Monday, November 23, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Labaran Kasashen Waje

An ji ƙarar fashe-fashe a kudancin Iran yayin da Amurka ta ƙaddamar da hare-haren sama

by The Nigeria Standard
July 9, 2026
in Labaran Kasashen Waje
Reading Time: 2 mins read
0 0
An ji ƙarar fashe-fashe a kudancin Iran yayin da Amurka ta ƙaddamar da hare-haren sama
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

An ji ƙarar fashe-fashe a wasu sassan kudancin Iran a yammacin ranar Laraba yayin da sojojin Amurka suka fara sabon jerin hare-haren sama kan ƙasar.

Wani jami’in gwamnatin Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa hare-haren da ake kai wa Iran a wannan karo sun fi na ranar Talata yawa.

Hare-haren sun biyo bayan sanarwar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi cewa yarjejeniyar fahimtar juna (Memorandum of Understanding) da Tehran “ta zo ƙarshe.”

Kamfanin dillancin labarai na Mehr mai alaƙa da gwamnatin Iran ya ruwaito cewa an kunna tsarin kariyar sararin samaniyar ƙasar a kudancin Iran bayan da aka ji ƙarar fashe-fashe a biranen Bandar Abbas da Sirik da Konarak da kuma Chabahar.

A wata sanarwa da Rundunar Sojin Amurka ta Tsakiya (CENTCOM) ta wallafa a shafinta na X, ta ce, “Bisa umarnin Babban Kwamandan Rundunar Sojin Amurka, dakarun CENTCOM sun fara ƙarin hare-hare kan Iran domin ƙara raunana ƙarfin da take da shi na barazana ga ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.”

Kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Iran sun ruwaito cewa gutsattsarin abubuwan da suka tashi sakamakon hare-haren Amurka sun faɗa wani asibiti da ke Chabahar.

Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Iran, IRNA, ya ce wasu sassan Chabahar sun fuskanci katsewar wutar lantarki bayan fashe-fashen, yayin da Nour News ya ruwaito cewa dakarun Iran na shirin ƙaddamar da “gagarumin hari” kan sansanonin sojojin Amurka da ke yankin nan ba da jimawa ba.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce hare-haren da Amurka ta kai wa Iran martani ne ga harin da ya ce Iran ta kai kan wasu jiragen ruwa a ranar Talata.

Ya ƙara da cewa, “Idan hakan ya sake faruwa, martanin zai fi wannan muni.”

Nour News ya kuma ruwaito cewa hare-haren da Amurka ta kai a Bushehr ba su yi wata illa ga tashar samar da wutar lantarki ta nukiliyar da ke yankin ba.

Har ila yau, kafar yaɗa labarai ta KAN ta Isra’ila ta ce Amurka ta sanar da jami’an Isra’ila tun kafin ta ƙaddamar da hare-haren kan Iran.

THE JERUSALEM POST

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media