Friday, September 18, 2026
  • #201 (no title)
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home News International

Kabilar Migili tana nemi kujerar Mataimakin Gwamnan Nasarawa a 2027

by The Nigeria Standard
June 7, 2026
in International
Reading Time: 2 mins read
0 0
Nasarawa 2027: Migili community appeals for Deputy Gov. slot
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga DAVID MICHAEL, Lafia

Kungiyar Raya Al’adun Migili (MCDA) ta bukaci Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, da ya yi la’akari da bai wa daya daga cikin ‘ya’yan kabilar Migili damar zama mataimakin gwamna a zaben gwamna na shekarar 2027.

Shugaban kungiyar na kasa, Dakta Abu Isaac Ishaq, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Lafia, babban birnin jihar.

Ya nuna damuwarsa cewa duk da irin kuri’un da al’ummar Migili ke bayarwa a zabukan jihar tun bayan dawowar dimokuradiyya a shekarar 1999, har yanzu ba su samu manyan mukamai kamar kujerar mataimakin gwamna ba.

Dakta Abu ya ce sarakunan gargajiyar Migili sun zagaya wajen sauran sarakunan kabilu a jihar domin neman goyon baya kan wannan bukata.

A cewarsa, “Mun zagaya muna roko da neman goyon bayan ‘yan uwarmu. Wannan aiki ne na daukacin al’ummar Migili. A karon farko, dalibai, matasa, kungiyar raya al’adu da majalisar sarakuna sun hada kai domin cimma wannan buri.

“Al’ummar Migili mutane ne masu zaman lafiya, masu bin doka kuma masu tsari. Mu ne farkon wadanda suka zauna a tsohuwar Lafia Division. Saboda haka muna rokon Gwamnan Jihar Nasarawa, wanda shi ne jagoran APC a jihar, da ya ba Migili damar samun kujerar mataimakin gwamna.

“Muna rokon cewa a wannan karon a ba mu wannan matsayi. Idan hakan ta faru, za mu yi farin ciki matuka.

“A matsayina na shugaban kabilar, mun amince baki daya cewa idan aka ba mu kujerar mataimakin gwamna, za mu hada kan kuri’unmu domin tabbatar da APC ta yi nasara a zaben 2027.”

Ya kara da cewa al’ummar Migili (Koro) suna zaune a kananan hukumomi biyar na jihar da suka hada da Lafia, Doma, Obi, Awe da Keana, kuma suna da kimanin kuri’u dubu 50.

An tuna cewa a baya matasan Migili a jihar sun yi irin wannan kira ga Gwamna Abdullahi Sule da ya dauki daya daga cikinsu a matsayin abokin takarar gwamna domin su ji suna da wakilci a harkokin mulkin jihar.

Mai magana da yawun kungiyar, Kwamared Sunday Aleku, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Lafia.

Ya ce al’ummar Migili suna zaune a sassa daban-daban na jihar kuma suna da muhimmiyar rawa a harkokin siyasa da zamantakewa na Nasarawa.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • #201 (no title)
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media