Friday, October 23, 2026
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
No Result
View All Result
The Nigeria Standard
SUBSRCIBE
  • Home
  • News
    • Middle-Belt
    • World
  • Business
    • Entrepreneurship
  • Politics
  • Science & Tech
    • IT
  • Sports
  • Opinion
    • Columns
  • Editorials
  • Lifestyle
    • Culture
    • Travel
  • ‘Yancin Dan Adam
The Nigeria Standard
Home Labari

Mauludi: Mutfwang ya bukaci Musulmi su rungumi zaman lafiya

by The Nigeria Standard
August 25, 2026
in Labari
Reading Time: 2 mins read
0 0
Mutfwang congratulates newly elected COCIN leaders
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga PETER TITLE, Jos

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya bukaci Musulmi da su ba da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya, hakuri da juna da kuma zaman tare tsakanin al’ummar Najeriya yayin da suke gudanar da bikin Mauludin Annabi Muhammad, tare da yin koyi da darussan rayuwarsa da koyarwarsa.

A cikin sakon taya murnar Mauludin da Daraktan Yada Labarai da Harkokin Jama’a na gwamnan, Gyang Bere, ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Jos, Mutfwang ya bukaci Musulmi su yi tunani kan kyawawan dabi’un Annabi Muhammad, musamman zaman lafiya, adalci, tausayi, hakuri da mutunta masu bin addinai daban-daban.

Gwamnan ya yaba wa Kwamitin Mauludin na shekara-shekara na Jos karkashin Jama’atu Nasril Islam (JNI) bisa zabar taken “Koyi da Hanyar Annabi ta Zaman Lafiya, Mutunta Juna da ’Yancin Addini”, yana mai cewa taken ya dace da lokacin, musamman wajen karfafa zaman lafiya a cikin al’ummar da ke da mabambantan addinai.

Ya bukaci Musulmi su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’ar samun zaman lafiya, hadin kai da tsaro a Jihar Plateau, tare da kira ga al’umma da su yi watsi da tashin hankali, kiyayya da duk wani abu da ka iya kawo cikas ga kyakkyawar alaka tsakanin al’ummomi.

Mutfwang ya kuma sake tabbatar da kudurin gwamnatinsa, karkashin ajandar “Lokaci Ya Yi” (The Time Is Now), na samar da yanayin da zai bai wa kowane dan kasa damar gudanar da ibadarsa cikin ‘yanci ba tare da wata tangarda ba.

Gwamnan ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatin za ta ci gaba da daukar kwararan matakai kan masu aikata laifuka da sauran bata-gari da ke kokarin kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin Jihar Plateau.

Mutfwang, a madadin gwamnatin jihar da al’ummar Plateau, ya yi addu’ar samun dawwamammen zaman lafiya, hadin kai da ci gaba a jihar da Najeriya baki daya.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook Twitter Youtube RSS

Subscribe to Weekly Newsletter for New Updates

Check News by Category

Not So Recent News

Important Links

  • About Us
  • Contact Us
  • Advertise With Us
No Result
View All Result

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertise With Us
  • Advertising Services
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
Subscribe

© 2025 The Nigeria Standard - Digital Media