Saturday, October 24, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Labari

‘Yan Majalisa 311 sun amince da kudirin ‘yan sandan jihohi

by The Nigeria Standard
July 23, 2026
in Labari
Reading Time: 3 mins read
0 0
311 Reps pass state police bill, Minority Caucus walks out5
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Majalisar Wakilai ta amince da kudirin dokar gwamnatin tarayya na kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, bayan ‘yan majalisa 311 sun kada kuri’ar amincewa da gyaran kundin tsarin mulkin da kudirin ya tanada.

Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana a ranar Alhamis cewa ‘yan majalisa 35 sun kada kuri’arsu ta yanar gizo, yayin da mambobi 276 suka halarci zaman a zauren majalisar.

Rahoton Vanguard ya ce an amince da kudirin ne bayan nazari da kuma karbar rahoton Kwamitin Majalisar kan Bita ga Kundin Tsarin Mulkin 1999, karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu, a zaman majalisar.

Kudirin mai taken, “Kudirin Dokar Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 domin tanadar da kafa Rundunar ‘Yan Sandan Jihohi da sauran batutuwan da suka shafe ta (HB.2797),” na neman samar da tubalin doka da zai ba da damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi.

A kwanakin baya ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aikewa Majalisar Wakilai da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin mai suna Constitution of the Federal Republic of Nigeria (Alteration) (State Police) Bill, 2026.

Sai dai tsirarun ‘yan majalisar (Minority Caucus) sun fice daga zauren majalisar domin nuna rashin amincewarsu da yadda aka zartar da kudirin, inda suka zargi shugabancin majalisar da karya tanade-tanaden kundin tsarin mulki da kuma dokokin gudanar da harkokin majalisar.

Da yake ganawa da manema labarai bayan ficewarsu daga zauren majalisar, Shugaban Tsirarun ‘Yan Majalisar, Fredrick Agbedi, tare da sauran shugabannin kungiyar, ya ce matakin da suka dauka ba wai saboda suna adawa da kafa ‘yan sandan jihohi ba ne, illa saboda abin da suka kira take ka’idojin majalisa.

Agbedi ya ce Kakakin Majalisar, yayin da yake jagorantar zaman Kwamitin Daukacin Majalisa, ya yi watsi da tanade-tanaden kundin tsarin mulki da suka shafi gyaran kundin.

Ya ce ana tantance adadin ‘yan majalisar da suka halarci zama ne ta hanyar rajistar da suke sanyawa hannu a kowace ranar zama, ba ta hanyar karanta sunayen mambobi yayin gudanar da zaman ba.

Ya ce, “Kundin tsarin mulki shi ne babbar doka ta kasa, kuma shi ne tushen duk sauran dokoki har da dokokin gudanar da harkokin majalisa. Saboda haka, watsi da tanadin Sashe na 9(2) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima babban saba wa tsarin aikin Majalisar Wakilai ne.”

Kungiyar ta kuma jaddada cewa dole ne a duba kudirin gyaran kundin tsarin mulki sashe bayan sashe, kuma kowanne sashe ya samu goyon bayan akalla kashi biyu cikin uku na mambobin majalisar kamar yadda kundin tsarin mulki da dokokin majalisar suka tanada.

Sun yi nuni da Dokar 13, Ka’ida ta 15(a) ta dokokin Majalisar Wakilai, wadda ta tanadi cewa duk wani sashe na kudiri zai kasance ya samu amincewa ne kawai idan ya samu kuri’ar goyon bayan akalla kashi biyu cikin uku na mambobin majalisar.

Har ila yau, sun soki matakin karanta dogon taken kudirin kawai tare da amincewa da shi ta hanyar kuri’ar murya ba tare da yin cikakken nazari kan kowane sashe ba.

A cikin wasikar da ya aike tare da kudirin, Shugaba Tinubu ya ce kudirin ya ginu ne kan kokarin da majalisar ta taba yi a baya, tare da tanade-tanaden kariya da za su tabbatar da samar da tsarin ‘yan sanda biyu domin magance kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta.

Shugaban ya ce kudirin wani muhimmin bangare ne na shirin gwamnatinsa na sake fasalin tsarin tsaron kasar da kuma inganta kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa Majalisar Wakilai za ta yi wa kudirin nazari cikin gaggawa.

Bayan karbar kudirin daga bangaren zartarwa, Majalisar Wakilai ta soke matsayarta ta ranar 11 ga Yunin 2026 kan kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, tare da rushe Kwamitin Sulhu mai mambobi 12 da ta kafa a ranar 9 ga Yulin 2026.

Yanzu kudirin zai ci gaba da sauran matakan gyaran kundin tsarin mulki kafin ya zama doka.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media