
Kasashen Turkiyya da Saudiyya da kuma Pakistan sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro a birnin Makka, kamar yadda suka bayyana a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Juma’a a birnin Makka mai tsarki yayin wata ganawa da ta hada Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif.
Yarjejeniyar, wadda aka yi wa lakabi da “Yarjejeniyar Hadin Gwiwar Tsaro ta Makka”, ta hada kasashen uku ne a daidai lokacin da ake fama da yakin Gabas ta Tsakiya da kuma sabon rikicin da ya sake barkewa a Yemen, makwabciyar Saudiyya ta kudanci.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta ce, “An tsara yarjejeniyar ne domin karfafa hadin gwiwar dakile duk wani hari daga wata kasa, kuma ta tanadi cewa duk wani hari da aka kai wa daya daga cikin kasashen uku za a dauke shi a matsayin hari da aka kai wa dukkansu.”
Wani jami’in gwamnatin Turkiyya ya bayyana cewa yarjejeniyar ta shafi harkokin tsaro kawai, kuma ta kunshi alkawarin ba wa juna goyon baya ne idan aka fuskanci barazanar tsaro.
Jami’in ya kara da cewa, duk da cewa mutane da dama na kallon yarjejeniyar a matsayin wata kawance da aka kulla domin tinkarar Iran, ba a yi ta ne domin wata kasa ko wani bangare na musamman ba, kuma a bude take ga sauran kasashen yankin.
Ya kuma ce yarjejeniyar ba ta soke ko maye gurbin duk wata yarjejeniyar bangarorin biyu ko ta bangarori da dama da kasashen ukun suka riga suka kulla da juna ko kuma da wasu kasashe da kungiyoyi.
Times of Israel
