
Daga DAVID MICHAEL, Lafia
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya tura sunayen mutum takwas domin nada su a matsayin kwamishinoni, bayan sauyin da ya yi a majalisar zartarwar jihar wanda ya sa kwamishinoni shida suka bar mukamansu.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Danladi Jatau, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin zaman majalisar da aka gudanar a Lafia, inda ya karanta wasiƙar gwamnan da aka aika wa majalisar.
Mutanen da aka tura sunayensu sun haɗa da Muhammad Nagogo (ƙaramar hukumar Wamba), Ahmed Mohammed (Lafia), Mohammed Shehu (Keffi), Mohammed Oyigye (Obi), Adamu Kpadji (Wamba), Nawani Aboki (Doma), Jibril Ibrahim (Nasarawa) da Ashefo Paul (Lafia).
Nadin ya biyo bayan ƙaramin sauyin da Gwamna Sule ya yi a majalisar zartarwar jihar a ranar 22 ga watan Yuli, inda aka sauke kwamishinoni shida daga mukamansu.
Gwamnan ya ce an yi sauyin ne domin sake tsara gwamnati ta yadda za ta iya cika sauran alkawuran da ta ɗauka kafin wa’adin mulkinta ya ƙare.
Da yake sanar da sauyin bayan taron Majalisar Zartarwar Jihar, Sakataren Gwamnatin Jihar, Labaran Magaji, ya ce an umarci kwamishinonin da abin ya shafa da su ajiye mukamansu a matsayin wani ɓangare na gyaran tsarin gwamnati.
Ma’aikatun da sauyin ya shafa sun haɗa da Ma’aikatar Ayyuka, Harkokin Mata, Yaɗa Labarai, Filaye, Kimiyya da Fasaha, da Tsaro da Sauran Harkokin Musamman.
