
Daga NANBAL PANPE
Super Falcons ta je gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata ta 2026 (WAFCON) tana dauke da tarihin nasarorin da ta samu a baya da kuma babban tsammanin ‘yan Najeriya, amma gasar ta kare mata cikin takaici, lamarin da ya sake haifar da tambayoyi kan shirye-shirye, shugabanci da yadda ake tafiyar da tawagar mata ta Najeriya.
A kasar da aka saba ganin Falcons na fafatawa wajen lashe kofunan nahiyar, yadda tawagar ta taka leda a Morocco ya bata wa magoya baya da dama rai, inda masu bibiyar kwallon kafa suka danganta rashin kyakkyawan shiri, matsalolin dabarun wasa da wasu kalubale na cikin gida da ake zargin sun taimaka wajen rashin nasarar.
Rashin kyakkyawan shiri ya jawo damuwa
An ce damuwar da ake ciki game da tawagar ta fara bayyana tun kafin fara gasar, bayan wasu zarge-zarge kan matsin lamba da ake cewa an yi wa wasu ‘yan wasa, da kuma tambayoyi kan yadda aka gudanar da shirye-shiryen gasar.
Duk da cewa Najeriya ta dade tana fuskantar suka kan jinkirin shirya tawagarta kafin manyan gasa, masu sha’awar kwallon kafa na ganin wannan dabi’a na ci gaba da shafar yadda kasar ke taka leda a wasannin kasa da kasa.
Miss Retdi Dabwol ta ce gasar ta nuna irin ci gaban da kwallon kafar mata ta samu a Afirka, inda kasashe da dama suka samar da tawagogin da suka nuna kwarewa sosai.
“Abin da ya fi daukar hankali a WAFCON shi ne irin ci gaba da karuwar gasa da kwallon kafar mata ta Afirka ta samu cikin shekaru,” in ji ta.
Dabwol ta ce kungiyoyin kasashe irin su Lionesses ta Kamaru, Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu, Morocco, Malawi da Zambia sun daga matsayin kwallon kafar mata a nahiyar.
A cewarta, ‘yan wasan sun nuna karin kwarin gwiwa, kwarewar dabarun wasa da karfin jiki idan aka kwatanta da gasannin baya, yayin da karuwar goyon bayan magoya baya da kafafen yada labarai ta kara wa gasar armashi da kwarewa.
Sai dai ta ce abin da aka dade ana yabawa Super Falcons da shi shi ne juriya da kuma iya taka rawar gani a lokacin da matsin lamba ya yi yawa, amma gasar ta bana ba ta nuna irin matakin da ake tsammani daga tawagar ba.
“Gaba daya, WAFCON ta tabbatar da cewa kwallon kafar mata a Afirka ba wasa ne na gefe kawai ba, domin ingancinta da nishadantarwarta na kara bunkasa a kowace gasa,” in ji ta.
Magoya baya sun soki yadda Falcons ta taka leda
Shi ma wani mai sha’awar kwallon kafa, Mista Jabez Dakum, ya bayyana wasan Falcons a matsayin daya daga cikin mafi munin wasannin da wata tawagar mata ta Najeriya ta yi a ‘yan shekarun nan.
“Tsawon shekaru da dama, Super Falcons ce ke kawo farin ciki a fuskokin ‘yan Najeriya,” in ji shi, yana mai bayyana yadda tawagar ta taka leda a gasar a matsayin abin takaici.
Dakum ya danganta rashin nasarar da abin da ya kira rashin kyakkyawan shiri da kuma shugabanci mara inganci, inda ya bukaci Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta gudanar da cikakken nazari kan tawagar da yadda ake shirya ta.
Ya ce Najeriya har yanzu tana da hazikan ‘yan wasan da za su iya fafatawa wajen lashe manyan kofunan kasa da kasa, ciki har da gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA, amma rashin kyakkyawan tafiyar da su da kuma sanya mutanen da ba su dace ba a wuraren da bai kamata ba na iya ci gaba da kawo cikas ga wannan dama.
Ya bukaci NFF ta koyi darasi daga wannan rashin nasara, ta tsara hanyoyin da za su dawo da Falcons matsayin da ta saba da shi na jagoranci a kwallon kafar mata ta Afirka.
Haka kuma, Mista Nnaemeka Okoroafor ya bayyana yadda Falcons ta taka leda a matsayin abin takaici, yana mai cewa Najeriya ta kafa irin wannan babban matsayi a kwallon kafar mata ta Afirka, wanda duk rashin kaiwa matakin karshe na WAFCON ake kallonsa a matsayin koma baya.
“A dukkan kwallon kafar Afirka, matsayinmu a Afirka da WAFCON kamar matsayin Brazil ne a gasar cin kofin duniya,” in ji shi, yana mai tunatar da cewa Najeriya ta dade tana mamaye gasar kuma ita ce kasar da ta fi lashe kofin.
Okoroafor ya ce da a ce Falcons ta sha kashi a wasan karshe ko ma a wasan kusa da karshe, da za a iya fahimtar hakan, amma rashin kaiwa matakin hudu na karshe ya fi tayar da hankali saboda samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya ya danganta ne da kaiwa matakin wasan kusa da karshe.
Ya kara da cewa mafi yawan manyan ‘yan wasan da suka wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniya da ta gabata har yanzu suna cikin tawagar, lamarin da ya sa rashin kyakkyawan sakamakon ya kara zama abin mamaki.
“Abin takaici ne matuka saboda irin matsayin da muka kafa wa kanmu,” in ji shi.
Nazarin wasannin Falcons daya bayan daya
Wani mai sha’awar kwallon kafa, Nanfwang Manasseh, ya yi nazari kan wasannin da Falcons ta buga daya bayan daya, inda ya fara da wasan farko da ta yi da Malawi.
Ya ce tun daga farko ba a ga wani abin kwarin gwiwa a yadda tawagar ta taka leda ba, yana mai cewa watakila Falcons ta raina karfin kungiyar Malawi.
“Tun daga farko, yadda suka taka leda bai kayatar ba a wasan da Malawi, wanda muka yi rashin nasara da ci 3-2,” in ji shi.
Manasseh ya ce rashin nuna damuwa da karfin abokiyar karawa na daga cikin abubuwan da ka iya haddasa rashin nasarar.
Sai dai ya ce tawagar ta inganta sosai a wasanta na biyu, duk da raunin da aka samu a bangaren tsaro da kuma jan kati da aka bai wa daya daga cikin ‘yan wasan tsakiya.
“Wasanmu na biyu shi ne inda muka taka leda sosai,” in ji shi, yana mai cewa tsakiyar fili ya kasance cikin yanayi mai kyau duk da jan katin da ya sa Najeriya ta buga da ‘yan wasa 10 na tsawon kusan awa guda.
Ya kuma yaba da yadda Okonkwo da Ajibade suka taka rawar gani a wasan.
A cewarsa, Falcons ta buga mafi kyawun wasanta a matakin rukuni ne a karawar da ta yi da Masar, inda ta mamaye wasan tare da zura kwallaye shida, yayin da aka zura mata biyu.
“Wani wasa mai kyau shi ne wanda muka yi da Fir’aunan Masar, inda muka mamaye wasan ta kowane bangare, muka zura kwallaye shida, aka zura mana biyu,” in ji shi.
Sai dai wasan daf da na kusa da karshe da Kamaru ya zama makoma ga Falcons, inda tawagar ta kasa samun nasara kuma gasar ta kare mata.
Manasseh ya danganta wani bangare na rashin nasarar da kura-kuran mai tsaron raga, wadanda ya ce sun bai wa Kamaru damar samun galaba a kan Najeriya.
Rashin samun nasarar tsallakewa zuwa matakin gaba ya kuma hana Falcons samun gurbin kai tsaye zuwa gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA ta 2027, lamarin da ya kara tsananta takaicin da aka samu daga gasar nahiyar.
Ga masu goyon bayan tawagar da dama, sakamakon ya kara nuna bukatar gudanar da cikakken nazari kan shugabanci, shirye-shirye da kuma bangaren fasaha na tawagar.
Sun ce Najeriya tana da hazikan ‘yan wasa da za su iya fafatawa a matakin koli, amma dole ne a inganta tsare-tsare, tabbatar da rikon amana da kuma gudanar da tawagar yadda ya kamata domin Super Falcons ta dawo matsayinta na daya daga cikin manyan tawagogin kwallon kafar mata a Afirka.
A karshe, sakon da magoya baya da masu sharhi kan kwallon kafa ke bayarwa shi ne cewa Najeriya ba za ta ci gaba da dogaro da hazikan ‘yan wasanta kawai ba tare da samar da ingantattun tsare-tsare da tsarin da zai taimaka wajen bunkasa da tafiyar da su yadda ya kamata ba.
Sun ce ana bukatar cikakken sauyi domin hana tawagogin kasar ci gaba da “yawo cikin da’ira” ba tare da cimma wani gagarumin buri ba, yayin da sauran kasashen Afirka ke ci gaba da rage tazarar da ke tsakaninsu da Najeriya.