Saturday, November 21, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Labaran Kasashen Waje

Dubban jama’a sun halarci jana’izar Ayatullah Khamenei a Tehran

by The Nigeria Standard
July 7, 2026
in Labaran Kasashen Waje
Reading Time: 3 mins read
0 0
Dubban jama’a sun halarci jana’izar Ayatullah Khamenei a Tehran
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daruruwan dubban mutane ne suka taru a birnin Tehran na kasar Iran ranar Litinin domin halartar jana’izar Ayatullah Ali Khamenei, Jagoran Kolin kasar, wanda ya rasu a farkon yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran.

An shirya gudanar da jana’izar tasa ta tsawon kwanaki shida, inda za a rika kai gawarsa ta wasu muhimman birane na Iran da Iraki kafin a binne shi ranar Juma’a a garinsu na haihuwa, Mashhad.

Za a fara jigilar gawar daga Tehran zuwa birnin Qom, kafin daga bisani a wuce da ita ta biranen Najaf da Karbala da ke Iraki, sannan a kammala da binne shi a Mashhad.

Duk da tsananin zafin rana, dubban masu makoki sanye da bakaken kaya sun cika titunan Tehran domin yi wa marigayin bankwana.

Gwamnati ta yi amfani da motocin fesa ruwa domin rage zafin da mahalarta jana’izar ke fuskanta.

An lullube akwatin gawarsa da tutar kasar Iran, yayin da ake jan ta a hankali cikin manyan titunan birnin, inda masu makoki suka kewaye ta.

An tsara bikin jana’izar ne domin nuna karfi da hadin kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, sai dai yakin da kasar ke ciki ya sauya yanayin taron.

Da dama daga cikin mahalarta sun rika yin taken “Mutuwa ga Amurka”, yayin da wasu ke daga jajayen tutoci a matsayin alamar daukar fansa.

Wasu kuma sun dauki allunan da ke dauke da sakonnin adawa da Amurka da Isra’ila, ciki har da wadanda aka rubuta “A kashe Trump.”

An ce adawa da Amurka ta kara karfi a Iran duk da cewa kasashen biyu na ci gaba da tattaunawar zaman lafiya bayan rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna a watan da ya gabata.

Sai dai ana ganin tattaunawar na cikin mawuyacin hali saboda ci gaba da hare-haren sama a yankin, ciki har da tashin hankalin da ke yankin mashigin Hormuz da kuma rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Lebanon.

Manyan jami’an gwamnatin Iran da kuma baki daga kasashe daban-daban sun halarci jana’izar.

Sai dai sabon Jagoran Kolin Iran, Mojtaba Khamenei, bai bayyana a wajen taron ba. Tun bayan rasuwar mahaifinsa ba a sake ganin sa a bainar jama’a ba.

A al’adar Musulunci, ana binne mamaci cikin sa’o’i 24 bayan rasuwa.

Sai dai gwamnatin Iran ta ajiye gawar Ayatullah Ali Khamenei na tsawon watanni hudu saboda ci gaba da rikici, wanda ya sa ba zai yiwu a gudanar da irin wannan babban taron jana’iza cikin aminci ba.

TIME

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media