
Daga ABBAS GUNGURA, Bauchi
Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Adamu, ya nada tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, sarautar Jigon Bauchi.
An gudanar da bikin nadin sarautar a Fadar Sarkin Bauchi a ranar Talata, inda Gwamna Bala Mohammed da sauran manyan jami’an gwamnati suka halarta.
Gwamna Bala Mohammed ya yabawa Sarkin Bauchi bisa wannan girmamawa da ya yi wa tsohon shugaban kasar, yana mai cewa sarautar wata karramawa ce ga gudummawar da Jonathan ya bayar wajen bunkasa dimokuradiyya, zaman lafiya da hadin kan kasa.
A nasa jawabin, Jonathan ya gode wa Sarkin Bauchi da al’ummar jihar bisa wannan karramawa, tare da yin alkawarin mutunta al’adu da dabi’un da ke tattare da wannan sarauta.
Bikin ya samu halartar masu sarautun gargajiya, manyan baki da jami’an gwamnati.
