
Daga JOHNSON NONGU, Makurdi
Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, ya tsayar da mutum shida domin tantancewa da tabbatar da nadinsu a matsayin mambobin Majalisar Zartarwar Jihar.
An bayyana hakan ne cikin wata wasika mai kwanan wata 18 ga Agusta, 2026, wadda gwamnan ya aika wa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Benue, Alfred Emberga, domin gabatar da ita ga ‘yan majalisar.
Lamarin ya fito fili ne a ranar Talata, lokacin da Kakakin majalisar ya karanta wasikar gwamnan ga ‘yan majalisar yayin zaman majalisa a Makurdi.
Mutanen da aka tsayar sun hada da Kuma Yenge, Roy Terna, Angwa Monday, Elizabeth Ogenyi, Solomon Iorpev da Nick Eworo.
Gwamna Alia ya bayyana cewa wadanda aka tsayar sun hada da mutanen da za su maye gurbin wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwar da suka bar mukamansu, da kuma wasu da za su cike guraben da ke akwai.
Ya ce matakin na da nufin karfafa majalisar zartarwar ta hanyar shigar da karin kwarewa da gogewa cikin gwamnatinsa yayin da take ci gaba da aiwatar da shirye-shiryenta a fadin jihar.
Gwamnan ya ce an gabatar da sunayen ne bisa ikon da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima, ya ba shi a karkashin Sashe na 192.
“An gabatar da sunayen ne bisa ikon da Kundin Tsarin Mulki ya ba ni, kuma bisa Sashe na 192 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima,” in ji Alia.
Don haka ya bukaci Majalisar Dokokin Jihar da ta gaggauta tantance mutanen tare da tabbatar da nadinsu bisa nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata.
