Saturday, October 24, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Labari

Atiku ya garzaya kotu domin neman hana Tinubu takarar 2027

by The Nigeria Standard
August 14, 2026
in Labari
Reading Time: 6 mins read
0 0
2027: Atiku asks court to disqualify Tinubu over names, certificate controversy
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya bayyana da kansa a ranar Juma’a a ofishin rajistar Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ya rantse tare da gabatar da takardar shaidar goyon bayan karar da ya shigar yana kalubalantar cancantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Jaridar VANGUARD ta rawaito cewa wata sanarwa da Mataimaki na Musamman kan Harkokin Hulda da Jama’a na Atiku, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku da jam’iyyar ADC sun shigar da karar ne a kan Tinubu, jam’iyyar APC da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), suna dogaro da wasu tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da kuma Dokar Zabe ta 2026.

Sanarwar ta ce ginshikin karar shi ne Sashe na 137(1)(j) na kundin tsarin mulkin, wanda ya tanadi cewa duk wanda ya gabatar da takardar shaidar bogi ga INEC ba zai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa ba.

A cewar masu karar, suna neman kotu ta yanke hukunci kan ko ya kamata a hana Tinubu da jam’iyyar APC shiga zaben shugaban kasa na 2027 bisa zargin cewa Tinubu ya gabatar wa INEC takardar shaidar NYSC ta bogi dangane da zabukan 2023 da 2027.

Da yake magana bayan ya rantse a gaban kotu, Atiku ya ce ya je da kansa ne saboda muhimmancin batun da ke gaban kotu.

Ya ce, “Na zo da kaina saboda batutuwan da ke gaban kotu sun shafi kundin tsarin mulkinmu da kuma mutuncin ofishin shugaban kasa. Ba zan iya bukatar ‘yan Najeriya su mutunta kundin tsarin mulki ba, sannan ni kuma in dauki irin wannan batu da wasa. Na sanya sunana, sa hannuna da rantsuwata a kan hujjojin da muka gabatar wa kotu, kuma yanzu lokaci ya yi da Shugaba Tinubu zai amsa su.”

A cikin takardar rantsuwar da ya gabatar, Atiku ya yi zargin cewa Tinubu ya mika wa INEC takardar shaidar kammala yi wa kasa hidima (NYSC) mai dauke da sunan “Tinubu Bola Adekunle”, wanda masu karar suka ce ya bambanta da sunan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Takardar ta kuma yi zargin cewa an sake amfani da wannan takarda wajen shirye-shiryen zaben shugaban kasa na 2027, kuma ba ita ce takardar da Tinubu ya samu ba.

Sanarwar ta ce Atiku ya kuma sanar da INEC cewa ya na son ta gabatar da takardar Form CF001 da Tinubu ya mika mata dangane da zabukan shugaban kasa na 2023 da 2027.

A cewarsa, ya nemi kwafin takardun da aka tabbatar da sahihancinsu kafin ya shigar da karar, amma bai samu amsa ba a lokacin da ake shirya takardun shari’ar.

Ya ce, “Wannan ne ya sa muka garzaya kotu. Ba mu neman ‘yan Najeriya su yanke hukunci a kafafen sada zumunta ba, kuma ba mu neman INEC ta zama kotu. Muna neman cibiyar da ke rike da takardun ta gabatar da su, sannan bangaren shari’a ya binciki hujjojin ya kuma yanke hukunci.”

Ya kara da cewa, “Idan takardar shaidar ta Bola Ahmed Tinubu ce, a tabbatar da hakan a gaban kotu. Idan ‘Tinubu Bola Adekunle’ da ‘Bola Ahmed Tinubu’ mutum guda ne dangane da wannan takarda, to hujjoji su tabbatar da hakan. Wadannan tambayoyi ne da suka cancanci amsoshi, ba zage-zagen siyasa ko shirun shugaban kasa ba.”

A cewar VANGUARD, baya ga batun takardar shaidar NYSC, Atiku da ADC sun kuma kalubalanci wasu tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026, wadanda suka ce sun takaita damar kalubalantar cancantar dan takara kafin gudanar da zabe, tare da cire cancanta a matsayin dalilin kalubalantar sakamakon zabe kamar yadda Sashe na 139(1)(a)(i) na kundin tsarin mulki ya tanada.

Sun yi hujjar cewa babu wata doka da Majalisar Tarayya za ta iya yi da za ta yi karo da kundin tsarin mulki, domin kundin tsarin mulki shi ne mafi girman doka a kasa.

Atiku ya ce wannan kara tana tayar da muhimmiyar tambaya ga dimokuradiyyar Najeriya.

Ya ce, “Za a iya amfani da wata doka ta Majalisar Tarayya a matsayin garkuwa daga wani sashe na kundin tsarin mulki? Za mu iya rubuta wata hanya ta tserewa ka’idar kundin tsarin mulki cikin doka ta yau da kullum ga masu neman shugabancin kasa? Matsayinmu shi ne kundin tsarin mulki ne mafi girma.”

Sanarwar ta ce takardar karar ta bukaci Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci kan ko irin takunkumin da doka ta tanada zai iya hana masu karar dogaro da Sashe na 137(1)(j) na kundin tsarin mulki, sannan a yanke hukunci kan ko ya kamata a hana Tinubu da APC shiga zaben shugaban kasa na 2027 idan har an tabbatar da hujjojin masu karar.

Atiku ya kara da cewa, “Kada wani ya yi kuskuren fahimtar abin da ke cikin wannan batu. Daliban Najeriya da suka kammala jami’a ba za su iya cike takardun NYSC da wata shaida ba sannan su bukaci masu daukar aiki su yi watsi da bambance-bambancen da ke cikinta. Ana tantance takardun matasan Najeriya sosai idan suna neman aikin gwamnati ko na kamfanoni. Bai kamata wannan ka’ida ta bace ba saboda mutum yana neman mukamin shugaban kasa. Shugabancin kasa ba takardar kariya ba ce daga binciken kundin tsarin mulki.”

Ya ce wannan matakin na shari’a ya dora wa INEC alhakin nuna cewa ba ta nuna son kai ta hanyar gabatar da takardun da ake bukata ga kotu.

A cewarsa, takardar rantsuwar da ya gabatar ta bayyana cewa INEC, a matsayinta na cibiyar gwamnati mai zaman kanta, tana da alhakin kare kundin tsarin mulki ba tare da la’akari da muradun siyasa ba.

Ya ce, “INEC ce ke rike da takardun. Kotu tana da ikon duba batutuwan. Shugaba Tinubu yana da damar kare kansa. Wannan shi ne tsarin da kundin tsarin mulki ya tanada, kuma babu wanda ya kamata ya ji tsoronsa. Dole ne zaben 2027 ya fara da fayyace cancantar masu neman shugabancin kasa. Bai kamata a bukaci ‘yan Najeriya su fara kada kuri’a sannan daga baya a fara bincike ba.”

Atiku ya jaddada cewa bayyana da ya yi da kansa domin rantsewa a gaban kotu ya nuna cewa a shirye yake ya fuskanci irin ka’idar kundin tsarin mulki da yake neman a yi amfani da ita ga sauran ‘yan takara.

Ya ce, “Na rantse da shari’ata a gaban doka. A shirye nake a dora min alhakin abin da na gabatar wa kotu. Ya kamata Shugaba Tinubu ma ya kasance a shirye ya amsa karar da ake yi masa a gaban doka.

“Wannan ba batu ba ne na gata ko mutum ko karfin shugaban kasa. Batu ne na kundin tsarin mulki guda daya da kuma ka’ida guda daya ga kowane dan Najeriya. Babu wanda ya fi karfin kundin tsarin mulki — ba Atiku Abubakar ba, ba Bola Tinubu ba, kuma ko shugaban Tarayyar Najeriya ma ba haka ba.”

Lauyoyin masu karar, Edwin Inegedu, SAN, da Joseph Onu Silas, sun bayyana kwarin gwiwa kan karar.

Da yake magana a madadin tawagar lauyoyin, Joseph Onu Silas ya ce sun yi nazarin doka sosai kuma sun gabatar da hujjojinsu a gaban kotu, tare da cewa a shirye suke su fuskanci hujjojin wadanda ake kara da zarar an mika musu takardun karar.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media