
Daga JENNIFER YARIMA
Shin akwai wani laifi da ya kamata ya kai ga azabtarwa da wulakancin da Ibrahim Pilasar Mbaya, wanda aka fi sani da Ibee, ya sha a hannun mutanen da yake kira abokai?
Matashin mai shekaru 25, wanda ya kammala karatu a Jami’ar Jos, kuma ya kasance ɗan kwalliya, mai girki da kuma ɗaya daga cikin matasan Najeriya masu cike da buri, an cire masa mutuncinsa, an azabtar da shi na tsawon sa’o’i, sannan aka tura shi zuwa kabari tun yana matashi, bisa zargin cewa ya kwana a gidan wani abokinsa bayan an rasa wayar iPhone 12 Pro.
A cewar Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, lamarin ya faru ne ranar Lahadi a wani gida da ke bayan yankin City of David a kan Ring Road, Jos. Mbaya ya halarci wani taron walima, sannan ya kwana a gidan wani abokinsa saboda dare ya yi masa don komawa gida.
Da safe, abokin nasa ya ce an rasa wata wayar iPhone, kuma ya zargi Mbaya a matsayin wanda ya fi kowa zargi, kasancewar su biyu ne kawai suka kwana a gidan. Ko da yake Mbaya ya riga ya bar gidan, sai aka kira shi ya dawo domin ya yi bayani. Da ya dawo, an ce ya tarar da abokin nasa tare da wasu matasa. Shaidun da aka tattara da rahoton ’yan sanda sun bayyana wani mummunan yanayi.
An lakada masa duka da bulala, hannu da katako, sannan aka kai shi kan wani tudu. An rataye shi, aka tilasta masa tsugunnawa na tsawon sa’o’i, sannan aka umurce shi da ya riƙa ɗebo ruwa daga wani bokiti zuwa wani da cokali a matsayin hukunci.
An ci gaba da dukan na tsawon sa’o’i domin tilasta masa amsa laifi har sai da ya suma. Daga baya aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), inda likitoci suka tabbatar da cewa ya rasu kafin a kawo shi.
Hotunan ban tsoro da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun jawo tashin hankali da damuwa. Amma abin da ya fi ciwo shi ne cewa yayin da ake yi masa wannan ta’asa, wasu sun zaɓi ɗaukar bidiyo da wayoyinsu maimakon su cece shi ko kuma su sanar da ’yan sanda.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta kama mutane huɗu: Rinji Daniel Fwanji, Emmanuel Newyear, Nensemka Fwanji da Joshua Tell. ’Yan sanda sun ce mutum shida ne suka shiga cikin lamarin kai tsaye, kuma ana ci gaba da neman wasu biyu da suka tsere. Ana zargin waɗanda aka kama sun amsa cewa maimakon su miƙa Mbaya ga jami’an tsaro, sai suka ɗauki doka a hannunsu.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, SP Alfred Alabo, ya yi Allah wadai da lamarin, yana mai jaddada cewa, “Babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon doka na duka ko kashe wanda ake zargi da aikata laifi”, sannan ya ƙara da cewa “duk wanda ake zargi yana da haƙƙin bin tsarin doka kafin a yanke masa hukunci.”
Sai dai kuma akwai zarge-zargen cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargin suna da alaƙa da manyan mutane a ƙasar nan. Wannan ya haifar da fargabar cewa binciken na iya fuskantar katsalandan. Saboda haka, wajibi ne ’yan sanda su yi watsi da duk wani yunƙurin tsoma baki. Dole ne a tabbatar da adalci, ko da kuwa waye abin ya shafa.
Kamar yadda ake tsammani, wannan kisan ya jawo fushin jama’a a faɗin ƙasa. Ƙungiyar Tsofaffin Daliban Jami’ar Jos, Ƙungiyar Daliban Najeriya (NANS) da ƙungiyoyin farar hula sun bukaci a gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wanda ke da hannu a cikin lamarin.
Ibee ba ɗan kwalliya kawai ba ne. Kwana biyu kafin mutuwarsa, masu shirya gasar Mr & Miss Glam Nigeria sun wallafa wani bidiyonsa yana kammala wani aikin tafiya a dandali. Saƙonsa na ƙarshe a Instagram ranar 24 ga Yuli ya ɗauki rubutun: “Ɗan hasken rana kaɗan, ɗan shiru kaɗan, da kuma salama mai yawa.” Ranar haihuwarsa ita ce 18 ga Satumba. An ce ya zo Jos ne domin warware wata matsalar karatu da ta rage masa a Jami’ar Jos.
An ɗauko gawarsa daga ɗakin ajiyar gawa na Jos ranar Alhamis, 30 ga Yuli, 2026, domin yi masa jana’iza, yayin da iyalansa, abokansa da abokan aikinsa ke jimamin rayuwar da aka katse tun tana da sauran zango.
Iyaye daga bangarorin biyu yanzu suna cikin raɗaɗi. Yayin da iyalan Mbaya ke neman adalci, iyalan waɗanda ke tsare suna fuskantar baƙin cikin shari’ar kisan kai da kuma kunyar da ta biyo bayanta.
A zahiri, wannan lamari ya fi batun bacewar wata iPhone nesa. Jita-jita sun yaɗu a Jos cewa wataƙila hassada da kishi ne suka haddasa wannan mummunan kisan. Ana zargin cewa waɗanda ake zargin sun aika bidiyon azabtar da shi zuwa wata hukumar kula da harkokin kwalliya domin bata masa suna ta hanyar zarginsa da sata.
Haka kuma, daga wasu bayanai da ba a tabbatar da su ba, ana cewa akwai wani shiri na dasa bindiga a ɗakinsa domin a ƙara ɗaura masa wani laifi idan zargin satar bai yi tasiri ba.
Waɗannan zarge-zarge ba a tabbatar da su ba, don haka ya kamata a yi taka-tsantsan wajen karɓarsu. Sai dai suna nuna irin yanayin da ya dabaibaye wannan lamari.
Daga ƙarshe dai, wannan bala’i yana nuna al’umma ce da ta rasa tausayin juna. Idan zargi ya zama hukuncin kisa, idan hassada ta maye gurbin ’yan’uwantaka, idan muka zaɓi ɗaukar bidiyo maimakon ceton rai, to lallai mun rasa ma’anar abota ta gaskiya.
Littafi Mai Tsarki ya gargade mu cewa “zuciyar mutum muguwar gaske ce”, sannan ya umurce mu da “ku kiyaye zukatanku, domin daga cikinsu ne al’amuran rayuwa suke fitowa.” A yau, wasu ƙungiyoyin matasa suna kama da wurare masu haɗari, inda ake ɗaukar zalunci da tashin hankali a matsayin ƙarfi ko fifiko.
Babu wani zargi da ya kamata ya zama hukuncin kisa. A cikin al’umma mai bin doka, wajibi ne tsarin shari’a ya yi aiki. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta ce bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu. ’Yan Najeriya na sa ido. Jama’a na sa ran ganin cikakken bincike na gaskiya da kuma tabbatar da adalci ba tare da sassauci ba.
Ana cewa abotar Ibee da Rinji ta fara ne lokacin wata gasa a bara. Tunanin cewa irin wannan alaƙa za ta ƙare da wannan mummunan bala’i abin takaici ne ƙwarai. Sun kira shi ɓarawo. Amma gaskiya ta bayyana ne bayan lokaci ya kure.
Idan muka ci gaba da fifita hukuncin jeji a kan bin doka, to babu wanda zai tsira; ba saboda waya ba, ba saboda jita-jita ba, kuma ba saboda zato kawai ba.
Allah Ya jikansa da rahama Ibrahim Ibee Mbaya. Amin.
