
Daga MARIE-THERESE NANLONG da SEKYEN WALSHAK
Gwamnatin Jihar Plateau ta shirya mika ragamar gudanar da Babban Asibitin Riyom ga Gwamnatin Tarayya, bayan Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta nemi karbe shi domin inganta harkokin kiwon lafiya da kuma samar da ingantaccen tsarin gudanar da asibitin.
Babban Daraktan Kiwon Lafiya na Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Plateau, CMD, Dakta Sumi Benjamin, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Kamfanin Buga Jaridu na Plateau (PPC), masu wallafa jaridun THE NIGERIA STANDARD da ‘YANCIN DAN ADAM, wadda ta kai masa ziyarar ban girma.
Benjamin ya ce gwamnatin jihar ta amince da bukatar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya na karbar asibitin, inda ya ce yanzu haka bangarorin biyu na shirin rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU).
Ya ce, “Mun samu wasikarsu. Sun aiko da tawagogi da dama. Mun ba su amincewar karbar wannan asibiti. Yanzu haka muna shirin rattaba hannu kan yarjejeniyar MoU da su.”
Ya bayyana cewa za a shigar da ma’aikatan asibitin cikin tsarin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, yayin da wadanda ke son ci gaba da aiki karkashin gwamnatin jihar za a iya mayar da su wasu asibitocin jihar.
A cewar CMD din, Hukumar na kuma kokarin inganta kayayyakin more rayuwa a asibitocin jihar ta hanyar samar da na’urorin kiwon lafiya na zamani da kuma amfani da hasken rana wajen samar da wutar lantarki.
Benjamin ya ce, “Burina shi ne in bar asibitoci masu kyau da ke amfani da hasken rana,” inda ya kara da cewa Hukumar na shirin bullo da tsarin adana bayanan marasa lafiya ta hanyar na’urorin zamani a dukkan asibitocinta.
Ya ce tsarin zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana, tare da bai wa asibitoci damar samun bayanan marasa lafiya daga wasu asibitoci ba tare da dogaro da takardun aiki masu yawa ba.
Dangane da karancin ma’aikata, Benjamin ya bayyana cewa an sake daukar likitoci 22 da suka yi ritaya domin karfafa yawan ma’aikata a asibitocin gwamnati, yana mai cewa matakin ya taimaka wajen rage korafe-korafen karancin kwararrun likitoci.
Ya ce Hukumar a halin yanzu tana kula da manyan asibitoci 19 da ke fadin kananan hukumomi 17 na jihar, kuma za ta ci gaba da kokarin inganta ayyukan kiwon lafiya.
Benjamin ya kuma bayyana cewa an gyara tare da sabunta motocin daukar marasa lafiya na Hukumar, inda aka sanya sabbin injuna a wasu daga cikinsu tare da gyara su domin kara musu ingancin aiki.
Ya yaba wa gwamnatin jihar bisa goyon bayan da take bai wa Hukumar, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da za su inganta harkokin kiwon lafiya a Plateau.
Tun da farko, tawagar PPC mai mutum biyar da Manajan Talla, Plangnan Akila, ya jagoranta, ta ce ta kai ziyarar ne domin karfafa alaka da Hukumar tare da tabbatar da cewa jama’a na samun cikakken bayani kan ayyuka da nasarorin da Hukumar ke samu a bangaren kiwon lafiya.
Akila ya ce wasu daga cikin shirye-shirye da sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa ba sa samun isasshen bayani a wajen jama’a, yana mai jaddada muhimmancin kafafen yada labarai wajen cike wannan gibi.
Ya ce, “Gwamna yana yin abubuwa da dama, amma jama’a ba su san abin da ke faruwa ba. Saboda irin shirye-shiryenku da manyan abubuwan da kuke yi, ya kamata jama’a su sani.”
Akila ya ce PPC na da sha’awar ci gaba da ba da rahoto kan ayyukan Hukumar, tare da neman karin damar yin hulda da ita, ciki har da gudanar da cikakkiyar hira da CMD.
Ya kara da cewa ziyarar ta kuma ba su damar duba hanyoyin hadin gwiwa tsakanin Hukumar da jaridun THE NIGERIA STANDARD da ‘YANCIN DAN ADAM.
