
Daga SEKYEN WALSHAK
Ƙungiyar Berom Diaspora Coalition (BDC) tare da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyi sun bayyana damuwa kan ci gaba da tashe-tashen hankula a Jihar Filato, inda suka yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa domin kwato ƙasashen kakanni da kuma sake tsugunar da al’ummomin da aka raba da muhallansu.
A wata taron manema labarai da aka gudanar a Jos, shugaban ƙungiyar kuma mai shirya taron, Barnabas Dazam, tare da BECO, BYM, BEC da BEWDA, ya ce ci gaba da hare-hare kan al’ummar Berom da sauran kabilu ya ƙara ta’azzara matsalar jinƙai a jihar da yankin Middle Belt.
Da yake magana a kan taken, ‘Reclaiming Our Lost Ancestral Lands and Resettlement of Our People’, Dazam ya tunatar da taron da suka yi a baya a ranar 12 ga Nuwamba, 2025, inda suka yi gargadi kan kisan gilla da korar jama’a daga muhallansu.
Ya ce daga Nuwamba 2025 zuwa Afrilu 2026, an kashe sama da mutane 500, yayin da wasu da dama suka jikkata, tare da lalata dukiya mai darajar miliyoyin naira a hare-hare daban-daban.
Ya ce an samu hare-hare a Barakin Ladi, Riyom, Jos South, Bokkos, Bassa da wasu sassan Jos North, ciki har da harin Angwan Rukuba na 29 ga Maris wanda ya kashe sama da mutane 30.
Dazam ya nuna damuwa cewa duk da gargadin da aka yi a baya, hare-hare na ci gaba a yankuna kamar Fan, Heipang, Kassa, Jol, Shonong, Gyel da Danwal, inda aka lalata gonaki tare da raba mutane da gidajensu.
Ya yi zargin cewa sama da ƙauyuka 70 na Berom sun fuskanci matsala, inda aka tilasta wa mazauna barin gidajensu, yayin da wasu ke zargin cewa an mamaye ƙasashensu.
Ya kuma ambaci Mahanga a ƙaramar hukumar Riyom a matsayin wuri da wasu ƙungiyoyi ke dangantawa da maboyar masu aikata hare-hare.
Ya koka da lalacewar gonaki da kuma yadda yankuna suka zama kufai, yana mai maimaita cewa ana ci gaba da raba mutane da muhallansu.
Dazam ya yi tambaya kan yadda hukumomin tsaro ke aiki, yana zargin jinkiri wajen bin bayanan sirri da kuma rashin daidaito a kama masu laifi.
Duk da jinjinawa ga Shugaba Tinubu da Gwamna Mutfwang bisa alkawuran kawo zaman lafiya, ya ce har yanzu ba a ga sauyi mai kyau a fili ba.
Ya bukaci a gudanar da cikakken bincike, a gurfanar da wadanda ake zargi tare da biyan diyya ga wadanda abin ya shafa.
Ƙungiyar ta kuma ƙara jaddada bukatar kafa ‘yan sandan jiha a matsayin mafita ga matsalolin tsaro.
A ƙarshe, Dazam ya roƙi ƙasashen waje da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da su shiga tsakani wajen kawo ƙarshen rikici da kuma taimakawa wajen mayar da ‘yan gudun hijira gidajensu.
Ya ce, “Tsaron al’umma ya kamata ya zama fifiko, ba wai amsa bayan faruwar hari ba.”
