Friday, November 20, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Rayuwa

Bayan kallo: Boyayyun hatsarin tumbi

by The Nigeria Standard
July 27, 2026
in Rayuwa
Reading Time: 7 mins read
0 0
Bayan kallo: Boyayyun hatsarin tumbi
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Abin da a da ake ɗauka a matsayin alamar wadata da jin daɗin rayuwa, a yau yana ƙara bayyana a matsayin babbar barazana ga lafiya. A wannan maƙala, YVONNE ISHOLA ta yi nazari kan yadda tumbi ke ƙaruwa a tsakanin ‘yan Najeriya, inda ta yi amfani da bayanan masana harkar lafiya da kuma abubuwan da mutane suka fuskanta domin nuna yadda salon rayuwa, rashin cin abinci mai kyau, tsufa da kuma rashin motsa jiki ke haddasa matsalar. Har ila yau, ta yi kira ga ‘yan Najeriya su fifita kula da lafiyarsu maimakon riƙe tsohuwar fahimtar cewa tumbi alamar arziki ce

Yawaitar masu tumbi a cikin al’ummar Najeriya na ci gaba da zama abin damuwa. A mafi yawan lokuta, tumbi shi ne abu na farko da ido ke hangowa idan aka kalli mutum. Baya ga sauya kamanni, yana kuma shafar yadda mutum ke tafiya da yadda yake ɗaukar jikinsa.

Tunanin da aka daɗe ana yi cewa tumbi alama ce ta arziki da walwala na ƙara gushewa, yayin da jama’a ke ƙara fahimtar irin matsalolin lafiya masu tsanani da ke tattare da kiba a yankin ciki.

Kiba a yankin ciki, wadda aka fi sani da pot belly, yanzu ta zama babbar matsalar lafiyar al’umma a Najeriya. Binciken ƙasa ya nuna cewa fiye da manyan ‘yan Najeriya miliyan 12 na fama da kiba.

Duk da cewa kiba gaba ɗaya ta fi yawa a tsakanin mata, kiba da ke taruwa a yankin ciki ta fi yawa musamman a tsakanin mazan da suka manyanta, kuma yanzu ana kallonta a matsayin babbar barazana ga lafiya, ba alamar arziki ba.

Sauyin salon rayuwa, sauyin jiki

“‘Tumbi’ mai girma yana kama da wanda yake jan mai shi. Ba tare da ya sani ba, mutum zai fara tafiya yana tura cikinsa gaba kamar shi ne mafi muhimmanci, tamkar mace mai juna biyu. A mafi yawan lokuta ma, girman tumbin yana sa hannuwansa su riƙa buɗewa gefe maimakon su riƙa motsi yadda ya kamata yayin tafiya,” in ji Malam Suleiman Ade.

Ade, wanda ya shafe shekara 20 da aure, ya ce cikin raha ya taɓa gaya wa matarsa cewa, “Ranar da kika fara yin tumbi, ranar ce soyayya za ta mutu a aurenmu.”

A yau, tumbi ya zama ruwan dare a faɗin Najeriya, tsakanin matasa da manya, masu kuɗi da marasa kuɗi.

A da kuwa, ba kasafai ake ganin matasa maza ko ‘yan mata da tumbi ba. Idan mace mara aure tana da irin wannan ciki, ana danganta shi da juna biyu ko wata matsalar lafiya. A wancan lokaci, ana iya bambance budurwa da matar aure ta hanyar kamanninta.

Misis Ene Oche, wata ‘yar jihar Benuwai da ke zaune a Jos, ta tuna da waɗannan kwanaki cikin kewa.

“Mun kasance muna sanya kayan da suka matse jiki domin nuna siririn kugu,” in ji ta. “A lokacin, kusan abin kunya ne budurwa ta yi tumbi saboda hakan kan rage mata masu neman aurenta.”

Ta ce a yanzu kuwa, ‘yan mata da dama kan shiga cibiyoyin motsa jiki kafin aurensu domin rage tumbi su fito cikin kyakkyawan kamanni a ranar biki.

Masana lafiya sun ce ba abu guda ne ke haddasa tumbi ba.

Dokta Samson Lohor, Babban Likita mai koyon ƙwarewa a fannin Mata da Haihuwa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), ya bayyana cewa yawan kitse a yankin ciki na mata yawanci yana faruwa ne sakamakon sauyin sinadaran jiki, wasu matsalolin lafiya da kuma salon rayuwa.

Ya ce daga cikin abubuwan da ke haddasa hakan akwai cututtuka irin su Polycystic Ovarian Syndrome (PCOS), Cushing’s syndrome, lokacin daina al’ada, matsalar insulin, prediabetes, hypothyroidism, fibroids da kuma ovarian cysts.

Haka kuma, ya ce bayan haihuwa wasu mata kan fuskanci rabuwar tsokokin ciki, abin da ake kira diastasis recti, wanda ke sa ciki ya ci gaba da fitowa ko bayan haihuwa.

Salon rayuwa irin su yawan cin abinci mai sukari da farin fulawa, shan barasa, yawan damuwa, rashin isasshen barci, tsufa da kuma rashin motsa jiki na taka muhimmiyar rawa wajen haddasa kiba a yankin ciki.

Wata ma’aikaciyar jinya, Talatu Ralph, ta ce bunƙasar birane da sauyin yanayin aiki sun rage motsa jikin mutane sosai.

“Arziki da manyan muƙamai suna sa ana yi wa mutum komai. Maimakon motsa jiki, kitse yana taruwa, wanda hakan na iya jefa rayuwa cikin haɗari,” in ji ta.

Illolin da Ke tattare da tumbi

Ga iyalai da dama, matsalar tumbi ba ta tsaya kan kamanni kawai ba.

Wani jami’in soja da ya nemi a sakaya sunansa ya ba da labarin yadda aurensa ya kusa rushewa bayan da aka tura shi aiki Maiduguri, yayin da matarsa ta ci gaba da zama a Legas saboda matsalolin tsaro.

“Da na dawo gida lokacin Kirsimeti, na tarar da matata ta ninka yadda take, har tumbi nata yana kwanciya a kan cinyoyinta,” in ji shi cikin jimami.

Ya ce daga baya ne likitoci suka gano cewa rashin motsa jiki da kuma barin kusan dukkan ayyukan gida ga mai aikin gida ne suka haddasa matsalar. Sai bayan shekaru na rage cin abinci da sauya salon rayuwa ne ta koma yadda take a da.

Misis Mantoe ma ta ba da irin wannan labari. Saboda tsawon shekarun rashin motsa jiki, yanzu ba ta iya tafiya ko ɗan tazara ko tsayuwa na fiye da minti biyu ba tare da jin zafi ba. A yau tana kashe kuɗaɗe masu yawa wajen neman magani domin ta ci gaba da tafiya.

Masana sun kuma nuna cewa shan barasa na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa tumbi.

Malam Ibrahim Adetunde, wanda ke wasan golf, ya ce bai fara yin tumbi ba sai bayan ya kai shekara 50, lokacin da rayuwarsa ta koma golf da kuma shan giya kowace maraice.

“A cikin shekaru biyar da suka wuce, kusan kowace rana ina zuwa filin golf ina shan giya tare da cin nama iri-iri har dare,” in ji shi.

Tsohuwar ma’aikaciyar jinya, Misis Martha Zi, ta bayyana cewa hanta kan fara sarrafa barasa kafin komai, wanda ke sa kuzarin da ke cikin abinci da abin sha ya rikide zuwa kitse.

Ta ƙara da cewa yayin da mutum ke tsufa, yadda jiki ke ƙona kuzari yana raguwa, lamarin da ke sa tumbi ya fi saurin fitowa idan ba a rage cin abinci ba.

Ta kuma ce sauyin salon rayuwa ya ƙara ta’azzara matsalar. Yawan cin abincin da aka sarrafa, abubuwan sha masu sukari da kuma cin abinci mai nauyi musamman da daddare na ƙara haddasa tumbi.

Amina Bala ta ɗora laifin kan rashin kyawawan halayen cin abinci da matasa ke yi.

“Matasa da yawa suna da tumbi saboda ba ma cin abinci yadda ya kamata,” in ji ta. “Muna fifita ice cream a kan moi-moi, kayan zaki maimakon cikakken abinci, sannan muna rayuwa da noodles, abubuwan sha masu sukari da abincin da aka sarrafa irin su sardine, baked beans, Geisha, Pringles da popcorn. Waɗannan abinci sun fi cutar da jiki fiye da amfani.”

Ta ƙara da cewa har yanzu iyalai da dama a Najeriya na cin tuwo ko swallow da miya da daddare duk da haɗarin da hakan ke tattare da shi.

Matsalar da za a iya kauce mata

A al’adance, tumbi alama ce ta arziki da jin daɗin rayuwa a al’ummomi da dama a Najeriya. Hoton mai kuɗi a zukatan mutane shi ne mutum mai babban ciki, kuma wannan fahimta ta sa mutane da yawa ba sa damuwa da ƙarin kiba har sai ta jawo matsalar lafiya.

Misis Chinyere Obi ta ce a wasu al’ummomin Igbo, ana kallon ɗan tumbi ga matar aure a matsayin alamar cewa ana kula da ita yadda ya kamata.

Sai dai ta ce a yanzu abubuwa sun fara sauyawa, domin mata da dama na ƙoƙarin rage tumbi domin kula da lafiyarsu da kuma kamanninsu.

Masana lafiya sun yi gargaɗin cewa yawan kitse a yankin ciki na ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya, hawan jini da ciwon sukari na nau’i na biyu, saboda kitsen da ke cikin ciki na kawo matsala ga yadda insulin ke aiki tare da ƙara wa zuciya nauyi.

Sun kuma shawarci duk wanda ke fama da tumbi tare da matsaloli irin su rikicewar al’ada, tsananin gajiya, hawan jini ko ƙarin kiba cikin sauri da ya garzaya asibiti domin a bincika yiwuwar cututtuka irin su PCOS, ciwon sukari ko matsalolin thyroid.

A wannan lokaci da ake yawan samun mutuwar gaggawa, masana sun ce ya zama wajibi kowane ɗan Najeriya ya riƙa duba lafiyarsa tare da kula da nauyin jikinsa.

Ko da yake a da ana kallon tumbi a matsayin alamar nasara da arziki, hujjoji sun nuna cewa a mafi yawan lokuta yana nuni ne da rashin kyakkyawan salon rayuwa da kuma yiwuwar matsalolin lafiya.

Sai dai akwai labari mai daɗi. Ana iya kauce wa kiba a yankin ciki, kuma a lokuta da dama ana iya rage ta ta hanyar cin abinci mai kyau, motsa jiki akai-akai da kuma neman kulawar likita cikin lokaci.

Kamar yadda ake cewa, lafiya ita ce babban arziki.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media