
Daga HASSAN SHALLPELLA, Yola
Gwamnatin Jihar Adamawa ta sake jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar.
Mataimakiyar Gwamnan Jihar, Farfesa Kaletapwa Farauta, ta bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da ta karbi bakuncin shugabannin Kungiyar Matan Jami’an ’Yan Sanda (POWA) a ofishinta.
Farauta ta ce ziyarar POWA ta nuna irin gudunmawar da mata, a matsayinsu na iyaye, ke bayarwa wajen tallafa wa jami’an ’yan sanda domin magance matsalar rashin tsaro.
Ta yaba wa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Adamawa, CP Kabir Umar, kan kokarin da yake yi wajen tabbatar da doka da oda tun bayan da ya fara aiki a jihar.
Ta ce, “Muna godiya ga CP Kabir Umar, domin tun bayan da ya zo Adamawa yake yin aiki mai kyau, kuma dalilin da ya sa yake yin hakan shi ne yana da mace ta gari a bayansa.”
Farauta ta kuma gode wa tawagar POWA bisa ziyarar, tare da tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro da iyalansu.
Ta ce gwamnati za ta ci gaba da yin iyakar kokarinta wajen inganta jin dadin mambobin POWA da kuma samar musu da walwala.
Tun da farko, Shugabar POWA ta jihar, Hajiya Hauwa Umar, wadda ita ce matar Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, ta ce ziyarar ta kasance ne domin karfafa alaka tsakanin kungiyar da gwamnatin jihar.
Ta yaba wa gwamnatin jihar kan kokarinta na tabbatar da zaman lafiya da tsaro, karfafa mata da kuma bunkasa al’umma.
Hauwa ta ce kungiyar na neman tallafi, shawarwari da karin hadin gwiwa daga gwamnati domin taimaka wa iyalan jami’an ’yan sanda da suka sadaukar da rayukansu wajen yi wa kasa hidima.
Ta ce POWA ta ci gaba da jajircewa wajen kula da jin dadin iyalan jami’an ’yan sanda da matayensu.
