Thursday, September 17, 2026
  • #201 (no title)
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home News International

KOFIN DUNIYA 2026: Shin Cape Verde ce sabuwar ƙasar ƙwallon ƙafar Afirka?

by The Nigeria Standard
June 23, 2026
in International, Wasanni
Reading Time: 7 mins read
0 0
Is Cape Verde Africa’s new football powerhouse?
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga VICTOR GAI

Bajintar da ƙasar Cape Verde ke nunawa a gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2026 da ake yi a ƙasashen Amurka, Kanada da Mexico ta sanya ana ta muhawara kan ko ƙasar tsibirin ce sabuwar ƙasar da za ta mamaye harkar ƙwallon ƙafa a Afirka.

Cape Verde, wadda ke buga gasar cin kofin duniya a karon farko, ta ci gaba da ba duniya mamaki bayan da ta tashi kunnen doki 2-2 da Uruguay a wasan rukuni na H da aka buga a birnin Miami da ke Amurka a daren Lahadi.

Duk da kasancewarta ta 63 a jadawalin FIFA, Cape Verde ta nuna ƙwazo da jarumta a karawarta da Uruguay mai matsayi na 18 a duniya.

Tun da farko dai ƙasar ta ja kunnen doki babu ci da ci da Spain, wadda ke matsayi na uku a duniya, a wasanta na farko a rukuni.

Wannan sakamako ya sa duniya ta fara mayar da hankali kan ƙungiyar da ake wa lakabi da Blue Sharks, musamman mai tsaron ragarta Vozinha wanda ya yi fice matuƙa a kafafen sada zumunta.

A wasan da Uruguay, Kevin Pina ne ya fara zura ƙwallo wa Cape Verde a minti na 21 da wata gagarumar harbi daga nesa.

Sai dai M. Araujo ya farke wa Uruguay a minti na 44 bayan kuskuren da masu tsaron bayan Cape Verde suka yi.

Daga bisani Canobbio ya ƙara wa Uruguay ta biyu a lokacin ƙarin lokaci na rabin farko, wanda ya sa suka tafi hutun rabin lokaci suna kan gaba da ci 2-1.

Da aka dawo daga hutun rabin lokaci kuwa, Cape Verde ta sake dawowa da ƙarfi.

Dan wasan da ya shiga daga baya, Hélio Varela, ya farke wa ƙasarsa a minti na 61 bayan ya ci moriyar kuskuren tsaron baya na Uruguay.

Wasan ya zarce hasashen masu yin caca tare da bai wa masoya ƙwallon ƙafa nishaɗi, dabaru da kuma ƙwarewar wasa mai inganci.

Masu sharhi sun yaba wa Cape Verde saboda yadda take taka leda ba tare da tsoro ba a gaban manyan ƙasashen ƙwallon ƙafa.

Wani mai sharhin wasan ya ce: “Magoya bayan Cape Verde ba su yarda da abin da ƙungiyarsu ke yi a wannan gasar ba. Suna taka leda da kwarin gwiwa kuma ba sa nuna alamar tsoro.”

Ya kuma bayyana ƙungiyar a matsayin wadda ke da tsari da kuma bin dabarun wasa yadda ya kamata.

A baya Cape Verde ba ta cikin manyan ƙasashen ƙwallon ƙafa a Afirka.

Sai dai ci gaban da ta samu a shekarun baya-bayan nan ya sa ta zama abin koyi ga sauran ƙasashe.

A gasar AFCON ta 2024, Cape Verde ta kai wasan kusa da na kusa da na ƙarshe kafin Afirka ta Kudu ta fitar da ita a bugun fenariti.

Har ila yau, ta jagoranci rukuninta a wasannin neman tikitin zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026 inda ta doke ƙasashe irin su Kamaru da Libya.

Mutane da dama ba su yi tunanin za ta samu tikitin zuwa gasar ba.

Yawancin ‘yan wasanta suna taka leda ne a ƙananan lig-lig na Turai kuma ba su da gogewa irin ta manyan ‘yan wasa.

Sai dai duk da haka ta ci gaba da karya hasashen masu nazari.

Yanzu haka Cape Verde tana da maki biyu bayan wasanni biyu kuma za ta kara da Saudiyya a wasanta na ƙarshe a rukuni.

Idan ta yi nasara za ta kai zagayen ‘yan wasa 32 na gasar.

Haka kuma tana iya tsallakewa a matsayin ta biyu a rukuni ko kuma cikin mafi kyawun ƙungiyoyin da suka zo na uku gwargwadon sauran sakamakon wasanni.

Alamu dai sun nuna Cape Verde za ta ci gaba da ba duniya mamaki tare da kafa kanta a matsayin ɗaya daga cikin sabbin ƙasashen da ke tasowa a harkar ƙwallon ƙafa ta Afirka.

Mbappé ya ce Messi zai ci gaba da kafa tarihi a Gasar Kofin Duniya

Kyaftin din tawagar Faransa, Kylian Mbappé, ya bayyana cewa bai yi mamakin yadda Lionel Messi ke ci gaba da kafa tarihi a gasar cin kofin duniya ba, yana mai bayyana tauraron na Argentina a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan da duniya ta taɓa gani.

Messi ya daidaita tarihin Miroslav Klose na cin ƙwallaye 16 a gasar cin kofin duniya bayan da ya zura hat-trick a wasan da Argentina ta doke Algeria da ci 3-0.

Mbappé, wanda ya taɓa buga wasa tare da Messi a Paris Saint-Germain, yanzu yana da ƙwallaye 14 a tarihin gasar bayan ya ci biyu a wasan da Faransa ta doke Senegal da ci 3-1.

Mbappé ya ce, “Tun tuni na san Messi zai ci gaba da zura ƙwallaye. Hakan dai dabi’arsa ce. Yana gaba da ni, ni kuma ina binsa. Zan ci gaba da zura ƙwallaye domin taimaka wa ƙasata ta kai inda ya kamata.”

Dan wasan na Real Madrid ya ce bai yi mamakin sabon tarihin da Messi ya kafa ba.

Ya ce, “A bayyane yake cewa Messi shi ne mafi kyau a duniya, haka kuma Cristiano Ronaldo. Tsawon shekara 16 Messi yana nuna irin baiwar da Allah Ya ba shi. Ni kuma zan ci gaba da nuna baiwata a manyan matakai tare da taimaka wa ƙasata.”

Mbappé ya ƙara da cewa zura ƙwallaye na da muhimmanci idan har Faransa na son sake lashe kofin duniya.

Ya ce, “Idan kana cin ƙwallaye, damar kaiwa nesa tana ƙaruwa. Burina shi ne lashe kofin duniya.”

Mbappé ya lashe kofin duniya a 2018 amma ya rasa damar ɗaga shi a karo na biyu a 2022 lokacin da Argentina ƙarƙashin jagorancin Messi ta doke Faransa a wasan ƙarshe ta hanyar bugun fenariti.

A yau Litinin ne Mbappé zai buga wasansa na 100 da tawagar ƙasarsa lokacin da Faransa za ta kara da Iraki a wasan rukuni na I da za a buga a Philadelphia.

Ya ce, “Kai wa wasa na 100 babban tarihi ne, musamman idan hakan ya faru a gasar kofin duniya. Babu abin da ya fi buga wa ƙasa muhimmanci.”

Ya ƙara da cewa, “Wasa ne na musamman a gare ni, amma dole mu yi nasara domin tsallakewa zuwa mataki na gaba.”
ESPN

Man City ta amince da biyan Fam Miliyan 17 domin naɗa Maresca a matsayin magajin Guardiola

Rahotanni sun bayyana cewa Manchester City ta cimma yarjejeniya da Chelsea domin ɗaukar Enzo Maresca a matsayin wanda zai gaji Pep Guardiola bayan ficewarsa daga kulob din.

Ana sa ran zakarun gasar Firimiya ta Ingila za su biya kusan fam miliyan 17 a matsayin diyya domin samun damar ɗaukar kocin ɗan asalin Italiya.

Bayan tabbatar da cewa Guardiola zai bar Manchester City, shugabannin kulob din sun fara neman wanda zai maye gurbinsa.

Maresca ya zama wanda aka fi so saboda saninsa da tsarin aiki da falsafar ƙungiyar.

Kocin mai shekara 46 a duniya ya taɓa zama mataimakin Guardiola a lokacin da Manchester City ta lashe kofuna uku a kakar wasa ta 2022/23.

Ko da yake Maresca ya bar Chelsea a farkon wannan shekara, har yanzu yana da alaƙar kwantiragi da kulob din na Landan.

Hakan ne ya sa aka shafe lokaci ana tattaunawa tsakanin kulob din biyu.

Sai dai yanzu rahotanni sun nuna an samu nasarar warware matsalar.

A cewar Sky Sports, Manchester City da Chelsea sun amince da yarjejeniyar biyan fam miliyan 17 domin sallamar Maresca daga sauran wa’adin kwantiraginsa.

Ana sa ran wannan yarjejeniya za ta share masa hanya domin komawa filin Etihad a matsayin sabon kocin ƙungiyar.

Naɗin nasa zai bude sabon babi ga Manchester City bayan shekaru masu cike da nasarori a ƙarƙashin Guardiola.

Masana ƙwallon ƙafa na kallon Maresca a matsayin ɗaya daga cikin fitattun matasan masu horaswa a Turai, kuma ana sa ran zai ci gaba da salon wasan da ya kawo wa Manchester City nasarori masu yawa.

Goal.com

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • #201 (no title)
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media