
Daga SABASTINE ABU, Abuja
Majalisar Wakilai ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin kasa da ke neman kafa rundunar ’yan sandan jihohi a fadin Najeriya, a wani mataki da ake ganin zai kawo babban sauyi a tsarin tsaron kasar.
Majalisar ta amince da kudirin ne a ranar Alhamis yayin zaman kwamitin daukacin majalisar.
Kudirin mai taken, “Kudirin Dokar Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 domin tanadar kafa ’Yan Sandan Jihohi da sauran batutuwa masu alaka da haka (Gyara Ta Shida), 2026,” ya samu amincewar ’yan majalisar bayan doguwar muhawara.
Kudirin ya samu nasarar tsallakewa ne bayan mataimakin kakakin majalisar kuma shugaban kwamitin duba kundin tsarin mulki, Benjamin Kalu, ya gabatar da rahoton kwamitin.
Sakamakon kuri’ar da aka kada ya nuna goyon baya mai karfi daga ’yan majalisar, inda mutum 289 suka kada kuri’ar amincewa da kudirin, mutum daya ya kaurace wa kada kuri’a, yayin da babu wanda ya yi adawa da shi.
Kudirin na neman samar da tsarin aikin ’yan sanda biyu da zai kunshi ’Yan Sandan Tarayya da kuma ’Yan Sandan Jihohi domin fuskantar kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta ta hanyar bai wa jihohi damar taka rawar gani wajen tabbatar da tsaro.
Yadda tsarin zai gudana
A karkashin kudirin, za a yi wa Sashe na 214 na kundin tsarin mulki kwaskwarima domin amincewa da kafa rundunar ’Yan Sandan Tarayya da kuma ta Jihohi.
Majalisar Tarayya za ta kasance mai ikon tsara tsarin aiki, gudanarwa da kuma karfin ikon ’Yan Sandan Tarayya, tare da kafa ka’idojin da jihohi za su bi wajen kafa da gudanar da rundunonin ’yan sandansu.
Kudirin ya tanadi cewa babu wata rundunar ’yan sandan jiha da za ta fara aiki sai bayan majalisar dokokin jihar ta amince da dokar kafa ta, sannan kuma a tabbatar ta cika sharuddan da Majalisar Tarayya ta gindaya.
Haka kuma, kudirin ya bayyana cewa rundunar ’Yan Sandan Tarayya za ta ci gaba da aiki a kowace jiha har sai rundunar ’yan sandan jihar ta fara aiki yadda ya kamata.
Domin kauce wa amfani da iko ba bisa ka’ida ba, kudirin ya sanya iyaka ga yadda gwamnatin tarayya za ta iya shiga harkokin rundunar ’yan sandan jihohi.
A karkashin sabon tsarin, rundunar ’Yan Sandan Tarayya za ta iya shiga tsakani ne kawai idan doka da oda sun tabarbare, ko kuma idan gwamna ya nemi hakan, ko kuma idan rundunar ’yan sandan jihar ta kasa gudanar da ayyukanta saboda matsalolin gudanarwa, kudi ko aiki.
Nadin shugabanni da tsarin kulawa
Kudirin ya kuma tanadi sauye-sauye masu muhimmanci a tsarin shugabanci da gudanar da rundunar ’yan sanda.
A karkashin gyaran, shugaban kasa ne zai nada Sufeto Janar na ’Yan Sanda bisa shawarar Majalisar Kula da Harkokin ’Yan Sanda ta Kasa daga cikin jami’an rundunar ’Yan Sandan Tarayya masu aiki, sannan Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin.
Haka zalika, gwamna ne zai nada Kwamishinan ’Yan Sandan Jiha bisa shawarar Majalisar Kula da Harkokin ’Yan Sanda ta Kasa daga cikin jami’an rundunar ’yan sandan jihar masu aiki, bayan samun amincewar majalisar dokokin jihar.
Kudirin ya kuma bai wa gwamnoni ikon bayar da umarni na halal ga kwamishinonin ’yan sandan jihohi kan batutuwan da suka shafi tsaron jama’a da tabbatar da zaman lafiya.
Sai dai idan an ga irin wadannan umarni sun saba wa doka ko kuma ka’idojin aikin ’yan sanda, za a iya mika batun ga Majalisar Kula da Harkokin ’Yan Sanda ta Kasa domin yanke hukunci na karshe.
Har ila yau, kudirin na neman yin gyara ga Sashe na 84 na kundin tsarin mulki ta hanyar maye gurbin Majalisar Kula da Harkokin ’Yan Sanda ta Kasa da Hukumar Ayyukan ’Yan Sandan Tarayya da sabbin sunayen da suka dace da tsarin da ake son kafawa.
Amincewar da Majalisar Wakilan ta yi wa kudirin na daga cikin manyan matakan da ake dauka wajen sake fasalin kundin tsarin mulkin kasa, tare da sake tayar da muhawarar da aka dade ana yi kan ko kafa ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya.
Kafin kudirin ya zama doka, dole ne Majalisar Dattawa ta amince da shi, sannan ya samu goyon bayan akalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi kafin shugaban kasa ya sanya wa dokar hannu.
Idan kudirin ya zama doka, ana sa ran zai samar da tsarin tsaro mai matakai daban-daban da zai taimaka wajen yaki da ayyukan ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane, ta’addanci da sauran matsalolin tsaro ta hanyar karfafa tsarin tsaro a matakin jihohi.
