Saturday, October 24, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Labari

Gwamnatin Kaduna da mazauna yankin sun karyata rugujewar madatsar Kangimi

by The Nigeria Standard
August 25, 2026
in Labari
Reading Time: 5 mins read
0 0
Gwamnatin Kaduna da mazauna yankin sun karyata rugujewar madatsar Kangimi
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga JOHN FWAH, Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna da mazauna al’ummomin da ke kewaye da madatsar ruwan Kangimi a Karamar Hukumar Igabi ta jihar sun karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa madatsar ruwan ta ruguje ko kuma tana dab da rugujewa.

Gwamnatin jihar ta tabbatar wa mazauna yankin cewa madatsar ruwan tana nan daram kuma tana aiki yadda ya kamata.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Din-din-din na Ma’aikatar Ayyukan Jama’a da Ababen More Rayuwa, Ashiru Abdu, ya sanya wa hannu, gwamnatin ta bayyana cewa hotunan da ake yadawa suna da alaka ne da wata matsalar tsarin ginin madatsar da aka fara gani a shekarar 2015/2016.

Gwamnatin ta ce matsalar tana da alaka da tsufar gine-ginen madatsar da kuma matsin lamba sakamakon yawan ruwan sama, kuma daga bisani Ma’aikatar Ayyukan Jama’a da Ababen More Rayuwa ta dauki matakan gaggawa na gyara ta.

Ta ce ana ci gaba da sa ido kan madatsar ruwan tare da gudanar da kananan ayyukan kula da ita, tana mai jaddada cewa “a halin yanzu babu wata alama da ke nuna cewa tsarin madatsar ruwan na rugujewa.”

Gwamnatin ta kara da cewa ana shirin daukar wasu matakan tsaro, ciki har da sanya na’urorin auna matakin ruwa kai tsaye, kararrawar gargadin gaggawa da na’urorin sadarwa na musamman domin kara inganta sa ido kan yanayin madatsar.

Ta kuma bayyana cewa an tsara gudanar da binciken fasaha na hadin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Tsaftar Muhalli ta Tarayya da gwamnatin Jihar Kaduna domin duba yanayin madatsar da kuma tantance wasu matakan da ake bukata domin kara inganta tsaronta.

A gefe guda, manoma, masunta da mazauna al’ummomin da ke kewaye da madatsar sun karyata rahotannin yayin da wasu ’yan jaridar African Climate Reporters suka kai ziyara domin gudanar da bincike kai tsaye bayan bullar rahotannin.

A lokacin ziyarar tantance gaskiyar lamarin, an ga manoma da masunta suna gudanar da harkokinsu na yau da kullum a bakin kogin, yayin da mazauna yankin suka ce babbar damuwarsu ba ita ce wai madatsar ta ruguje ba, sai dai mummunan yanayin hanyar da ta hada al’ummominsu da manyan garuruwa da kasuwanni.

Hanyar da ta taso daga Maraban-Jos zuwa madatsar Kangimi, wadda ta kai tsawon kimanin kilomita 14, tana cikin mummunan hali, lamarin da ke sa jigilar amfanin gona, kifi da sauran kayayyaki ta kasance mai wahala da tsada.

Wani masunci kuma manomi da ke zaune kusa da madatsar, Malam Shamsu Abubakar, ya ce ya ga rahotannin a kafafen sada zumunta, amma bai damu matuka ba.

Abubakar, wanda ya ce ya shafe shekaru yana noma da kamun kifi a kusa da madatsar a lokacin damina da rani, ya bayyana madatsar a matsayin wata muhimmiyar hanya da ke amfanar da shi da sauran mazauna yankin.

Ya ce duk da cewa an taba samun damuwa kan zubar ruwa, babbar matsalarsa ita ce bukatar a kwashe tarkace da laka daga madatsar domin kara karfin adana ruwa.

A cewarsa, inganta hanyoyin zai bai wa manoma da masunta damar kai kayayyakin da suka samar kasuwanni cikin sauki, tare da rage asara da kudin sufuri.

Ya tuna cewa kimanin shekaru takwas da suka gabata, lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, wata karamar tsagewa ta samu a madatsar, amma ya ce an gyara matsalar kuma harkokin da ke wajen madatsar suka ci gaba yadda ya kamata.

Abubakar ya kara da cewa tun bayan da rahotannin madatsar suka fara yawo a kafafen sada zumunta, jami’an gwamnati da dama sun ziyarci yankin domin duba yanayin madatsar.

Haka kuma, wani manomi kuma mazaunin al’ummar Gwauro, Jibril Isa, ya ce manoma da ke kusa da madatsar na ci gaba da cin moriyar noman rani da damina.

Isa ya ce madatsar ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin noma da tattalin arziki a yankin, yana mai cewa kwashe laka da tarkace daga cikinta zai kara karfin adana ruwa domin noma.

Ya ce rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta ba su kawo cikas ga ayyukansu ba, amma ya bukaci gwamnati ta inganta hanyoyin sadarwa tare da kara gudanar da ayyukan gyara a madatsar.

Wani mazaunin Rugugi-Gwauro, Adamu Galadima, ya ce yawancin mazauna yankin sun dogara ne da noman shinkafa, masara, dankalin Hausa da sauran amfanin gona wajen samun abin dogaro da kai.

Ya ce, “Rashin kyawun sufuri ya zama babbar matsala, inda wasu mazauna yankin ke dogaro da manyan motocin dakon kaya, babura da kekuna wajen kai amfanin gonarsu kasuwanni.”

Galadima ya bukaci gwamnatin jihar ta gyara hanyar da ta taso zuwa madatsar, yana mai cewa inganta hanyar zai saukaka jigilar kayan amfanin gona zuwa kasuwanni tare da saukaka wa mazauna yankin zuwa asibitoci, makarantu da sauran muhimman wurare.

A nata bangaren, kungiyar African Climate Reporters (ACR) ta yaba wa gwamnatin jihar kan matakin da ta dauka wajen mayar da martani ga damuwar da aka nuna kan yanayi da tsaron madatsar ruwan.

Kungiyar ta kuma yi maraba da bayanin da Ma’aikatar Ayyukan Jama’a da Ababen More Rayuwa ta Jihar Kaduna ta fitar a ranar 20 ga Agusta, bayan rahotannin da suka ce madatsar ta ruguje.

Kungiyar ta ce bayanin gwamnatin ya taimaka wajen fayyace tarihin matsalolin tsarin ginin madatsar da aka gano a baya, tare da tabbatar wa mazauna yankin cewa a halin yanzu babu wata alama da ke nuna cewa tsarin madatsar na rugujewa.

ACR ta bukaci ’yan jarida, masu rubutun ra’ayi a shafukan intanet da kafafen yada labarai su ba da fifiko ga binciken gaskiya da aikin jarida mai zurfi, maimakon dogaro da jita-jita ko bayanan da ba a tantance ba.

Ta yi gargadin cewa yada bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba na iya haifar da fargaba da rudani ba tare da dalili ba a tsakanin jama’a, tana mai jaddada muhimmancin aikin jarida mai nagarta, musamman kan batutuwan da ka iya jefa al’umma cikin fargaba.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media