
Daga HASSAN SHALLPELLA, Yola
An nada Gangwari Ganye, Alhaji Umaru Sanda, wanda shi ne babban sarkin masarautar Ganye a Jihar Adamawa, a matsayin Kansilan Jami’ar Jihar Taraba.
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya taya sarkin murnar wannan mukami tare da yabawa Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, bisa nada wani sarkin gargajiya daga Adamawa a wannan matsayi.
Fintiri ya bayyana nadin a matsayin wanda ya dace, yana mai cewa sarkin yana da kwarewa, hikima da nagartar shugabanci da ake bukata domin samun nasara a sabon mukaminsa.
Ya kuma jaddada muhimmancin cibiyoyin gargajiya wajen inganta zaman lafiya, hadin kai da zaman tare cikin lumana.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da Gangwari Ganye ya kai masa ziyarar girmamawa a Gidan Gwamnati da ke Yola.
A cewarsa, nadin ya nuna irin amincewar da ake da ita ga sarakunan gargajiya wajen bayar da gudummawa ga ci gaban kasa fiye da yankunan da suke mulki.
Fintiri ya ce wannan mukami wata alama ce ta hadin kan Najeriya duk da bambancin da ke tsakanin al’ummominta, yana mai cewa jihohin Adamawa da Taraba suna da kyakkyawar alakar tarihi da al’adu.
Tun da farko, Gangwari Ganye ya ce ziyarar da ya kai wa gwamnan ta kasance ne domin sanar da shi a hukumance game da nadin da aka yi masa kafin ya fara aiki.
Sarkin ya yi alkawarin amfani da kwarewarsa da hikimarsa wajen taimakawa ci gaban Jami’ar Jihar Taraba, tare da gode wa gwamnan bisa goyon baya da amincewar da ya nuna masa.
