
Daga DAVID MICHAEL, Lafia
Shugabannin Arewa sun yi kira da a gaggauta aiwatar da gyare-gyare domin magance matsalolin rashin tsaro, talauci, koma bayan ilimi, rashin aikin yi ga matasa da kuma ƙalubalen shugabanci da ke addabar yankin.
Haka kuma sun buƙaci kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje da ke aiki ba tare da cikakken tsari ba su mutunta dokokin yaɗa labarai na Najeriya, tare da neman ƙarin haɗin gwiwa domin kare ikon ƙasar kan bayanai da kuma tsaron ƙasa.
An yi wannan kira ne a yayin taron Liberty Symposium karo na biyu da aka gudanar a Abuja.
A cikin wata sanarwa da kakakin taron, Malam Aminu Imam, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa Arewacin Najeriya ba zai iya ci gaba da yin watsi da matsalolin tsarin da ke hana ci gaba da bunƙasarta ba.
Taron mai taken “Re-Imagining the North: Media, Productive Power and the Making of the Next Northern Nigeria” ya samu halartar masu tsara manufofi, shugabannin kafafen yaɗa labarai, sarakuna, masana, ƙwararrun harkokin tsaro, jagororin kasuwanci da ƙungiyoyin farar hula.
Mahalarta taron sun lura cewa duk da dimbin albarkatun noma, ma’adanai da ɗan Adam da yankin Arewa ke da su, har yanzu yankin bai kai matsayin da ya kamata ba kuma bai yi amfani da cikakken ƙarfinsa ba.
Sun bayyana rashin tsaro, raunin hukumomi, ƙarancin ingancin ilimi, ware matasa daga dama da anfani, durƙushewar tattalin arziki da kuma ƙaruwa rarrabuwar kawuna a matsayin manyan barazana ga makomar yankin.
Taron ya yi kira da a samar da abin da ya kira “Sabuwar Fahimtar Arewa” wadda za ta ginu kan gaskiya, aiki tukuru, cancanta, haɗin kai da shugabanci nagari.
Mahalarta taron sun jaddada cewa makomar Arewa dole ta ta’allaka ne kan bunƙasa tattalin arziki, ƙirkire-ƙirkire da shugabanci mai gaskiya maimakon dogaro da tallafi da tunanin cewa komai hakki ne.
Ɗaya daga cikin manyan batutuwan da taron ya mayar da hankali a kai shi ne tsarin Almajiranci, wanda mahalarta suka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan matsalolin zamantakewa da ci gaba a yankin.
Saboda haka taron ya yi kira da a yi cikakken garambawul wanda zai haɗa ilimin zamani, koyon sana’o’i, fasaha da kuma harkokin kasuwanci cikin tsarin.
Masu ruwa da tsaki sun kuma nuna damuwa kan yadda bambance-bambancen ƙabila, addini da siyasa ke ƙara tsananta a yankin.
Sun yi gargaɗin cewa wannan rarrabuwar kawuna na rage ƙarfin Arewa wajen magance matsalolinta na bai ɗaya da kuma gogayya yadda ya kamata a duniyar da ke saurin sauyawa.
Taron ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen samar da ci gaba, ƙara wa masu zuba jari kwarin gwiwa, tabbatar da ɗaukar alhakin gwamnati da kuma ƙarfafa haɗin kan al’umma.
Mahalarta taron sun koka kan abin da suka bayyana a matsayin nuna wariya ga kafafen yaɗa labarai mallakin ’yan Arewa wajen rabon kuɗaɗen tallace-tallacen gwamnati da na ƙasa.
An kammala taron da ƙaddamar da shirin Abuja Media Compact for the Next Northern Nigeria 2026–2036.
Shirin wani tsari ne da kafafen yaɗa labarai suka jagoranta domin samar da sauyi a yankin, bunƙasa tattalin arziki, farfaɗo da zamantakewa da kuma inganta ci gaba mai ɗorewa da kowa zai amfana da shi a Arewacin Najeriya.
