAHMAN IBRAHIM
Yayin da babban zaben shekarar 2027 ke kara karatowa, yanayin siyasar kasar na kara daukar zafi, yayin da magoya bayan jam’iyyun siyasa, masu neman takara da sauran masu ruwa da tsaki a siyasa ke kara ruruta wutar siyasa.
Wannan na bayyana ne ta hanyar yada farfaganda mai raba kan al’umma da kalaman batanci da ake amfani da su da sunan yakin neman zaben wasu jam’iyyun siyasa ko ‘yan takarar neman mukaman siyasa a zaben 2027.
Abin damuwa ne yadda wasu daga cikin mutanen da ke yada sakonni masu rarrabuwar kai da nuna bangaranci mutane ne masu ilimi da fahimta a cikin al’umma, ciki har da wasu shugabannin addini masu dimbin mabiya.
Saboda irin tasirin da suke da shi, wasu ‘yan siyasa kan yi amfani da wadannan mutane wajen isar da sakonninsu da kuma rinjayar mabiyansu.
Haka kuma, mawaka da masu rera yabo da wakokin siyasa masu goyon bayan wasu jam’iyyun siyasa kan kara dagula al’amura ta hanyar kai wa abokan hamayyarsu hari da kalamai masu muni da za su iya bata musu suna ko kuma bata sunan jam’iyyunsu.
Illolin yakin neman zabe mai raba kai
Irin wadannan dabarun yakin neman zabe sun dade ana amfani da su tun bayan kafuwar Jamhuriyya ta Hudu a shekarar 1999, inda ‘yan siyasa kan koma ga bata suna, zargin karya da kuma kai wa abokan hamayya hare-haren baki da na sirri.
Maimakon su mayar da hankali kan sukar manufofin siyasa cikin mutunci, wasu kan yi amfani da kalaman batanci, zagi da ma hare-haren jiki da sunan neman goyon bayan jama’a.
Idan aka yi la’akari da raunin al’ummar Najeriya, inda ake fama da kiyayya, shakku da rashin amincewa tsakanin jama’a, yakin neman zabe na bata suna na iya kara ruruta karancin zaman lafiyar da ake samu.
Wannan ya fi zama abin hadari a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin rashin tsaro, talauci, jahilci da sauran munanan dabi’un zamantakewa da gwamnatoci daban-daban suka kasa shawo kansu yadda ya kamata.
A daya bangaren kuma, ana zargin ‘yan siyasa da gangan suke ci gaba da amfani da irin wadannan rarrabuwar kai domin cimma muradunsu, ta hanyar karfafa gwiwar masu yada kalaman tunzuri da su ci gaba da yin hakan ba tare da daukar matakin ladabtarwa a kansu ba.
A duk lokacin da aka fara shirye-shiryen zabe a Najeriya, salon da wasu ‘yan siyasa ke amfani da shi wajen samun goyon bayan masu kada kuri’a kan kasance mai hadari, musamman idan yana karfafa kiyayya da rarrabuwar kai.
Mutanen da a baya suke zaune lafiya da hadin kai kan samu kansu ba zato ba tsammani cikin rarrabuwar kai bisa addini, kabila ko yankin da suka fito, har ta kai ga wasu ‘yan kasa suna kallon junansu a matsayin makiya ba tare da wani dalili mai tushe ba.
Sau da yawa, ‘yan siyasa marasa cancanta da masu son kai ne ke amfani da irin wadannan dabarun yakin neman zabe domin boye gazawarsu da raunin da suke da shi, da nufin samun nasarar zabe.
Masu kada kuri’a sun sha ganin illar haifar da irin wannan rarrabuwar kai, musamman ganin yadda wasu ‘yan siyasar da suka shafe shekaru suna rike da mukaman gwamnati suka kasa kawo gagarumar gudunmawa ga ci gaban al’umma ko inganta rayuwar mutanen da suke wakilta.
Da zarar irin wadannan ‘yan siyasa sun samu mulki, sau da yawa sukan fi mayar da hankali kan biyan bukatun kansu da cimma burinsu, yayin da jama’a ke ci gaba da jiran wani lokacin zabe kafin a sake sauraron korafe-korafensu.
Hanyar siyasa mai nagarta
Ya kamata siyasa ta kasance wata hanya ta yi wa jama’a hidima, maimakon ta zama hanyar haifar da tashin hankali, rashin tabbas da fargaba a tsakanin al’umma.
Ya kamata sadaukar da kai da kishin kasa su zama ginshikan shiga harkokin siyasa, tare da manufar rage radadin matsin tattalin arziki, rashin tsaro, talauci da rashin abubuwan more rayuwa na yau da kullum.
Saboda haka, ya kamata a dakile dabi’ar amfani da sakonnin yakin neman zabe marasa inganci idan ana son kasar ta samu ci gaba mai ma’ana.
Daya daga cikin manyan kalubalen da ake fuskanta shi ne gazawar hukumomin gwamnati wajen yin abin da ya kamata na tsara da kuma dakile yakin neman zabe na bata suna, ta hanyar gargadi ko daukar matakin hukunci kan wadanda ke aikata hakan.
Rashin aiwatar da dokoki yadda ya kamata ya karfafa wa mutane da dama, musamman masu amfani da kafafen sada zumunta, gwiwar yada sakonnin da suka ga dama, kai wa mutane hari, zagi da kuma yin kalaman tozarci ba tare da tsoron fuskantar hukunci ba.
Yaduwar karyace-karyace da labaran karya da sunan yakin neman zabe, da nufin bata sunan wata jam’iyyar siyasa ko wani mutum, na iya kawo cikas ga tsarin zabe.
Hakan na iya kuma hana ‘yan kasa sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu, tare da iya haifar da tashin hankali kamar yadda aka sha gani a lokacin zabukan baya.
Don haka, ya kamata ‘yan siyasa su rungumi hanyoyin yakin neman zabe masu inganci da da’a, tare da isar da sakonnin da za su karfafa hadin kai da zaman lafiya tsakanin al’umma.
Haka kuma, ya kamata a gargadi mawaka da masu rera yabo da wakokin siyasa da ke kai wa abokan hamayya hari, saboda saurin yaduwar wakoki da irin tasirin da suke da shi a kan halayyar jama’a.
A karshe, domin tsarin zabe ya kasance sahihi kuma abin amincewa, ya kamata a sanya ido sosai kan dukkan ayyukan siyasa, ciki har da yakin neman zabe, domin hana haifar da tashin hankalin da zai iya kai wa ga rugujewar doka da oda.
A daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubale da dama, daga ‘yan bindiga da Boko Haram zuwa talauci da karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta, ya kamata ‘yan siyasa su sake duba salon siyasarsu, su rungumi mutunci, nauyin da ke kansu da kuma kyawawan dabi’u a tsarin siyasa.
Matasa masu tasowa sun cancanci su gaji kasa mai hadin kai, zaman lafiya da ci gaba, ba kasar da siyasa da yakin bata suna suka kara raba kan al’ummarta ba.
