
Dan wasan tsakiya na tawagar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu da kuma kungiyar Mamelodi Sundowns, Jayden Adams, ya rasu yana da shekara 25 a duniya, makonni kadan bayan ya wakilci kasarsa a Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Marigayin ya buga dukkan wasannin rukuni uku da Afirka ta Kudu ta yi a gasar, kafin kasar ta fice a zagayen ‘yan wasa 32 bayan ta sha kashi a hannun kasar Canada, wasan da bai samu damar bugawa ba.
Har yanzu ba a bayyana musabbabin rasuwarsa ba.
Ministan Wasanni, Fasaha da Al’adu na Afirka ta Kudu, Gayton McKenzie, ya bayyana alhininsa cikin wata sanarwa, inda ya ce: “Na samu labarin rasuwar Jayden Adams, dan wasan tsakiya na Mamelodi Sundowns da Bafana Bafana, yana da shekara 25, cikin matukar kaduwa da nauyin zuciya.”
Ya kara da cewa: “Kwallon kafar Afirka ta Kudu ta yi rashin daya daga cikin fitattun matasanta, kuma kasarmu na jimami tare da iyalansa, abokan wasansa da miliyoyin magoya bayan da suka ga yadda ya taso daga matashin da ya fara haskawa a makarantar horas da ‘yan wasa har ya zama cikakken dan wasan Bafana Bafana.”
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, shi ma ya mika sakon ta’aziyyarsa cikin wata sanarwa, inda ya ce: “Abin bakin ciki ne matuka jin cewa dan wasan tsakiyar Afirka ta Kudu, Jayden Adams, ya rasu makonni kadan bayan ya taka rawa a gagarumar fafatawar da kasarsa ta yi a Gasar Kofin Duniya ta FIFA.”
Infantino ya kara da cewa: “Tunanina da ta’aziyyata, tare da na daukacin ma’aikatan FIFA da al’ummar kwallon kafa ta duniya, na tare da iyalansa, abokansa da abokan wasansa. Za a yi matukar kewar tauraron Bafana Bafana da Mamelodi Sundowns. Allah Ya jikansa da rahama.”
Kungiyar Mamelodi Sundowns ta kuma tabbatar da rasuwar dan wasan nata cikin wata sanarwa, inda ta ce: “Shugaban kulob din da iyalan Motsepe, kwamitin gudanarwa, masu horaswa, ‘yan wasa, jami’ai, ma’aikata, magoya bayan Mamelodi Sundowns FC da daukacin Yellow Nation suna mika sakon ta’aziyyarsu ga iyalai da abokan arzikin Jayden yayin da muke jimamin rashinsa.”
Kungiyar ta ci gaba da cewa: “Muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba iyalan Adams, abokansa da duk wadanda suka san shi hakurin jure wannan babban rashi.”
Kungiyar Kare Hakkokin ‘Yan Kwallon Kafar Afirka ta Kudu (SAFPU) ita ma ta fitar da sanarwa tana cewa: “SAFPU ta yi matukar kaduwa da rasuwar Jayden Adams, dan wasan tsakiya na Mamelodi Sundowns da Bafana Bafana.”
Sanarwar ta kara da cewa: “Kwanan nan ne kawai Jayden ya wakilci Afirka ta Kudu a Gasar Kofin Duniya ta 2026, inda ya dauki burin al’ummar kasa cikin alfahari, jarumtaka da kwarewa.”
SAFPU ta kuma ce: “Rasuwarsa babban rashi ne wanda ba za a iya auna girmansa ba ga iyalansa, abokan wasansa, kungiyoyin da ya buga wa, daukacin al’ummar kwallon kafa da kuma kasa baki daya. Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan Adams, Mamelodi Sundowns, Stellenbosch FC, Bafana Bafana da kuma duk wadanda rayuwarsa ta taba.”
Sky Sports
