Saturday, October 24, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Labari

Mutfwang ya yabawa Tinubu yayin da REA ta kaddamar da aikin wutar lantarki a Pankshin

by The Nigeria Standard
July 21, 2026
in Labari
Reading Time: 3 mins read
0 0
Mutfwang congratulates newly elected COCIN leaders
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga PETER TITLE, Pankshin

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya kaddamar da aikin gina tashar samar da lantarki mai karfin megawatt 1.5 ta Pankshin Hybrid Interconnected Mini-Grid, wanda Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA) ke aiwatarwa, tare da yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da kuma goyon bayan aikin.

An gudanar da bikin aza harsashin aikin ne a ranar Talata a al’ummar Angrest da ke Karamar Hukumar Pankshin ta Jihar Filato.

Gwamna Mutfwang ya bukaci al’ummar jihar su ci gaba da mara wa gwamnatin da ke mulki baya, yana mai cewa Shugaba Tinubu ya kuduri aniyar samar da ci gaba a sassan Najeriya baki daya, ciki har da Jihar Filato wadda ke ci gaba da cin gajiyar ayyukan gwamnatin tarayya a fannoni daban-daban.

Ya bayyana aikin a matsayin wanda zai sauya rayuwar jama’a, yana mai cewa zai samar wa matasa ayyukan yi, ya bunkasa tattalin arziki, ya samar da wutar lantarki ga al’ummomi da dama tare da taimakawa wajen rage ayyukan ta’addanci da sauran laifuffuka.

Ya ce, “Wannan aiki yana da matukar muhimmanci a gare ni domin zai samar wa dimbin matasanmu ayyukan yi, ya bunkasa tattalin arzikinmu, ya haskaka kauyuka da dama tare da taimakawa wajen rage aikata laifuffuka.”

Gwamnan ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnatin jihar za ta mara wa aikin baya tun daga farko har zuwa kammalawa, sannan ya bukaci matasan yankin su kasance sahun gaba wajen kare ma’aikatan da ke aikin da kuma kayayyakin aikin.

Har ila yau, ya yabawa Shugaba Tinubu bisa amincewa da aikin fadada hanyar Mararaban Jama’a–Barkin Ladi–Mangu–Pankshin–Langtang–Shendam–Ibi, yana mai cewa al’ummomin Berom da Mwaghavul da Ngas da Taroh da Gamai da kuma mutanen Jihar Taraba suna godiya tare da alfahari da shugabancinsa.

Ya kuma sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da kai wa al’umma romon dimokuradiyya, yana mai bayyana cewa an kammala takardar mallakar filin aikin (Certificate of Occupancy), wadda za a mika wa ‘yan kwangilar nan ba da jimawa ba.

Babban Daraktan Hukumar REA, Abba Aliyu, ya bayyana aikin a matsayin wani babban ci gaba da zai inganta samar da lantarki, ya hada al’ummomi tare da kyautata rayuwar jama’a.

Ya ce aikin zai samar da ingantacciyar wutar lantarki mai tsafta da aminci, tare da taimakawa wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaba mai dorewa a yankunan da za su ci moriyarsa.

Aliyu ya yabawa Gwamna Mutfwang kan ci gaba da hadin gwiwarsa da hukumar, yana mai cewa gwamnan ya taimaka wajen samar da karin ayyukan makamashi mai sabuntawa guda 10 a Jihar Filato.

Ya kuma bayyana cewa hukumar na kashe sama da dala miliyan 750 wajen aiwatar da irin wadannan ayyukan lantarki a sassan Najeriya, tare da tabbatar da cewa za a samar da karin na’urorin rarraba lantarki (transformers) domin inganta rabon wutar lantarki.

Aliyu ya bukaci al’ummar jihar su ci gaba da goyon bayan kokarin gwamnatin Mutfwang na kawo ci gaba tare da tabbatar da kare kayayyakin aikin, yana mai cewa mallakin al’umma ne.

Tun da farko, Kwamishinan Albarkatun Ruwa da Makamashi na Jihar Filato, Bashir Datti, ya bayyana aikin mini-grid din a matsayin mafi girma kuma mafi saukin gudanarwa a bangaren makamashi mai sabuntawa a jihar.

Ya yabawa Gwamna Mutfwang bisa jajircewarsa wajen tabbatar da aikin ya zama gaskiya, yana mai cewa gwamnatin na da burin barin jihar cikin kyakkyawan yanayi fiye da yadda ta same ta.

Shugaban Karamar Hukumar Pankshin, Felix Gonung, da Ngolong Ngas da Nde Jika Golit da sauran masu ruwa da tsaki sun gabatar da sakonnin fatan alheri, inda suka yi alkawarin ba da cikakken goyon baya domin tabbatar da nasarar aiwatar da aikin.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media