
Daga DAVID MICHAEL, Lafia
Yanayin siyasa a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, ya kara zafafa sakamakon rashin jituwar da ta barke tsakanin magoya bayan dan takarar gwamnan APC, Sanata Ahmed Wadada, da masu biyayya ga tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Abubakar Adamu, wanda ake zargin yana da burin neman kujerar gwamnan jihar.
Sabbin abubuwan da suka kunno kai, da suka hada da zargin hare-hare, lalata kayayyakin yakin neman zabe, sauya sheka da barazanar daukar matakin ladabtarwa a cikin jam’iyyar mai mulki, sun kara jefa masu bibiyar siyasar jihar cikin fargaba yayin da zaben 2027 ke kara matsowa.
Takaddamar tikitin APC ta kara rura rikicin bangarori
Binciken ‘YANCIN DAN ADAM ya gano cewa sabon rikicin ya samo asali ne daga sakamakon zaben fidda gwani na APC, bayan jam’iyyar ta ki bai wa tsohon IGP Adamu tikitin takara, lamarin da ya haifar da rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu.
An ce takaddamar ta haifar da cacar baki da zargin juna tsakanin magoya bayan bangarorin, yayin da wasu masu bibiyar siyasa ke danganta tashin hankalin da zargin magudi da rashin bin ka’ida a zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Lamarin ya kara kamari bayan wani furuci da aka danganta ga Gwamna Abdullahi Sule, inda aka ce ya gaya wa wasu ’yan jam’iyyar da ba su gamsu da sakamakon zaben fidda gwani ba su “shiga lagoon”.
An ce furucin ya fusata wasu jiga-jigan APC da ’yan takara wadanda suka ji cewa an yi musu rashin adalci a sakamakon zaben fidda gwani.
Binciken ‘YANCIN DAN ADAM ya kuma gano cewa kimanin ’yan majalisar dokoki biyar masu ci a karkashin APC sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar tare da komawa SDP, suna danganta matakin da zargin magudi da rashin bin ka’ida a zaben fidda gwani.
Rashin jituwar ya kuma bayyana ta hanyar lalata allunan talla da tutoci, baya ga arangama da hare-haren da ake zargin magoya bayan bangarorin siyasa masu hamayya da juna suna kai wa.
A baya-bayan nan ne aka samu wani lamari a Lafia, inda ake zargin wasu magoya bayan SDP da ake kyautata zaton masu biyayya ne ga tsohon IGP Adamu sun kai hari kan ayarin motocin Hajiya Maryam Aliyu Wadada, matar dan takarar gwamnan APC, jim kadan bayan ta bar fadar Sarkin Lafia.
An ce wadanda suka kai harin suna rera taken “IG Gauna”, lamarin da ya kai ga kama wasu matasa da ake zargin suna da hannu a harin.
Harin ya kara bayyana zurfin rashin jituwar da ke tsakanin bangaren tsohon IGP Adamu da na Sanata Ahmed Wadada kan tikitin takarar gwamnan APC.
Jiga-jigan siyasa sun yi Allah-wadai da harin, suna mai bayyana shi a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, kuma barazana ga siyasa mai cike da zaman lafiya a jihar.
An yi kira da a dakatar da tashin hankalin siyasa
Da yake mayar da martani kan lamarin, Kwamishinan Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Nasarawa kuma jigo a APC, Hon. Ibrahim Hamza, ya bayyana harin a matsayin wata hanya marar wayewa ta gudanar da siyasa.
“Ya kamata ’yan siyasa su nemi hanyoyin da suka dace kuma masu wayewa wajen magance korafe-korafensu,” in ji Hamza, inda ya gargadi magoya bayan dukkan bangarorin da su guji daukar doka a hannunsu.
Ya bukaci jami’an tsaro da su gudanar da bincike kan lamarin tare da gurfanar da wadanda aka samu da hannu a gaban shari’a domin zama darasi ga wasu.
Hamza ya kuma yi kira ga mazauna Karamar Hukumar Lafia da su ci gaba da karbar dukkan ’yan Jihar Nasarawa ba tare da la’akari da kabila, addini ko siyasa ba.
“Lafia gida ce ga kowa. Dole ne mu ci gaba da zama tare cikin zaman lafiya da hadin kai, musamman yayin da zaben 2027 ke kara matsowa,” in ji shi.
Ya ce Hajiya Maryam Wadada ta kasance kan gaba wajen shirye-shiryen tallafa wa mata da matasa a fadin jihar ta hanyar shirin Hajiya Maryam Wadada Women Empowerment Scheme 2026.
Hamza ya kuma jaddada cewa Sanata Wadada ne dan takarar gwamnan APC a babban zaben 2027, yayin da ya ce masu ruwa da tsaki a siyasar jihar suna kara yin kira da a mayar da hankali kan manufofi da shirye-shirye maimakon tashin hankali yayin da harkokin siyasa ke kara daukar zafi.
A gefe guda, ana ta yada jita-jitar cewa Shugaban APC na Jihar Nasarawa, Dr Aliyu Bello, na shirin dakatar da tsohon Gwamnan jihar, Sanata Umaru Al-Makura, daga jam’iyyar bisa zargin goyon bayan burin tsohon IGP Adamu na neman kujerar gwamna.
Sai dai Bello ya musanta wannan ikirari, yana mai cewa ba a gudanar da wani taro da aka tattauna batun dakatar da tsohon gwamnan ba, yana zargin cewa jita-jitar an kirkire ta ne domin haifar da gaba tsakaninsa da tsohon gwamnan.
Gwamna ya gargadi masu tayar da rikicin siyasa
A daidai lokacin da ake fuskantar wannan tashin hankali na siyasa, Gwamna Abdullahi Sule ya ce gwamnatinsa ta lura cikin damuwa da wasu ayyukan siyasa da suka hada da daba, toshe hanyoyin zirga-zirga, lalata tutoci da allunan talla, tsokana ga jama’a da kuma hare-haren da ake kai wa fararen hula masu bin doka.
Gwamnan ya gargadi cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani aiki da ya saba wa doka wanda zai iya jawo asarar rayuka da dukiyoyi a jihar ba.
A cewar Sule, gwamnati ba ta hana kowane mutum goyon bayan dan takarar jam’iyyar da yake so a zaben 2027 ba, muddin ana yin hakan bisa ka’ida da tanadin doka.
Ya ce, “Gwamnati ba ta hana mutane goyon bayan duk dan takarar jam’iyyar siyasa da suka zaba a babban zaben 2027 a jihar ba, matukar suna yin hakan cikin tsarin doka.”
Sai dai ya gargadi cewa gwamnati ba za ta amince da duk wani mataki da zai kawo cikas ga zaman lafiyar da ake da shi a Nasarawa ba.
Sule ya ce, “Yunkurin wasu mutane marasa kishin kasa na hura wutar siyasa abin Allah-wadai ne kwata-kwata, saboda yana iya kawo cikas ga zaman lafiya da zaman tare da wannan gwamnati ta samar.”
Daga bisani, gwamnan ya bayar da umarnin a dawo da hankali da da’a a harkokin siyasa a jihar, yana gargadin cewa za a dauki mataki kan duk wanda ya ki bin umarnin.
Yayin da zaben 2027 ke kara matsowa, abubuwan da ke faruwa a Lafia na nuna cewa fafutukar siyasa a Nasarawa na iya wuce takarar neman kuri’u kawai, yayin da rikicin cikin gida na APC ke kara jarrabar zaman lafiyar siyasar jihar.