
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ajiye hukunci a karar da Kwamitin Amintattu (BoT) na jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Sanata Adolphus Wabara ya shigar, inda yake neman kotu ta tilasta wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da sabon shugabancin riƙon ƙwarya na jam’iyyar.
Mai shari’a Salim Ibrahim ne ya sanar da hakan a ranar Talata bayan lauyoyin ɓangarorin da ke shari’ar sun gabatar da hujjojinsu da takardunsu na goyon baya da na ƙin amincewa da ƙarar.
Ya ce za a sanar da ɓangarorin ranar da za a yanke hukuncin sa’o’i 24 kafin ranar.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa mambobin BoT ƙarƙashin jagorancin Wabara sun shigar da sabuwar ƙarar ne domin neman umarnin kotu da zai tilasta wa INEC ta amince da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na riƙon ƙwarya na PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki, SAN, tare da wallafa sunayensu a shafin yanar gizon hukumar.
Masu ƙarar sun kuma nemi kotun ta umarci INEC ta sabunta bayananta tare da wallafa sunayen mambobin sabon NWC kamar yadda suka miƙa wa hukumar ta hannun Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC).
Sun bayyana cewa an aika sunayen mambobin kwamitin da Kabiru Turaki ke jagoranta ga INEC ta wasiƙu da aka rubuta ranar 4 ga watan Mayu.
An shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1159/2026 a ranar 4 ga watan Yuni ta hannun tawagar lauyoyi ƙarƙashin jagorancin Cif Chris Uche, SAN.
Masu ƙarar sun haɗa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Adolphus Wabara; Sakataren BoT kuma tsohon Gwamnan Jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu; tsohon Ministan Yaɗa Labarai, Farfesa Jerry Gana; da jigo a PDP, Olabode George.
Sauran sun haɗa da tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Hajiya Maryam Ciroma; tsohuwar Ministar Harkokin Mata da Raya Al’umma, Hajiya Zainab Maina; mambar BoT da NEC, Dame Esther Uduehi; da kuma jam’iyyar PDP.
INEC ce kaɗai ke matsayin wadda ake ƙara.
Sai dai wani ɓangaren PDP mai biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya garzaya kotu yana ƙalubalantar ikon kotun na sauraron shari’ar.
A zaman kotun na ranar Talata, Chris Uche ya bayyana cewa shi ne lauya ga masu ƙara na ɗaya zuwa na takwas, yayin da Sunday Ameh, SAN, ya ce shi ne ke wakiltar mai ƙara na takwas wato jam’iyyar PDP.
Hakazalika, shugabannin PDP masu goyon bayan Wike ƙarƙashin jagorancin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Alhaji Abdulrahman Mohammed; Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu; da Mai Ba da Shawara kan Shari’a na Ƙasa, Kamardeen Ajibade, sun nemi kotu ta shigar da su cikin shari’ar a matsayin waɗanda ake ƙara na biyu zuwa na huɗu.
Emmanuel Ukala, SAN, ne ya wakilce su, yayin da Joseph Daudu, SAN, ya wakilci Austin Nwachukwu, tsohon shugaban PDP na Jihar Imo; Abraham Amah; da George Turner, waɗanda suka nemi a shigar da su a matsayin waɗanda ake ƙara na biyar zuwa na bakwai.
Dukkansu sun roƙi kotun ta yi watsi da ƙarar baki ɗaya.
A baya dai Mai shari’a Ibrahim ya sanya ranar Talata domin sauraron dukkan buƙatun da ke gaban kotun, ciki har da ainihin ƙarar.
Ya kuma ba wa masu neman shiga cikin shari’ar damar shigar da takardunsu, ƙorafe-ƙorafen farko da kuma martaninsu kan babbar ƙarar domin a saurare su lokaci guda tare da yanke hukunci a kansu.
An yanke wannan hukunci ne bayan Chris Uche ya shaida wa kotun cewa shari’ar tana da matuƙar muhimmanci saboda sabon jadawalin INEC na zaɓen shekarar 2027, wanda ya sanya ranar 17 ga watan Yuli a matsayin wa’adin ƙarshe na miƙa sunayen ‘yan takara.
Da aka kira shari’ar, Uche ya ce suna shirye domin ci gaba da sauraron ƙarar.
Ya ce a zaman da ya gabata an amince cewa dukkan takardun da ɓangarorin da ma waɗanda ba sa cikin shari’ar suka shigar za a karɓe su tare da sauraron babbar ƙarar saboda gaggawar lamarin da kuma muradun adalci.
Sai dai Sunday Ameh ya ce bai yarda da maganar cewa akwai gaggawa ba.
A cewarsa, masu ƙarar ne suka janyo wa kansu wannan gaggawa domin da sun san muhimmancin lamarin da sun shigar da ƙarar tun da wuri.
Ya kuma ce suna ƙalubalantar kasancewar jam’iyyar PDP a matsayin mai ƙara, saboda jam’iyyar ba ta ba Chris Uche izinin shigar da ƙarar ba.
Saboda haka ne suka shigar da takardar sauya lauya tare da neman a cire sunan PDP daga cikin masu ƙarar.
Ameh ya ce hukuncin kotu ne zai tantance ko PDP za ta ci gaba da kasancewa cikin shari’ar ko a’a.
Lauyan INEC, Olusegun Adeyemi, shi ma ya shaida wa kotu cewa hukumar ta shigar da ƙorafin farko da kuma takardar martani kan ƙarar.
Yayin da yake gabatar da buƙatarsa, Ameh ya roƙi kotun ta amince da sauya lauyan PDP tare da cire sunan jam’iyyar daga cikin masu ƙarar.
Sai dai Chris Uche ya nuna ƙin amincewa da wannan buƙata, yana mai cewa sun shigar da takardar martani mai sakin layi 72, wadda Kabiru Turaki ya rantse a kanta tare da haɗa hujjoji guda biyu.
Ya roƙi kotun ta yi watsi da buƙatar saboda rashin tushe da kuma rashin cancanta.
Game da buƙatar shigar da sababbin waɗanda ake ƙara, Emmanuel Ukala ya ce Alhaji Abdulrahman Mohammed, Sanata Samuel Anyanwu da Kamardeen Ajibade muhimman ɓangarori ne da ya kamata su kasance cikin shari’ar.
Ya ce Anyanwu ya rantse da takardar shaidar da ta ƙunshi hujjoji daga XN1 zuwa XN6, yana mai cewa an zaɓe su a matsayin kwamitin riƙon ƙwarya bisa hukuncin wata kotu da ke Ibadan.
A cewarsa, kotun ta soke babban taron jam’iyyar da aka gudanar tsakanin ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamban 2025 a Ibadan tare da umartar a kafa kwamitin riƙon ƙwarya.
Sai dai Chris Uche ya ƙi amincewa da wannan buƙata, yana mai cewa tsohon Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu ya rantse da takardar martani.
Ya bayyana masu neman shiga cikin shari’ar a matsayin masu tsoma baki ba tare da wani dalili ba.
Ya ce tambayoyin da ke cikin ƙarar sun shafi INEC ne kaɗai, kuma ya jingina da Sashe na 287 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya wajen kare hujjar tasa.
Joseph Daudu shi ma ya gabatar da buƙatar shigar da Austin Nwachukwu, Abraham Amah da George Turner cikin shari’ar, amma Uche ya yi adawa da hakan.
Kotun ta kuma saurari ƙorafin farko da kuma babbar ƙarar, inda dukkan lauyoyin ɓangarorin, ciki har da na INEC, suka gabatar da hujjojinsu.
Lauyan INEC, Olusegun Adeyemi, ya roƙi kotun ta yi watsi da ƙarar saboda rashin ikon sauraron ta.
Ya ce ƙorafin farko da suka shigar ranar 23 ga watan Yuni ya dogara ne kan hujjoji huɗu, tare da takardar bayanin doka da suka nemi kotun ta yi la’akari da ita wajen soke ƙarar.
A nasa martanin, Chris Uche ya ce sun shigar da takardar martani ranar 29 ga watan Yuni, yana mai roƙon kotun ta yi watsi da ƙorafin INEC saboda rashin tushe da cancanta.
Ya kuma ce INEC ba ta da hurumin yin irin wannan martani a wannan nau’in ƙara.
Bayan sauraron dukkan hujjojin lauyoyin, Mai shari’a Salim Ibrahim ya ajiye hukunci, yana mai cewa za a sanar da dukkan ɓangarorin ranar da za a yanke hukuncin nan gaba.