
Daga WAKILINMU
Shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI) na Karamar Hukumar Jos North, Injiniya Muhammad Bello, ya halarci wani taron horas da shugabanni da masu ruwa da tsaki kan hanyoyin zamani na tafiyar da Zakka, Waqf da harkokin tallafin al’umma na Musulunci a Jihar Sakkwato.
An gudanar da horon na tsawon kwanaki biyar, daga ranar 11 zuwa 16 ga Agusta 2026, a Dankane Guest Inn da ke Sakkwato, wanda Hukumar Zakka da Kafaffen Arziki ta Jihar Sakkwato (SOZEA) ta shirya tare da hadin gwiwar Bankin Raya Musulunci (IsDB) da Kungiyar Masu Gudanar da Zakka da Waqf ta Najeriya (AZAWON).
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na JNI Jos North, Suleiman Hassan, ya sanya wa hannu a ranar Talata, tare da aikawa da ita ga ‘YANCIN DAN ADAM, kungiyar ta ce karfafa kwarewar hukumomi da samar da kawance na dabaru na da muhimmanci wajen tunkarar matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da kuma tabbatar da amfani da hanyoyin tallafin al’umma na Musulunci wajen taimaka wa mabukata.
Sanarwar ta ce taron ya hada masu ruwa da tsaki da kwararru a fannin tallafin al’umma na Musulunci, domin karfafa kwarewar hukumomi, samar da ingantattun dabarun rage talauci da kuma bunkasa shigar da hanyoyin tallafin Musulunci cikin shirye-shiryen raya kasa.
Kwararru daga manyan cibiyoyi ciki har da Jami’ar IPB ta Indonesia da Jami’ar Jihar Yobe, sun jagoranci darussa kan hanyoyin zamani na tafiyar da Zakka da Waqf, bunkasa hukumomi, zuba jari don amfanin al’umma da kuma samar da hanyoyin dogaro da kai mai dorewa.
Da yake bayyana muhimmancin horon, Injiniya Bello ya ce taron ya ba shi damar kara ilimi, kulla alakar aiki da masu ruwa da tsaki da kuma lalubo damar samar da kawance da zai amfani al’ummar Musulmi.
Ya ce JNI Jos North na kokarin kulla alaka mai amfani da kungiyoyi da cibiyoyi daban-daban a matakin kananan hukumomi, kasa da kasa, musamman wadanda ke gudanar da ayyukan jin kai, yaki da talauci, ilimi, kiwon lafiya da bunkasa tattalin arziki.
Bello ya ce irin wadannan alaka na daga cikin kokarin da JNI Jos North ke yi na jawo sahihan abokan hulda da tallafi da za su taimaka wajen samar da ayyuka da shirye-shiryen da za su shafi rayuwar al’ummar Musulmi kai tsaye.
Ya yabawa SOZEA, IsDB, AZAWON, kwararru da masu shirya taron bisa samar da damar musayar ilimi, kulla alaka da kuma bunkasa kwarewar hukumomi.
Bello ya sake jaddada kudurin JNI Jos North na ci gaba da neman kawance da shirye-shiryen da za su bunkasa rayuwar jama’a, jin dadin al’umma, dogaro da kai, zaman lafiya da kuma ci gaba mai dorewa.
