
Daga HASSAN SHALLPELLA, Yola
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya gargadi ’yan siyasa da su daina amfani da addini wajen raba kan al’umma domin neman wata fa’ida ta siyasa gabanin babban zaben shekarar 2027.
Fintiri ya yi wannan gargadin ne a ranar Talata lokacin da shugabannin Majalisar Addinai ta Najeriya (NIREC) reshen Jihar Adamawa suka kai masa ziyara a Gidan Gwamnati da ke Yola.
Ya ce galibin ’yan siyasar da ba za su iya cin zabe bisa nagarta da abin da suka aikata ba, sukan koma amfani da bambance-bambancen addini domin samun kuri’u.
Gwamnan ya bayyana cewa al’ummar Adamawa sun daina kallon shugabanni ta fuskar addini ko kabila ko kuma inda suka fito, sai dai suna daraja shugabannin da ke gudanar da mulki cikin tsoron Allah, tausayi da kuma kula da jin dadin jama’a.
Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta bari wani abu ya kawo cikas ga zaman lafiya da hadin kai da ake da shi tsakanin al’ummomin jihar ba.
Fintiri ya ce ana raba ayyukan gwamnati a sassa daban-daban na jihar ba tare da nuna bambanci na addini ko kabila ba, kuma an tsara su ne domin amfanar daukacin al’umma.
Ya kara da cewa ci gaban da ake samu a jihar ba zai dore ba sai cikin yanayin zaman lafiya, hadin kai da fahimtar juna.
Gwamnan ya bukaci mazauna jihar da kada su bari ’yan siyasa su lalata kyakkyawar alakar da ke tsakanin Musulmi da Kirista saboda bukatun siyasa, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da gudanar da mulki ba tare da nuna son kai na addini ko kabila ba.
A nasa bangaren, shugaban NIREC daga bangaren Musulmi, Alhaji Gambo Jika, da shugaban daga bangaren Kirista, Rev. Joel Manzo, sun yi Allah-wadai da kokarin amfani da addini wajen cimma muradun siyasa.
Sun bayyana sakonnin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke kokarin raba kan jama’a ta fuskar addini a matsayin masu hadari, tare da yin kira ga al’umma su yi watsi da su.
Shugabannin NIREC sun ce ba Musulmi kadai ba, ba kuma Kirista kadai ba ne za su iya bunkasa Adamawa, don haka suka bukaci jama’a su ci gaba da aiki tare duk da bambancin addini.
Sun yaba da irin zaman lafiyar da ake da shi a jihar, suna masu cewa babu ci gaban da zai tabbata a inda ake kin juna da tashin hankali na addini.
Sun kuma sanar da aniyarsu ta kara karfafa ayyukan majalisar a matakin kananan hukumomi domin yada sakon zaman lafiya, hakuri da zaman jituwa tsakanin mabambantan addinai a fadin jihar.
