
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin kama Yarima George Nwabueze nan take, biyo bayan gano wata hukumar bogi mai suna National Brands Development and Made in Nigeria Special Project Office.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Sauran Laifukan Alaka da Hakan (ICPC) ce ta gano hukumar bogin a cikin ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.
Shugaban ICPC, Dakta Musa Aliyu, SAN, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa bayani bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a ranar Juma’a.
Adamu ya bayyana cewa an gano sabuwar hukumar bogin ne a wani bangare na binciken da ake ci gaba da yi kan wata kungiyar bogi mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council, wadda Adeyemi Matthew ke gudanarwa.
Ya ce an ware wa hukumar bogin wani ofishi ba bisa ka’ida ba a cikin harabar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Haka kuma, Tinubu ya ba da umarnin dakatar da sakatarorin dindindin guda uku nan take, wadanda suka hada da M.S. Danjuma, Injiniya Nadungu Gagare da Richard P. Pheelangwah, bisa lamarin.