Friday, October 23, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Labari

Mutfwang ya sauya wa kwamishinoni ma’aikatu a Plateau

by The Nigeria Standard
August 22, 2026
in Labari
Reading Time: 3 mins read
0 0
Beyond political panic: The people, not the elite, define Gov Mutfwang’s strength

Governor Mutfwang

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga SEKYEN WALSHAK

Majalisar Zartarwa ta Jihar Plateau ta sake sabon salo, bayan da Gwamna Caleb Mutfwang ya sauya wa wasu kwamishinoni ma’aikatun da suke jagoranta a gwamnatin jihar.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Arc. Nanchang Jatau, ya sanya wa hannu ranar Juma’a kuma ya rabawa ‘YANCIN DAN ADAM, gwamnatin jihar ta ce sauyin ya kasance ne domin kara inganta aiki da kuma samar da ingantaccen gudanar da ayyuka a Majalisar Zartarwar jihar.

Sanarwar ta ce sauyin ma’aikatun ya biyo bayan karin kwamishinoni uku da gwamnan ya yi wa Majalisar Zartarwar jihar.

Philemon Daffi, SAN, daga Mangu, ya ci gaba da rike mukamin Antoni-Janar na jihar kuma Kwamishinan Shari’a, yayin da Mrs. Dongkum Grace Shwarta ta Pankshin ta ci gaba da kula da Ma’aikatar Kudi.

Dr. Nicholas Baamlong daga Qua’an Pan ya ci gaba da rike Ma’aikatar Lafiya, yayin da Arc. Sylvester Dongtoe daga Shendam ya ci gaba da kasancewa Kwamishinan Gidaje da Raya Birane.

Rt. Hon. Joyce Ramnap daga Langtang South ta ci gaba da kula da Ma’aikatar Yada Labarai, yayin da Hon. Ephraim Usman daga Kanam ya ci gaba da rike Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta.

Mr. Jatau Davou Gyang daga Jos South ya ci gaba da rike Ma’aikatar Sufuri, yayin da Hon. Bashir Lawandi Datti daga Jos North ya ci gaba da kula da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Makamashi.

Mrs. Caroline Panglang daga Mikang ita ma ta ci gaba da rike Ma’aikatar Harkokin Mata.

An dora wa Hon. Peter Nyam Gai daga Jos North kula da Ma’aikatar Aikin Gona, yayin da Hon. Ishaku Maren daga Bokkos aka dora masa Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare.

Hon. Musa Ibrahim Ashoms daga Jos East aka dora masa Ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu, yayin da Prof. Gloria Samuel Karuri daga Bassa aka dora mata Ma’aikatar Ilimi.

Hon. Joshua Laven Ubandoma daga Langtang North aka dora masa Ma’aikatar Muhalli, yayin da Dr. Mrs. Kacholom Gang daga Riyom aka dora mata sabuwar Ma’aikatar Harkokin Jin Kai.

Mr. Peter Gwom daga Barkin Ladi an mayar da shi Ma’aikatar Filaye, Auna da Tsare-tsaren Birane, yayin da Hon. Samson Bugama daga Kanke aka dora masa Ma’aikatar Kiwo da Kamun Kifi.

Nyalum M. Salihu daga Wase aka dora masa Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha, yayin da Dr. Cletus Shurkuk daga Pankshin aka dora masa Ma’aikatar Ayyuka.

Comr. Prince Miaphen daga Qua’an Pan aka dora masa Ma’aikatar Matasa da Bunƙasa Wasanni.

Sabon tsarin ya raba kwamishinoni 20 zuwa muhimman sassan gudanar da mulkin jihar, ciki har da aikin gona, shari’a, ilimi, lafiya, ayyukan more rayuwa, kudi, sufuri da harkokin jin kai.

Wakiliarmu ta ruwaito cewa ana sa ran sauyin zai kara fayyace nauyin da ke kan kowane mamba na Majalisar Zartarwar Jihar Plateau, yayin da gwamnatin ke ci gaba da aiwatar da shirye-shiryenta na raya jihar.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media