
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT), Nyesom Wike, ya ce ba zai iya kasancewa cikin kwamitin yakin neman zaben sake zaben Shugaba Bola Tinubu ba, saboda ba ya cikin jam’iyyar APC mai mulki.
Wike ya bayyana hakan ne ranar Asabar, bayan ya duba wasu ayyukan raya kasa da ake ci gaba da gudanarwa a Abuja.
Ministan ya jaddada cewa kasancewa mamba a kwamitin yakin neman zabe ba yana nufin mutum zai samu nasara a zabe ba.
A cewarsa, muhimmancin dan siyasa a zaben shugaban kasa ya ta’allaka ne kacokan kan yadda zai iya samun nasara a jiharsa, kananan hukumominsa da mazabarsa.
Wike, wanda ya jaddada cewa, “duk siyasa ta gida ce”, ya bukaci ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban da su mayar da hankali wajen hada kan masu kada kuri’a a matakin kasa da kasa domin Tinubu, maimakon fafutukar neman mukamai a kwamitocin yakin neman zabe.
Ya yi watsi da ra’ayin cewa rashin kasancewar wasu fitattun ’yan siyasa cikin Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na APC zai hana su taimakawa wajen samun nasarar zaben shugaban kasa.
Da yake misalta hakan da abubuwan da suka faru a siyasar baya-bayan nan, Wike ya ambaci wasu fitattun ’yan siyasa da suka jagoranci kwamitocin yakin neman zaben shugaban kasa a matsayin Daraktocin-Janar (DG), amma suka kasa samun nasara a jihohinsu.
Ya ce, “Rotimi Amaechi ya kasance Darakta-Janar na yakin neman zaben Muhammadu Buhari a 2015 da 2019, amma ya kasa samun nasara a Rivers.
“Bukola Saraki ya jagoranci kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar a matsayin DG a 2019, amma ya rasa jihar Kwara da kujerarsa ta Sanata.
“Aminu Tambuwal ya kasance DG na yakin neman zaben Atiku Abubakar a 2023, amma ya rasa jihar Sokoto.
“Simon Lalong ya jagoranci Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na APC a matsayin DG a 2023, amma ya kasa kai Plateau.”
Wike ya ce, “Idan kai DG ne kuma ba ka iya lashe jiharka, mene ne amfanin kasancewarka DG? Idan ka rasa jiharka, ko da kana DG, za ka ji kunya. Idan ka ce ka yi nasara, mutane za su tambaye ka: ‘Me ya sa ba ka yi nasara a jiharka ba?’”
Ministan ya bayyana cewa kawancen siyasa ya wuce tsarin jam’iyyu na yau da kullum, inda ya ce akwai wata kungiyar kawance ta jam’iyyu daban-daban mai suna ‘Rainbow Coalition’, wadda ke aiki a wasu jihohi da suka hada da Bayelsa, Benue da Kwara domin mara wa shugaban kasa baya, ba tare da la’akari da nadin da aka yi a kwamitin yakin neman zabe ba.
Da yake magana kan rawar da kungiyar G-5 ta taka a zaben 2023, Wike ya jaddada cewa fitattun ’yan siyasa na iya yin aiki ta wasu tsare-tsare masu zaman kansu domin samun nasara a yankunansu.
Ya ce, “Ni ba dan APC ba ne, don haka ba zan iya kasancewa cikin Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa ba. Mun yi namu dabarun yadda za a samu nasarar shugaban kasa.
“A cikin Rainbow Coalition, ba sai mun kasance mambobin Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na APC ba. Muna gudanar da namu aikin.”
Wike ya tabbatar da cewa shi ne zai jagoranci harkokin siyasa a Abuja da Rivers domin tabbatar da samun nasarar shugaban kasa a zaben 2027.
Ya ce, “Abin da yake da muhimmanci shi ne: shin za ku iya kai wa nasara a wadannan jihohi biyu? Wa zai jagoranci yakin neman zabe a Rivers? Ni. Wa zai jagoranci na FCT? Ni.”
(NAN)
