
Daga HASSAN SHALLPELLA, Yola
An nada Dr. Sumayya Sabo, malama kuma Mai Kula da Sashen Fasahar Sadarwa da Bayanai (IT) a Jami’ar American University of Nigeria (AUN) da ke Yola, a matsayin Mai Tsara da Gudanar da Shirye-shiryen Adamawa Digital Academy.
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ne ya sanar da nadin ta hannun Babban Sakataren Yada Labaransa, Humwashi Wonosikou.
A cewar wata sanarwa da kakakin gwamnan ya fitar, nadin wani bangare ne na kokarin da gwamnati ke yi na fara aiwatar da ayyukan Adamawa Digital Academy gaba daya.
Makarantar wata babbar manufa ce da ke karkashin Tsarin Sauya Fasahar Zamani na Adamawa 2.0, wanda ke da burin horas da matasa da ma’aikatan gwamnati sama da 100,000 kan dabarun fasahar zamani da sabbin fannoni na kimiyya da fasaha.
Ana sa ran Dr. Sabo za ta jagoranci gudanar da ayyukan yau da kullum na makarantar.
Haka kuma za ta kasance mai kula da rajistar dalibai, hulda da masu ruwa da tsaki, tafiyar da harkokin ilimi da kuma aiwatar da yarjejeniyoyin hadin gwiwa da cibiyoyi daban-daban.
Manufar ita ce a mayar da makarantar daya daga cikin manyan cibiyoyin koyar da fasahar zamani a Najeriya da ma nahiyar Afirka baki daya.
Gwamna Fintiri ya taya Dr. Sabo murnar wannan nadi tare da yi mata fatan alheri da nasara wajen gudanar da sabon aikin.
Dr. Sabo kwararriya ce a fannin Tsarin Bayanai (Information Systems), mai kula da harkokin ilimi da kuma gogaggiyar mai gudanar da shirye-shirye.
Tana da gogewa sosai a bangarorin bunkasa dabarun fasahar zamani, gudanar da harkokin ilimi, shirye-shiryen kirkire-kirkire da kuma tafiyar da harkokin fasahar sadarwa da bayanai.
