Sunday, October 25, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Labari

Gwamnan Neja ya maye gurbin hakiman Fulani da sarakuna

by The Nigeria Standard
July 20, 2026
in Labari
Reading Time: 3 mins read
0 0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga SAMUEL MATHIAS, Minna

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Bago, ya maye gurbin hakiman Fulani da sarakuna a wasu sassan jihar, saboda matsalar tsaro da ta yi kamari.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Litinin yayin da ya kai ziyara Fadar Sarkin Borgu domin jajanta wa al’ummomin da hare-haren baya-bayan nan suka shafa.

Ya ce matakin ya biyo bayan karuwar sace-sacen mutane domin neman kudin fansa, hare-haren ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro da suka addabi jihar.

A cewar rahoton Nasarawa News Daily da wakilinmu ya bibbiya, Gwamna Bago ya ce mutanen da ake sacewa, idan aka sake su bayan an biya kudin fansa, galibi suna bayyana cewa Fulani ne suka yi garkuwa da su.

Ya kuma ce idan rikici ya barke tsakanin al’ummomin asalin Jihar Neja da wasu Fulani, ana zargin bangaren Fulani da kiran ‘yan uwansu daga kasashe makwabta domin su shiga rikicin.

Bugu da kari, gwamnan ya ce wasu al’ummomi sun shafe lokaci suna fama da rikice-rikicen da ake dangantawa da kwace filaye da wasu Fulani ke yi a jihar.

A wani bangare kuma, Gwamna Bago ya gargadi shugabannin addinai da su guji yin hudubobi ko wa’azuzzuka masu haddasa kiyayya, rarrabuwar kawuna da tashin hankali.

Ya ce wajibi ne wuraren ibada su kasance cibiyoyin zaman lafiya, kauna, hadin kai da zaman tare cikin fahimtar juna.

Rahotannin Niger State Media News 24 da Crystal Radio 91.3 FM Minna, wadanda wakilin THE NIGERIA STANDARD da ke Minna ya samu, sun ruwaito gwamnan na cewa: “Duk wani limami ko masallacin da aka samu ana wa’azin ta’addanci, kiyayya da tashin hankali maimakon zaman lafiya, a kai rahotonsa. Za a kama limamin, sannan a rufe masallacin.”

Ya kuma ce duk wani limamin Babban Masallaci ko Masallacin Juma’a da aka samu yana wa’azin da ke haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin addinai ko akidu, ya kamata a kai rahotonsa.

A cewarsa: “Za a kama limamin, sannan a rufe masallacin gaba daya.”

Haka kuma, gwamnan ya yi gargadin cewa duk wani limami ko masallacin da ke yada akidar Lakurawa, ko kuma ya bai wa mabiyanta damar yin wa’azi, za a dauki mataki a kansa.

Ya ce: “Za a tsare limamin, sannan a dakatar da dukkan ayyukan masallacin.”

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, kokarin jin ta bakin Babban Sakataren Yada Labarai na Gidan Gwamnatin Jihar Neja bai yi nasara ba.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media