Tuesday, November 24, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Yancin Dan Adam

Gwamnatin Plateau ta kafa kwamitin koli domin daidaita batutuwan da aka tattauna da Tinubu

by The Nigeria Standard
May 14, 2026
in Yancin Dan Adam
Reading Time: 4 mins read
0 0
Plateau sets up high-powered c’ttee to harmonise issues raised during Tinubu interaction
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Jihar Plateau ta kafa wani babban kwamitin ƙaramin sashi domin daidaita batutuwan da aka tattauna a taron da aka yi kwanan nan da Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, domin ƙarfafa alaƙa tsakanin jihar da gwamnatin tarayya kan muhimman batutuwan ci gaba da tsaro.

Gwamnatin ta ce matakin na da nufin samar da tsarin haɗin gwiwa mai inganci don tattaunawa na gaba da Fadar Shugaban Ƙasa da sauran hukumomin tarayya, domin amfanin ci gaban Jihar Plateau.

An ƙaddamar da kwamitin ne a ranar Talata, 12 ga Mayu, 2026, a Twin Theatre, New Government House, Rayfield, Jos, ta hannun Gwamna Caleb Mutfwang.

A cewar wata sanarwa da Kwamishinar Yaɗa Labarai da Sadarwa, Hon. Joyce Ramnap, ta sanya wa hannu kuma aka mika wa jaridar ‘YANCIN DAN ADAM, tsohon Gwamna Joshua Dariye ne ke jagorantar kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Pauline Tallen, Sheikh Ghazali Ismail Adam, Bishop Jwan Zumbes, Hon. Sani Muazu, Rev. Gideon Para Mallam, Hon. Sani Suleiman Maigoro, Barr. Panmak Lere, Mrs. Esther Gonda da Dr. Sumaya Hamza.

Akwai kuma Dr. Julie Sanda da Dr. Joseph Lenmang da za su taimaka a matsayin Sakatariyar kwamitin.

Gwamna Mutfwang ya umarci kwamitin da ya gano muhimman fannoni da ke bukatar taimakon gwamnatin tarayya, da bayar da shawarwari kan matakan tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai, tsaro da ci gaba mai ɗorewa.

Ya kuma bukaci kwamitin da ya yi shawarwari da duk masu ruwa da tsaki domin samun sakamako mai faɗi da ya haɗa kowa da kowa.

Haka kuma ya umurci kwamitin da ya mika rahotonsa cikin kwanaki bakwai daga ranar ƙaddamarwa.

Gwamnatin jihar ta bayyana kwarin gwiwa kan ƙwarewa da gogewar mambobin kwamitin, tare da buƙatar su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da ƙwazo domin ci gaban jihar.

Ta ce wannan mataki na nuna ƙudirin gwamnati na ci gaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya domin magance matsalolin tsaro da ci gaba da ke addabar jihar.

A na tunawa cewa Gwamna Caleb Mutfwang tare da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da tsofaffin gwamnoni, shugabannin addini da sarakunan gargajiya, sun gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja domin tattaunawa kan matsalar tsaro a jihar da hanyoyin kawo ƙarshen ta.

An gudanar da taron ne bisa gayyatar Shugaba Tinubu bayan buƙatar da masu ruwa da tsaki suka gabatar a lokacin ziyarar ta’aziyyarsa zuwa Jihar Plateau bayan kisan mutane sama da 30 a Angwan Rukuba, Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

Tawagar ta fara taruwa a Gidan Gwamnatin Plateau da ke Asokoro kafin daga bisani ta wuce Fadar Shugaban Ƙasa domin tattaunawar da ta ɗauki kusan sa’o’i bakwai, wanda aka bayyana a matsayin mafi tsawon taro da Shugaba Tinubu ya taɓa yi da wata tawaga a ƙasar.

A yayin taron, Shugaba Tinubu ya bukaci shugabanni daga Plateau da su koma gida da niyyar zaman lafiya, tare da kawo ƙarshen rikice-rikicen da ke ci gaba da faruwa.

Ya kuma buƙaci a sake duba rahotannin gwamnati na baya (White Papers) kan rikice-rikicen tsaro domin samo mafita mai ɗorewa.

A wajen taron, Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dr. Benard Doro, ya sanar da cewa Shugaba Tinubu ya amince da tallafin Naira biliyan 2 ga waɗanda rikicin Angwan Rukuba ya shafa.

Shugaban ƙasa ya ce: “Babu wata takura ko ƙa’ida mai hana mu faɗin gaskiya, muna nan ne domin nemo mafita ta dindindin ga rikici da tashin hankali. Na ji shugabanni, kowa yana neman zaman lafiya. Ta yaya za mu gina hanyar wannan zaman lafiya?”

Shugaba Tinubu ya ƙara jaddada bukatar haƙuri, adalci da haɗin kai, yana kira ga shugabanni da su haɗa kai domin hana sake zubar da jini a jihar.

Gwamna Mutfwang a jawabinsa ya gode wa Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarinsa na ci gaba da neman mafita ga matsalar tsaro a Plateau, yana mai tabbatar masa da ƙudirin shugabanni da masu ruwa da tsaki na gina haɗin kai tsakanin kabilu da addinai.

Mai Martaba Gbong Gwom Jos, Da Jacob Gyang Buba, ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu tare da roƙon a tura ƙarin sojoji zuwa jihar, sannan ya goyi bayan kafa ‘yan sandan jiha domin inganta tsaro a ƙasar.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media