
Daga AFOSEH HAMZA
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kammala aikin Rajistar Masu Zabe na Dindindin (CVR), inda Jihar Filato ta samu sabbin masu zabe 175,494 a fadin kananan hukumominta 17.
An fara aikin rajistar ne a ranar 18 ga Agusta, 2025, kuma tun farko an tsara a kammala shi a ranar 10 ga Yulin 2026, amma daga bisani aka tsawaita wa’adin zuwa ranar 26 ga Yuli domin bai wa karin ’yan Najeriya masu cancanta damar yin rajista.
Kammala aikin ya janyo ra’ayoyi mabambanta daga jam’iyyun siyasa, kungiyoyin fararen hula da masu ruwa da tsaki a harkar zabe, inda aka bayyana damuwa kan matsalolin fasaha, rashin tsaro da kuma wahalar isa cibiyoyin rajista gabanin babban zaben shekarar 2027.
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta soki dakatar da rajistar tare da yin kira da a ci gaba da yin rajistar masu zabe ba tare da sanya wa’adi ba, yayin da Social Democratic Party (SDP) ta goyi bayan dakatarwar na wani dan lokaci domin bai wa INEC damar shirye-shiryen zaben 2027, amma ta dage cewa ya kamata rajistar ta kasance a bude.
Alkaluman karshe na INEC sun nuna cewa Karamar Hukumar Mangu ce ta fi kowace karamar hukuma yawan sabbin rajista da mutum 17,568, sai Jos North mai mutum 15,065, sannan Jos South mai mutum 12,594, yayin da Riyom ta samu mafi karancin rajista da mutum 4,988.
Sauran alkaluman sun hada da Barkin Ladi 7,509, Bassa 9,524, Bokkos 7,675, Jos East 9,832, Kanam 11,602, Kanke 8,666, Langtang North 8,466, Langtang South 9,907, Mikang 9,083, Pankshin 11,807, Qua’an Pan 10,344, Shendam 8,954 da Wase 6,745.
Sabbin alkaluman sun nuna karin rajista idan aka kwatanta da mutum 119,144 da aka samu a matakin farko na aikin.
A fadin Najeriya kuwa, INEC ta yi rajistar sabbin masu zabe 2,970,257 a matakin karshe na aikin, lamarin da ya kawo jimillar sabbin masu zaben da aka yi wa rajista zuwa kusan miliyan 9.2.
