Sunday, October 25, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Labari

Mutfwang ya taya Kwashi murnar zama Akbishop na Chadi

by The Nigeria Standard
June 9, 2026
in Labari
Reading Time: 2 mins read
0 0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya taya Mai Martaba Akbishop Benjamin Kwashi murnar nadinsa da kuma naɗa shi a matsayin Akbishop na Chadi ƙarƙashin Lardin Alexandria da ke Arewacin Afirka, inda ya bayyana cewa wannan karin girma wata shaida ce ta irin gudunmawar da ya bayar tsawon shekaru wajen hidimar coci da kuma bil’adama.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Harkokin Jama’a na Gwamnan Jihar Filato, Gyang Bere, ya fitar a ranar Talata, Mutfwang ya ce nadin ya nuna irin jajircewar Akbishop Kwashi wajen bautar addinin Kirista, jagoranci da kuma yi wa al’umma hidima.

Gwamnan ya ce tsohon Akbishop na Cocin Anglican na Jos ya yi fice a tsawon shekarun da ya shafe yana gudanar da hidima, wadda ta zarce iyakokin Najeriya da ma nahiyar Afirka, lamarin da ya sa ya samu girmamawa saboda fafutukarsa wajen tabbatar da zaman lafiya, adalci, sulhu da kuma farfaɗo da rayuwar addini.

Ya kuma yaba da gudunmawar da Kwashi ya bayar wajen bunƙasa coci da ci gaban al’umma ta hanyar ba da jagoranci, horar da matasa da kuma ayyukan jin ƙai.

A cewar Mutfwang, nadin ba wai babban nasara ce ga Akbishop Kwashi kaɗai ba, har ma abin alfahari ne ga Jihar Filato da Najeriya baki ɗaya.

Ya ce, “Wannan karin girma ya nuna irin tasirin da hidimar Akbishop ɗin ta yi a wurare da dama, da kuma irin amincewar da aka yi da hikimarsa da gogewarsa, tare da sadaukarwarsa ga hidimar Allah da bil’adama.”

Gwamnan ya bayyana fatansa cewa wa’adin mulkin cocin da Akbishop Kwashi zai yi zai taimaka wajen ƙarfafa ci gaban ruhaniya, haɗin kai da zaman lafiya, tare da ƙara bunƙasa ayyukan coci a Chadi da ma sauran yankunan da ke makwabtaka.

Ya ce, “Yayin da Akbishop Kwashi ke karɓar wannan muƙami mai tsarki kuma mai tarihi, ina addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba shi ƙarin hikima, ƙarfi, alheri da jagoranci domin ya yi wa bayin Allah jagoranci yadda ya kamata tare da ci gaba da yaɗa aikin coci a Chadi da sauran sassan duniya.”

Mutfwang ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa jagorancin Kwashi zai zama abin koyi ga sabon ƙarni na shugabannin Kiristoci a faɗin Afirka da kuma sauran sassan duniya.

A ƙarshe, ya taya Akbishop ɗin murna a madadin gwamnatin Jihar Filato da al’ummarta, tare da yi masa fatan samun nasara da albarka a sabon muƙamin da aka ɗora masa.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media